*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA BIYU*
Wani irin dariya ta ɓarke da shi da ya sake bayyana girman wawakeken bakinta, lokaci ɗaya kuma duk girman bakin ta tattare shi ta tsuke guri ɗaya ta cono shi gaba kamar bakin kare. Ta kwance haɓar zaninta ta ciro namijin goro da ɓawonshi ta hurga a baki ta tattattaune, ta buɗe gorar lacaseran da yake gabanta ta kafa a baki ta fara ɗaɗɗaka, bata sauke ba saida ta shanye tas tayi hurgi da goran a wani ɓangare na tafkeken falon, ta buɗe baki kamar za tayi hamma sai kuma saki ƙaƙƙarfar gyatsa da bakinta mai fitar da ɗoyi kamar an buɗe bakin masai.
Da sauri Hajiya tasa hannu biyu ta rufe bakinta, a wayance kuma taja jikinta baya ta ɗan matsa cikin kujerar tana yamutsa fuska cike da ƙyanƙyani da jin haushi. A zuciyarta take ayyana
'In banda Lariyar na da matuƙar amfani a gare su tabbas da tuntuni ta yanke alaƙa da ita.'"Uhmmm! kina jina Hajjaju?"
Da sauri ta katse tunanin da take yi ta amsa da
"Ina jinki Lariya""A ƴan majalisu unguwar dosa akwai wani Alhaji Lukman..."
"Haba Lariya, ke fa daɗina dake baki iya sirri ba, murya ce dake tubarkallah kamar na garjejen gardi. Ki sassauta murya ƙasa ƙasa mana, dukda gidan babu kowa amma ai iska ma bata da sirri. Yauwa ina jinki!"
Sai da ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta turɓune fuska kamar an sheƙa ma kakkauran ƙullu tafasasshen ruwa, ta watsa mata wani mugun kallo sannan ta ci gaba da magana da murya mai bayyana ɓacin rai.
"Hajjaju miye haka? kin sanni sarai ba na ciki da wulaƙanci da rainin ajawali. Daman fa tun ɗazu ina lura da yadda kike ta wani gyatsine kina min kallon uku-ahu. Idan kin san yau bakya cikin yanayi tun wuri in cikawa buje na iska in ƙara gaba...""Haba mana Lariya.! Daga magana sai cibi ya zama ƙari? kinga ungo cikon kuɗinki na rannan ma don ki ji ƙarfin bani rahoto."
Ta buɗe jakar dake ajiye kusa da ita ta ƙirgo ƴan ɗari biyar sabbi kar ta miƙa mata guda ashirin. Sannan ta gyara zama ta matsa kusa da ita sosai ta ce
"Yauwa to ina jinki, ki rage murya sosai don Allah"Saida ta kalmashe kuɗin ta cusa a lalitar dake cikin patarinta sannan tasa hannun dama ta rufe bakinta ta ƙara matsawa daf da Hajiyar ta fara koro mata bayanin da ta take tafe da shi na gidan wani hamshaƙin mai tashen arziki a unguwar dosa.
"Kin tabbatar da abinda kike faɗa min kuwa Lariya?"
"Ƙwarai da gaske Hajiya. Ba fa yau muka fara aikinnan ba kin san babu yadda za ayi in kawo miki maganar da ban tabbatar ko ji ko in gani ba. Don in ƙara tabbatarwa ne fa dukda ina da ƴan aiki a ƙasa nace mata babu, nayi ta shige da fice da bugun ruwan cikinta don in gano sirrin komai na ahalin gidan, a ƙarshe ma ƴata nakai mata da sunan ta fara taya ta ƴan aikace aikace kafin a samu wata. Sai da na tabbatar da komai sannan na taho miki da zancen."
"To madallah! aikinki yayi kyau Lariya. Za ki iya tafiya..."
"Ya hausar zan iya tafiya baki bani ko na mota ba Hajiya?"
Tayi maganar tana washe baki.Girgiza kai Hajiyar tayi a zuciyarta tana mamakin masifaffen son kuɗi irinna Lariya, ta buɗe jakar kusa da ita ta sake ƙirgo ƴan ɗari biyar guda goma ta miƙa mata
"Ungo wannan! Idan aiki yayi kyau za ki ga gwaggwaɓar sakamako."*ADON TAFIYA*
Shekaru bakwai da suka wuce suka hadu da Sadeeq, lokacin shekarunta sha hudu. Tana aji na biyar a sakandare gab da zata shiga aji uku.
Kyakkyawan matashi ne mai jini a jika, wanda yaje makarantar da suke a matsayin corper. Duk da cewa yan aji hudu yake koyawa, hakan bai hana kaddara yin halinta ta hanyar hadasu ba a wata rana da suke cikin tsakiyar rubuta jarabawar 'mock'.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari