BABI NA UKU

160 40 2
                                    

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*TSAKANINA DA MUTUWA*

©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals

*BABI NA UKU*

Ta yi kuka sosai har ta gode Allah, ƙirjinta yayi mata nauyi sosai. Zuciyarta sai suya da raɗaɗi take mata. Tun bayan komawarsu gida daga asibitin da mahaifiyarta ta kaita aka duba ta da bata magunguna ta kasa kataɓus ko aikata wani abin kirki.

Fiye da awa biyu da rabi kanta na kwance akan cinyar mahaifiyarta tana zubar da hawaye masu tsananin zafi ta raɗaɗi. Lokaci bayan lokaci kuma sai ta ja majina ta haɗa da sauke nannauyar ajiyar zuciya irinna wacce ta daɗe tana kuka.

   "Kiyi haƙuri Haneepha."
Hajiyar ta sake faɗa a karo na ba adadi tana shafa lallausar suman kanta.

    "Ya zanyi Umma? wallahi tallahi ko kaɗan ba ni da wata masaniya ko sila ta mutuwar duk waɗanda suke nema na da aure..."

   "Na sani Haneepha ba sai kin rantse ba. Jarabta ce kawai irinta Ubangijin halittu don ya gwada ƙarfin imaninki da namu. Ki cigaba da haƙuri har muga iya abinda Allah zaiyi"
Ta faɗa da tattausar murya mai baiyani tsananin damuwa da tausayin tilon ƴar tata.

Bata sake cewa komai ba, lumshe idanu tayi a ranta take ayyana kullum de haka Hajiyar take cewa, yaushe ne samarin da take niyyar aure za su daina mutuwa har ita ma ta samu shiga daga ciki? kullum shekarunta ƙara yawa suke yi, ga mahaifinta ta lura matsalar da take ciki ko a jikinsa wai an tsikari kakkaura.

*******

A dabarance ya sake ɗan juyar da wayar don kar taga abinda yake kallo. Saboda tsarguwa ma sai ya danna gefen wayar ta shiga key ya ajiye wayar a cinyarsa.
   "Yauwa! ina jinki? me kika ce?"

Ta fara bubbuga ƙafafu a ƙasa tana direwa cike da taɓara da sangarta, ta turo baki gaba a sakalce ta ce
   "Ni dai Allah barci nake ji My dear. Mu kwanta kawai,  tunda baza kayi kallon ba nima na haƙura. Kallon ba daɗi tunda ba ka yi."

Tattausan murmushi ya sakar mata, ya kamo hannunta ya zaunar da ita a cinyarsa bayan ya aje wayarsa a kan kujera. Hannunsa biyu yasa ya zagaye cikinta dasu sannan yasa fuskarsa a wuyanta yana sansana ƙamshin humran da ta shafa.
   "Yanzu dai ga ni gare ki Ammatana, zaɓi da lokacina duk naki ne sai abinda kike so zanyi. Kallon kike son muyi ko kuma barcin kike so muyi? Daman wani aiki da aka bamu a islamiyarmu ta kafar sada zumunta nake so inyi amma tunda kina son lokacina dole in kauda komai inji dake Ammata."

Murmushi ta sake tana jin wani alfahari a zuciyarta, kanta sai ƙara girma yake saboda matuƙar jin daɗin kalaman da suka fito daga bakinsa. Mijinta nata ne ita kaɗai babu wacce yake da lokacin kulawa, a gida da waje baiwa lokaci da abinda take so muhimmanci shi ne abinda yasa a gaba. Ko cikin ƙawaye da ƴan'uwa tana alfahari da haka. Hannuwanta ta ɗora a saman nasa da suke cikinta ta fara cewa
   "Muje mu kwanta kawai Mijina, na san kaima ka gaji tunda yau ka yini a ofis, gobe kafin ka tafi ofis sai kayi aikin islamiyar."

   "Angama Ma'am!"
Dariya suka yi gaba ɗaya ta miƙe ya kama hannunta suka nufi ɗakin barcinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci suka gama shirin bacci sannan suka kwanta tana maƙale a jikinsa, addu'ar bacci ya fara karantawa a fili tana biye da shi har ya gama suka shafa a fuska haɗe da shafe jikinsu gaba ɗaya.

Da yake gwana ce wurin saurin barci nan da nan sarkin ɓarayin yayi awon gaba da ita. Minti uku ya ƙara don ya tabbatar barcin nata yayi nisa a hankali ya zare jikinsa daga nata ya maida mata da filo a madadinsa ya fita falo.

Wayarsa ya ɗauka da sauri ya danna kiran lambar tsohuwar budurwarsa Ashfat, ya san ko ya hau online ba lallai ya same ta on ba. Ƙasaitacciyar mace ce da bata jira sai dai a jira ta.

TSAKANINA DA MUTUWA...! Where stories live. Discover now