*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA ASHIRIN DA HUDU*
Washegarin ranar da aka yi kamun amarya ya kama juma'a, walima za ayi. Da yake da yamma ne walimar don haka da safe suna ta hutawa abinsu.
Babbar kawar amarya Ramlat wadda tunda amarya Khadeeja ta haɗasu suka manne da Khadeeja kamar wasu sanannun abokai, ta kalli Khadeejah lokacin da suke karyawa a dakin da aka musu makwanci da misalin karfe goma na safe.
Tace, "Sister Khadeeja don Allah mu shirya mana ki rakani cikin gari inyi gaisuwar rasuwa?".Khadeejah din ta danyi dumm! Kafin ta gyada kai da ta tuna na zaune baiga gari ba, kuma zaman hakanan dama ya fara isarta.
Don haka suka shirya, wajen karfe sha daya da yan mintuna suka fita zuwa gidan gaisuwar. A cikin napep suka tafi, tafiyar kusan mintuna ashirin da biyar aka ajiyesu a kofar wani hadadden lafiyayyen gida daya sanya Khadeeja taji kanta yana juyawa saboda tsabar girmanshi da kuma haduwarshi. A ranta ta ke raya jama'a wannan gida haka kamar ba za a mutu ba?!.
Cikin nutsuwa suka fita daga napep din, suka gaisa da daidaikun mutanen dake kofar gidan, daga gani rasuwar an kwana biyu da yinta.
Haka suka shiga gidan suka dinga danna kai waje-waje, kai daga ganin gidan kasan kaga inda aka kashe dukiya tayi kuka sosai da sosai.
Bata ma tsinke da lamarin ba sai da suka shiga cikin falon gidan, sai ta kara tsinkewa da lamarin mutanen ganin irin kayan alatun dake shimfide a wajen.
Suka bi kowa suka musu gaisuwa, daga nan ciki suka nufa suka ratsa cikin wani ƙayataccen falo, nanma mata suka gani amma basu kai na falon farko da wuto ba.Bayan sunyi musu gaisuwa ne suka shiga wani daki da ta kula babu mutane a ciki, daga wata matashiyar budurwa kyakkyawa sai wata magidanciyar mata.
Tashi daya taji wani irin yarr! A jikinta lokacin da suka hada idanu da budurwar. Tana kishingide a kasan carpet din dakin jikinta saye da doguwar riga da hijabi, Tally Counter ne a daure jikin yatsar hannunta na dama tana lazumi. Bata san ko me ya hau kanta ba, amma hakanan taji wani irin tausayin budurwar ya ratsa mata har kwanyar kanta. Daga ganinta babu tambaya kaga wadda aka yiwa rashin daya ratsa mata jiki matuka. Yanayin sanyin jikinta da ramar da tayi, tayi fayau fuskarta duk ta komade, ga idanun duk sun shige ciki, sai taji jikinta ya kara yin sanyi.
Nan suka gaisa dasu suka kuma yi musu ta'aziyya. Budurwar da Ramlat ta ambata da 'Haneepha' ta mike zaune da kyar, suka kara yi mata ta'aziyya. Suka zauna shiru-shiru babu mai bakin magana.
Tana jin matar da suka samu tare da Haneepha a dakin tana mata fadan rashin cin abinci da kuma rashin shiga cikin mutane da take yi, a cewarta hakan ai ba shi zai dawo mata da Ummanta ba. Haneepha dan murmushi kawai tayi mai nuna alamun ta jima tana jin makamanciyar wannan maganar.
Basu jima ba suka musu sallama suka tashi suka tafi. Khadeeja ta kara kallon Haneepha lokacin da suka tashi, cikin sa'a kuma itama ta juya tana kallonta. Sai suka samu junansu da yin ɗan musayar murmushi a tsakaninsu.
Haneepha ta daga baki da kyar tace,
"Ramlat na gode kwarai, ku gaida gida", da haka suka juya suka fita daga dakin.
Daga ita har Ramlat babu wanda ya sake yin magana a tsakaninsu.A farfajiyar gidan suka ci karo da gayyar mutane sun shigo, Khadeeja bata maida hankali kansu ba saboda kanta a matukar daure yake da wasu al'amura da suke mata yawo a cikin jiki wadanda ta rasa ta yadda zata kwatanta su a cikin kanta. Abin ya daure mata kai matuka.
Kamar ance mata daga kanki, suka hada idanu da matashin da ke saitinta a cikin jerin mutanen dake tafe, taja ta tsaya cak cikin wani irin tu'ajjibi da mamaki.
Ta yaya hakan zata faru? Shin wannan kaddara ce ko kuwa arashi?!
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari