*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA BAKWAI*
Sam basu ankara da Ɗan Malam ya fita daga cikin ɗakin ba suna ta buɗawa ana ba hammata iska, duk sun ji jiki sun hayayyakewa juna kamar wasu karnuka.
Cike da shammata Karishma ta samu nasarar damƙo na shanun Haly guda ta kai mishi wani mugun fincika kamar za ta tunɓuko daga ƙirjinta, azaba yasa Haly ta yanka wani gigitaccen ihun da yayi nasarar janyo hankalin su Habib suka banko cikin ɗakin a gaggauce.
A haukace kuma cike da matsanancin fushi ta yayimi Karishma ta ɗaga sama ta nunawa mai sama sannan ta kifa ta da ƙasa tim, ƙwal! kake jin sautin lokacin da goshinta ya bugu da tile ɗin da ya mamaye tsakiyar ɗakin.
Ko kafin tayi wani yunƙuri don miƙewa sai jin wani ɓangare na naman mazaunanta tayi a bakin Haly ta gantsara mata wani mugun cizo da dukkan ƙarfin haƙoranta, babban burin Haly so take kawai ta gutsuro naman inda ta damtsa ta ƙarfin tsiya.
Ihu itama ta yanka a gigice tana wani irin gurnani da mutsu-mutsun ƙwatar kai kamar karya saboda tsananin zafi da raɗaɗi.
"Subhanallahi... Halima kina hauka ne? Kasheta za kiyi?"
Habib ya faɗa cikin fushi da mamaki yana ƙoƙarin janye fuskar Halyn daga mazaunan Karishma.Su kuwa Ucee da Abdul dariya suka fashe dashi suna nuna Halima da Habib ya samu nasarar ɓamɓaro bakinta daƙyar, haƙwaranta duk jini kamar wata mayya. Bata gutsuro naman mazaunan ba amma tayi mata mugun rauni, idanu a warwaje sai zazzare su take yi.
Kayan jikinta duk a yayyage, tsagun ɗamammen siket ɗin atamfar jikinta Karishma ta ƙara shi tun daga sama har kasa ana ganin ɗan kamfanta. Rigarta ma an yaga ana ganin rabin ƙirjinta a waje.
Ita kuwa Karishma abin ya fi muni don dama ƙarfi ba ɗaya ba, ko da aka raba su kasa tashi tayi sai malele-kuwa take yi tana jan nishi da gurnani kamar mai naƙuda don tsananin wahala da azaba.
"To tunda kun gama damben ko wacce ƴar iska ta tattara yagaggun kayanta ta bar ɗakinnan kafin inci ubanta. Ƴan iska kawai, dabbobi marassa mutunci. Sai hauka kuke akan namijin da ko darajar tsinken sakacensa baku kai ba. Namijin da ko a kyauta aka ce za a bashi aurenku da ƙarin kyautar gida da mota wallahi bazai amsa ba. Ya kuma ce in faɗa muku duk ƴar iskar da ya sake ganin ƙafarta a inda yake wallahi na lahira sai ya fita jin daɗi. Wawaye kawai sakarkaru....! Duk ku zo ku san nayi",
Ta inda Habeeb yake shiga ba ta nan yake fita ba sai da yayi musu tass! Kafin ya juya ya bar dakin.Haly bata saurare shi ba tana miƙewa ta shige cikin ɗan ƙaramin banɗakin da yake cikin ɗakin tayi wanka da ruwa mai tsananin zafi, ko da ta fito daga ita sai towel kai tsaye gurin kayan Ɗan malam ta nufa ta ɗauki wata jallabiyarshi ta saka a jikinta ba tare da jin kunyarsu ba.
Cikin ƙanƙanin lokacin ta tattara kayayyakinta tayi rolling ɗin gyalenta ta fice daga ɗakin tana watsa musu wani mugun kallo, da ta kalli Karishma kuwa ƙwafa tayi haɗe da girgiza kai, irin alamun za su haɗu dinnan.
Ita kuwa Karishma kasa tashi tayi sai da Ucee ya taimaka mata. Ya kaita cikin bayin ta watsa ruwan zafi itama ya miƙa mata jallabiya ta saka, sannan ya fita da ita ya tare mata napep zuwa gida.
Ko a cikin napep ɗin kasa zama tayi, ita ba a goho ba, ita ba a kwance ba, abin tausayi abin dariya, ta tsinewa Haly ya fi dubu a fili da cikin zuciyarta. Da azaba ya ishe ta ma maimakon gida chemist ta cewa mai napep ɗin ya kaita.
'Dole in nemi kashin kaza in shafa a gurin cizon nan dan haƙoran tsinanniya su zube.'
Ta dinga faɗin haka a cikin zuciyarta.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari