*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA TAKWAS*
Ya gyara zama sosai akan kujera, ya waiga gefe da gefe hagu da dama kamar mai neman wani abu. Sai da ya tabbatar babu motsin kowa sannan ya tsaida idanunshi guri ɗaya. Ya ƙurawa amintaccen yaronsa Zalɓe idanu yana karantar yanayinsa, sai kuma ya fara magana da muryarsa ƙasa ƙasa.
"Zalɓe ka san me nake so?""A'a sai ka faɗa Your Excellency"
Zalɓe ya amsa da muryar dabanci, yana ƙara tattara dukkan hankali da nutsuwarsa akan Alhaji Safiyanu."Jarirai nake so sabbin haihuwa guda uku! maza biyu mace ɗaya. Ka tabbatar sun samu nan da kwanaki uku ta ko wace hanya kuma ta ko wane hali. Idan an gama haɗa su ka kaimin inda aka saba ajiyewa. Kana ji na? ina fatan ka fahimce ni?"
"Ƙwarai na fahimta. An gama Ranka ya daɗe"
Wani yar ƙaramar jaka dake ajiye kusa da shi ya buɗe zip ɗin, ya ɗauko bandir na ƴan dubu ɗai-ɗaya guda biyar ya mika mishi,
"Amshi wannan! idan komai ya kammala zan ƙara maka kamarsu.""Godiya nake Ranka ya daɗe."
"Yauwa kana iya tafiya, sai na ji ka."
Sadaukarwa yake so yayi ta musamman ga jagoransu ba don an umarce shi ba sai don kawai ya faranta masa kamar yadda shi ma yake biya masa buƙatunsa ako wane lokaci.Zalɓe yana gaf da ficewa daga falon Haneepha ta sanyo kai ciki bakinta ɗauke da siririyar sallama.
Da kallon tsarguwa da tsana ta bi Zalɓe har ya ƙarasa ficewa daga falon, haka kawai ta rasa dalilin da yasa tun ganin farko da ta fara yiwa Zalɓe a gurin mahaifinta taji sam bai kwanta mata arai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta watsar da tunanin komai ta ƙarasa cikin falon bayan ta sake yin wata sallamar ya amsa mata.
Da wani irin kallo data kasa fassarawa ya bita har ta nemi guri ta zauna a kusa da ƙafafunshi.
"Abba barka da hutawa",
Ta furta a hankali kamar mai tsoron magana."Me yake damunki ne naga kin faɗa Haneepha?"
Ya tambayeta cike da kulawa yana mamakin ramar da yaga ta yi, bai jira amsarta ba ya ci gaba da cewa
"Ko kina da wata matsala ne baki faɗa min ba? Idan kuɗi kike so kin san ba matsalarmu bace, dukiya na tara wanda nan gaba har tattaɓa kunnenmu baza suyi talauci ba. Faɗa min matsalar ta nawa ce?"
Ya karasa maganar cikin faɗa-faɗa zuciyarsa cike da jin haushin yadda Haneephar take kasa sakin jikinta a mafi yawancin lokuta balle har ta ɓarje guminta ta wataya tayi wadaƙa da dukiya yadda ya kamata."Abba ba matsalar kuɗi ba ce..."
"To matsalar ta mecece? Damuwar ta mecece? Me kike buƙatar samu a duniyar nan da kuɗi bazai iya sayenshi ba? Kinsan dai in wani abu kike so da ya shafi neman alfarmar wani ko wata a ƙasar nan har ma dana ketare ina da ƙarfi da ikon da zan shiga ko ina ne in nema miki alfarma don ki samu abinda kike so."
Na wasu ƴan daƙiƙu shiru tayi kawai tana kallon kan kafet, zuciyarta cike da mamakin halin mahaifinta. Shi dai ko wane lokaci ya bata kuɗi dai ta siyi ko me take so. An faɗa mishi ko wace damuwa ce kuɗi take iya magancewa? Ga babbar damuwarta nan mace-macen da masu neman aurenta suke yi akai-akai amma shi ko a jikinsa.
Bai taɓa zama sun tattauna da mahaifiyarta ko ita don ya nuna damuwa da alhininsa akan mutuwar da samarinta suke yi ba. Tun abin yana bata mamaki da takaici, ya koma yana ci mata tuwo a ƙwarya yanzu kam har ya daina. Kawai ta zubawa sarautar Allah ido ne tana addu'a domin tana da tabbacin Allahn da ya halicce ta shi zai yi mata maganin damuwoyinta.
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari