BABI NA ASHIRIN DA UKU

137 22 1
                                    

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*TSAKANINA DA MUTUWA...!*

©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals

*BABI NA ASHIRIN DA UKU*

Amarya da ango na can a filin rawa, suna tsaye a gefen juna, a fuskokinsu cike da annurin da ke bayyana matsanancin farin cikin da zukatansu ke ciki.

Challenge aka sa tsakanin amarya da ango waye zai fi samun kuɗin liƙi a cikin minti goma kacal. Nan da nan filin ya fara cika da dangin amarya da ango ta ko wane ɓangare suna ƙoƙarin nuna tasu bajintar.

Mai waka yaga ruwan manyan kuɗaɗe, ya ruɗe, ya ɗimauce, ya ma rasa irin waƙar da zayyi, sai zabga musu kirarin sun dace da juna da addu'ar zaman lafiya yake yi a cikin waƙe.

Khadija da daidaiku kadan daga cikin mutane ne kawai a zaune, yawancin mutanen sun tafi liki, wasu kuma suna daukar vedios ta wayarsu, yayinda wasu suke taya ma'auratan takawa.

Ta kula da wannan kyakkyawa kuma zankaɗeɗen matashin da suka dinga haɗa idanu da shi da abokinshi, har lokacin idanunsu na kanta.

Jifa-jifa kuma zata ga sun haɗe kawuna suna kus-kus kafin su ɗan saci kallanta, sai kuma suyi ƴar dariya. Koma menene dai tasan tabbas da ita suke yi, duk da cewa dai bata san akan me suke tattaunawa ba, amma sai taji ta tsargu.

Sosai matashin ya burgeta, a kallon farko da tayi masa haka nan ta ji kirjinta ya yanke ya faɗi, sai da taita jan addu'o'i a ranta kafin nutsuwa da walwalarta ya dawo normal.

Ya dauki hankalinta sosai har ta kasa daina satar kallonsa. Abinda ta jima rabon da taji game da wani ɗa namiji shi ne ya burge ta.

Ta rasa da me ya fi sauran maza ne da har yake ɗaukar hankalinta? idan ta kalle shi akai sa'a shi ma ita yake kallo sai taji kamar wani maganaɗisu daga idanunshi suna fisgarta zuwa gare shi. Haka dai taita ƙoƙarin fuskewa tana kauda kanta daga gare shi don kar ta bada mata.

Kamu ya taho gangara, masu rawa duk sun fara dawowa suna zama, yayinda aka fara fitar da drinks da kayan makulashe ana rabarwa.

Sai kwatsam wayarta ta hau ƙara, ganin sunan Ummanta yasa ta tashi da ɗan saurinta ta fita saboda hayaniyar wajen ba zata bari ta jiyo me take cewa ba.

Ta fita can waje tana amsa wayar. Gaban wani windon glass ta tsaya, tana amsa wayar tana ƙarewa kanta kallo da yadda shigar tayi mata kyau kwarai ainun kamar ba ita ba. Ta lumshe kyawawan idanunta tana jin wata natsuwa da annashuwa da ta jima bata ji irinta ba tana shigarta.

Buɗe idanun da zata yi, taci karo da wasu dara-daran idanu lumsassu suna kallonta ta cikin madubin windon. Ta zabura matsa gefe guda a firgice, kafin ta juya da sauri tana kallonshi.

Wannan haɗaɗɗen gayen ne na ɗazu mai nacin kallo, amma shi ɗaya ne yanzu babu wannan abokin nashi.

Wani sihirtaccen Kallon da yake jifanta dashi ba yau ta saba ganinshi a idanun maza ba, amma na shi na musamman ne cike da gayu da ƙasaita irin na ingarman namiji ɗan ƙwalisa da ya saba janye hankalin duk budurwar da ya ɗora ƙwayoyin idanunsa a kanta.

Matuƙar ƙoƙari da jarumta tayi wajen hana kanta sakar mishi kyakkyawan murmushi, a lokaci guda kuma sai tayi ƙoƙarin haɗe girar sama da ƙasa don kar yaga kamar ya samu nasarar sace zuciyarta.

Ya wani rausayar da kai gefe guda ya sakar mata tattausan murmushi, cikin wani irin jan aji da kasaita da bata saba gani a tattare da namiji ba,
   "Hi! Barka da yamma Mai kyau!".

Yuuuu tayi idanunta saboda tsananin daɗin muryarsa, haka kawai sai taji yawun bakinta suna neman kafewa. Wannan wane irin mutum ne kuma mai yake nema da ita da yake kokarin haddasa mata mutuwar barin jiki a lokaci ɗaya?

TSAKANINA DA MUTUWA...! Where stories live. Discover now