*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*
Da fari duk sunyi tsaye ne cirko-cirko saboda tsananin ruɗewa da tashin hankali sun rasa me ya kamata suyi. Sai da Mal Inuwa mai gadi ya ankarar da su batun ruwa sannan suka shiga rige-rigen ɗauko ruwa domin su yayyafa mata.
Tsawon wasu daƙiƙu can Allah yasa ta ja wata irin doguwar numfashi, a hankali ta ci gaba da sauke numfashi har numfashin ya daidaita, sai kuma ta fara ƙoƙarin tashi zaune.
Su suka taimaka mata ta tashi zaune, suka matsa da ita ta jingina da jikin kujera guda ɗaya dake ajiye a ɗakin.
Ɗaya bayan ɗaya ta dinga binsu da kallo kamar wacce ta warke makanta, mai gadi da sauran ma'aikatan gidan maza ganin ta dawo hayyacinta sai suka mata sannu ba tare da sun jira amsawarta ba suka fice daga ɗakin.
Jin kanta da gefen fuskarta inda sashin yatsu suka fito kamar a cikin wuta suke saboda tsananin zafi da yadda suke buga mata.
Hannu tasa ta dafe kan da ya mata wani irin nauyi gingirim kamar ba nata ba, tana ta ɗan girgizawa ko ta samu ta ji ya dama-dama, amma duk da haka yana nan da nauyi da ciwon da yake mata.
Baki ta buɗe da niyar yin salati da hailala, sai taji harshenta yayi mata wani irin nauyi kamar an sanya sarka an ɗaure mata shi, ga wani irin cika da harshen yayi a bakinta.
A tsorace ta zazzare idanu tana kallon su Talatu, ta sake yunƙurin buɗe baki da nufin ta amsa sannun da suke ta jejjera mata akai-akai nanma magana ya ƙi fitowa, sai harshen da ya ƙara cika mata baki.
Abin ya girme ma tunaninta, hankalinta idan yai dubu ya tashi.
Ta dinga ɗaga baki tana maidawa ta rufe ba tare da ko sautin 'a' ya fita daga bakinta ba.Can kasar zuciyarta da ƙirjinta kuma wani irin abu ne ya danneta kamar mai masifar nauyi kamar gingimemen dutse, sai kokawa take da numfashinta da yake fita daƙyar.
Wani abin ƙarin tashin hankali da ban tsoro a gare ta shi ne yadda ko a cikin ranta ta kasa ayyana yin bismillah balle ayi zancen ta furta salati a fili.
Ta sadaƙar da rayuwar duniya, ta gama sarewa lallai ba ta da sauran shan ruwa. Da hannu ta yiwa su Aliya nuni da alamun su fice su bata guri, ta gode.
Sum-sum suka fita kowa daga cikinsu yana furta Allah Ya bata lafiya da kuma sauki. Suna bada baya kuma sai suka fara maida yadda aka yi cikin tsananin mamaki da tu'ajjibin abinda yake faruwa mai matukar daure kai.
Kowa da irin abinda bakinshi yake furtawa dangane da halin da Haneepha ta samu kanta, da kuma wanda Hajiyar ke ciki. Maganar da duk suka fi raja'a akai ita ce da alama daga uwar har diyar muggan aljanu ne suka buge su shi yasa wadannan abubuwa masu ban mamaki suka faru dasu cikin ɗan kankanin lokaci.
Haneepha da taga ba sarki sai Allah komawa ƙasan carpet din dakin tayi tai male-male, ajiyar zuciya kawai take saki akai-akai. Zuciyarta da kwalwarta gabadaya jinsu take a kulle babu abinda suke iya tabuka mata.
Wannan dalilin yasa ta ƙara sarewa da rayuwar duniya, ta lumshe idanunta wasu zafafan hawaye suka kwaranyo daga cikinsu, komai nata ya tsaya cak! Aniyarta mutuwa ne zayyi awon gaba da ita saboda matsanancin zafin dake ƙara zagaya ilahirin jikinta, ta tabbatar wannan azababben ciwo na lokaci ɗaya sam ba na tashi bane.
===¤¤¤===
Yana daga cikin kogon da wani ƙaton madubin tsafi a hannunshi, dukkan abinda ke faruwa yana ji kuma yana gani tarwai kamar a gaban idanunshi al'amarin ke gudana.
![](https://img.wattpad.com/cover/282387074-288-k586079.jpg)
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
TerrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari