BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA

136 27 4
                                    

*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*

*TSAKANINA DA MUTUWA...!*

©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals

*BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA*

Yadda ya isa gidan a haukace, fuskarsa bayyane da matsanancin tashin hankali da damuwa sai ka rantse da Allah har a zuciyarsa hakan take.

Saboda tsabar dimuwa da tashin hankali motar tasa ma a waje ya barta, ƙofa a buɗe ya bari ko makullin bai samu zarafin zarewa ba ya shiga gidan afujajan kafa babu ko takalmi. Idonshi a rufe bai ma kula da maza maƙwaftanshi da suka fara yiwa gidan tsinke sunyi dako-dako a ƙofar gidan ba.

Kasancewar rasuwar ya faru ne an kira sallar la'asar a babban masallacin da yake kusa da gidan, amma ba'a tayar da sallar ba. Da wannan damar ma'aikatan gidan maza suka yi amfani wajen sanarwa da Liman shi kuma ya sanarwa da mamu bayan an idar da sallah.

Shi yasa ko kafin ya dawo ƙofar gidan yayi danƙam da bil'adama. Da yawansu duk da basu shaida Hajiya Rasheeda a kamannin fuska ba, amma sun shaida kirkinta da son kyautatawa wanda ta fi, saboda duk juma'a kyakkyawan abinci da abin sha take yi da uban yawa ta aike da shi masallacin. Kuma idan ana neman taimako in dai Liman ya aike mata tana taimakawa gwargwadon hali. Shi yasa rasuwar ta dake su ba kaɗan ba, babu abinda yake fita a bakunansu sai kyakkyawan fatan halinta na gari ya bita, da addu'ar Allah ya gafarta mata Ya kai haske cikin kabarinta.

Alhaji Safiyanu kai tsaye babban falon gidan ya nufa inda ya hangi takalma da yawa a ƙofar falon, yana ta saɓa babbar riga yana sharce zufa, lokaci bayan lokaci sai ya ɗora hannuwansa biyu akai kamar zai rusa ihun wayyo Allah na.

   "Alhaji barka da zuwa. Ya muka ji da haƙuri? Ubangiji Allah ya gafarta mata."
Ire-iren maganganun da ke fita daga bakin matan da ke zazzaune a falon kenan suna kallonsa da fuskokinsu mai ɗauke da tausayawa. Da yawa daga cikin matan hannayensu dafe da kuncinsu suna jimamin rasuwar.

Bai samu zarafin amsa gaisuwar ko mutum ɗaya daga cikinsu ba, zazzare idanu kawai yake yi yana kalle-kalle. Da ya kai gwauro ya kai mari bai hangi gawar Hajiyar shimfiɗe a tsakiyar falon ba sai ya saka kai ya nufi hanyar da zai sada shi da ɓangarenta cikin sassarfa.

A falon Hajiyar ya yakice babbar rigar jikinshi ya wullar, ya cire hular kansa ya jefar ta faɗa can kusa da dining. Ƙarfi da yaji ya fara matso hawaye yana jan hanci sannan ya tura ƙofar ya faɗa ɗakin a firgice.

Idanunshi basu sauka ko ina ba sai akan gawar Hajiya Rasheeda, shimfiɗe a tsakar ɗakin wasu mata su biyu suna zaune gefe da gefenta suna zare kayan jikinta a sannu-sannu. Da alamun wanka za suyi mata, domin sun tanadi komai a kusa da su. Sai wata dattijuwa ita kuma zaune gurin kanta tana warware kitson da yake kanta.

Fuskar marigayiyar tayi fayau tayi haske, ta rame sosai daga cikar da fuskar take da shi. Sai fuskar ta ƙara kyau hancin ya ƙara tsawo, idan ka kalleta da kyau ma sai a zaci murmushi take yi. Allahu akhbar, mai rai baƙon duniya. Allah Yasa mu cika da imani. Kamar a kirata ta amsa.

Can gefe guda Haneepha ce zaune ta haɗe kai da gwuiwa tana sharɓen hawaye, duk yadda aka so da ta fita, ta bari a kimtsa gawar ayi mata sutura ta ƙi fita. Ta ce komai ayi mata a gabanta, da suka ce mata ba a son kuka mai ƙarfi ko surutu cewa tayi baza ta yi ba. Hawayen ma sai da taga an fara kimtsa gawar sannan ne suka samu sukunin diga akan kumatunta, da idanunta sun gama soyewa saboda azabar kukan da ta ci lokacin data tabbatar da cewa Ummanta ta bar duniya.

A slow motion ya ƙarasa kusa da gawar ya tsugunna gwiwa a sanyaye, tsawon wasu daƙiƙu ya tsura mata idanu yana kallonta, zuciyarsa na tunano masa kyawawan lokuta masu tsawo da suka gabatar tare da ita.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da kwashe hawayen dake mishi zarya a fuska, ya yiwa matan nuni da umarni akan su fita shi zai yi mata wanka. (Daman abinda aka fi so kenan idan da hali miji ya wanke matarsa), hakan yasa suka tattago Haneepha tana turjewa da bori, da kyar suka fita da ita. Dakin ya rage daga shi sai gawar.

TSAKANINA DA MUTUWA...! Where stories live. Discover now