Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DAvZ5MDoOVSLXMUGsb6DKc
*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA GOMA SHA TARA*
Shiru tayi kawai tana kallonsa, tsawon lokaci har ya fidda tsammanin za ta tanka masa. Ya sake gyara zama yana niyyar ci gaba da zuba mata magiya ta ɗaga mishi hannu alamar dakatarwa.
"Zan yi haƙuri..."
"Alhamdulillah! Allah Na gode maka. Na gode my luvly Zee, daman na san baza ki iya dogon fushi da khal..."
"Dakata mana Malam, ai ban gama ba ka katse ni."
Ta dakatar da shi tana sake haɗe rai, sannan ta watsa mishi hararar sama da ƙasa.Tsumu yayi yana kallonta, a hankali murnarsa ta fara komawa ciki. Sosai ya Marairaice fuska, abin tausayi sak!
"Yi haƙuri Ammata na. Ai na zaci kin haƙuran ne, kin san na sha wahala a ƴan kwanakinnan! Ina jinki, ni dai don Allah don Annabi ki tausaya min.""Zan haƙura. Amma bisa sharaɗi ɗaya."
Ta faɗa kai tsaye har lokacin fuskarta babu walwala."Sharaɗi kuma?"
Ya tambaye ta da mamaki a fuska da muryarsa."E! Sharaɗi. Idan ka amince da sharaɗi na yanzunnan sai mu tattake guri a maida magana a wuce gurin kamar ba'a yi ba."
"Menene sharaɗin naki? ina jinki"
Ya amsa yana sake dubanta da maraitaccen kallo mai ɗauke da saƙon ta tausaya masa."Sharaɗin nawa shi ne ka faɗa min gaskiyar wace ƴar iskar yarinya ce ta fara ɗauke hankalinka daga kaina. Domin ba tun yanxu ba ina lure da halin da kake ciki. Na yi shiru ne kawai kamar ban san komai ba.
Idan ka fita aiki baza ka dawo da wuri kamar yadda ka saba ba, idan ka dawon kuma wani lokacin sai ka tsiri wani uzurin mare muhimmanci don dai kawai ka sake barin gidannan.
Ga wani kaffa-kaffa da shegen tsaro da kake kafa ma wayarka, bini-bini da na ɗan kauce zan ganka ka duƙufa kana chatting. Lokuta da dama ina kallonka kayi ta zabga murmushi kai kaɗai.
Don Allah yau dai ka faɗa min me kake ciki ne? Ina tsananin sonka Mijina, kaima ka san da haka. Amma Allah na gani waɗannan baƙin halayyar da ka tsiro min da su suna saka ni jin shakku da zarge-zarge kala daban-daban a zuciyata game da kai.
Ina jin tsoro kada shaiɗan ya ƙara samun galaba akanmu karo na biyu har ta kaimu ga mu rusa kyakkyawan tubalin zamantakewar auren da muka faro akai.
Ka faɗa min komai don Allah, kar ka ɓoye min komai. Ko da kuwa jin gaskiya daga bakinka zai ƙona min zuciya, ka faɗa min, ko kana neman aure ne kake ɓoyewa baka so in sani?"
Da sauri ya girgiza kai alamar a'a! wani zazzafan gumi yana kwaranyo mishi tun daga tsakiyar kwanyar kansa zuwa fuskarsa, dukda sanyi A.c da ya wadaci falon.
Murmushin takaici da ƙunar zuciya ta saki, ta ƙara matsawa kusa da shi sosai cinyoyinta na gogan nasa. Ta riƙo tafukan hannayensa a cikin nata. Ta ci gaba da magana a tausashe
"Bari ka ji Mijina. Ba mafita bane ɓoye min ɗin da kake ƙoƙarin yi. In ji gaskiya daga bakinka tun a karon farko zai fi min sauƙin jin zafi da raɗaɗi gami da ƙunar zuci da in ji ana wai-wai a gari.Kyakkyawan zamantakewar aurenmu nake so mu gyara mu ci gaba da tsarkakewa ba tare da zato ba.
Don Allah ka faɗa min, me yake faruwa? To ko akwai wani abu da nake yi ne wanda baka so amma ka kasa sanar min...?"
YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari