BABI NA BIYAR

164 28 0
                                    

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DAvZ5MDoOVSLXMUGsb6DKc

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*TSAKANINA DA MUTUWA...!*

©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals

*BABI NA BIYAR*

Yayi ƙasa-ƙasa da murya sosai yadda Matarsa Zainab da take can cikin banɗaki baza ta iya jiyo shi ba, sai kallon hanyar cikin ɗakin yake yi alamun rashin gaskiya da tsarguwa ƙuru-ƙuru a tattare da shi.
"Haba darling, Haba Habeebtee Ashfat, kina so ki zauta ni ne in rasa yadda zanyi da rayuwata? Wallahi tunda kika kashe min waya na rasa duk wani sukuni nawa. Ko ɗigon barci bai ziyarci ƙwayar idanuna ba don tsananin tashin hankali da tunanin kina can kina kukan shagwaɓar nan taki. Don Allah ki dinga tausayawa ɗan bawan Allah mana! Ni ne fa Khalil ɗinki da kike mutuwarso, ko so kike tsananin soyayyarki ta zauta ni?."
Ya ƙarasa maganar cikin marairaita da lallami mai cike da yaudara irin ta ɗa namiji.

Daga can bangaren Ashfat fari tayi da idanunta, tana jin ranta yayi fari tas don jin cewa haƙanta yana ta cimma ruwa. Ta riga ta gama sace zuciyar Khalil ta ko wane ɓangare, tana da tabbacin babu wata ya mace dake da wani tasiri a wajenshi sai ita kadai, hatta da wannan ƙwarangwamar da take a matsayin matarsa, abu ɗaya da za ta nuna masa kawai igiyoyin aurensa da yake kanta saɓanin ita da har yanzu ko kuɗin gaisuwar neman aurenta bai kawo gidansu ba.

Ta kalli ƙawarta da suke zaune ta ƙyafta mata ido ɗaya, sannan ta buɗe wayar a sifika ta fara magana cikin kissa da kisisina mai ɗaukar hankalin
   "Ni me zaka ce min kuma Habeebee? bayan kana nema ka jajaba min kalmar mara tarbiya da da'a bayan ni dai nasan akan gaskiyata nake? Kai fa mijin da zan aurane nan da abinda bai wuce shekara daya ba, za mu zama babu wani abu da zai zama hijabi a tsakaninmu, amma kullum dana dan tattaleka na nuna maka kaɗan daga kulawar da zanyi maka idan munyi aure sai ka nuna min kamar bana tsoron Allah, ya kake so inyi ne!?...".
Ta karasa maganar tana sakin wani irin kukan shagwaba da yasa ya ƙara rikicewa, ya hau lallashinta yana bata hakuri kamar zai fasa ihu. Da yake mutum ne da yasan kan zama da 'ya mace, nan da nan ya kalallameta da dadin baki.

To da yake itama ba baya bace a wajen bi da d'a namiji don kuwa idanunta a bude suke sosai, sai da tayi yadda tayi ta ƙara nuna mishi ita fa a tafarki mai kyau take, Kuma hakan da take mishi shi ne kaiwa ƙololuwar wayewa a zazzaƙar soyayya. Da haka dai suka yi sallama cikin daɗin rai kamar ba zasu rabu ba, amma da yaga lokaci ya ja ako wace daƙiƙa Zainab za ta iya fitowa daga wanka sai yayi mata sallama ya bata uzurin zai tafi Ofis, amma da alƙawarin idan ya tashi aiki kafin ya wuce gidanshi zai je gurinta.

Ya kashe wayar ya ajiye a kusa dashi. Komawa yayi ya jingina da kujera yana shafa sumar kanshi tare da sauke ajiyar zuciya. A ranshi yake ayyana yau de ga amfanin daɗewar Zainab a wanka. Sai kuma yayi wa kanshi murmushi, Yana tsoron ranar da Zainab za ta gano abinda yake aikatawa a bayan idanunta.

Mace ce ita mai ɗan banzan kishi, yadda take kishinshi gami da gwada mishi nata salo-salo na babin soyayyar gani take babu wata ƴa mace duk ƙwalisarta da ta isa takai mishi hari. Shi mijinta ne ita kaɗai ƙwallin ƙwal. A gabanshi da bayan idanunshi ta sha faɗin haka.

'Ashfat ita ma ba baya ba wajen masifaffen kishi, ga ta ba kanwar lasa bace a fagen iya soyayya, kuma wayayya ce ƴar boko kyayyawa ta bugawa a jarida. Taken gidansu ma kenan Gidan Hajiya Laura mai kyawawan ƴammata. Asalinsu ƴan cameru ne, babu wanda yasan takamaimai gaskiyar abinda ya ƙauro da Hajiya Laura da Yayanta Alhaji Hassan zuwa Nigeria, suka yi masauki a garin kaduna. A lokacin Ashfat da yayyinta huɗu suna ƙaƙana sosai.

Ashfat ce macen da ya fara so a rayuwarsa ta duniya, ta tara duk wasu abubuwa da namiji ke so kuma yake burin samu a gurin ƴa macen da zai aura. Ya kira haɗuwarsu da ƙaddara a gurin dinnar bikin ɗaya daga cikin abokansu.

TSAKANINA DA MUTUWA...! Where stories live. Discover now