*FIKRAH WRITERS ASSOCIATION*
*TSAKANINA DA MUTUWA...!*
©Fareeda Abdallah & Jeeddah Lawals
*BABI NA ASHIRIN*
Wata irin kwafa tayi cikin kunar zuciya tana jin yadda ranta yake wani suya da kara tafarfasa. Ai bata sani ba! Tayi amanna da tasan cewa shine in charge din wajen da babu abinda zai sanyata zaman jira har ta bata lokacinta a banza tana jiranshi kamar wata sokuwa.
Tayi zamanta anan bata yi yunkurin tashi ba har sai da daya nurse din ta fita daga ofis ta kuma sanar da ita cewar yana jiranta, sannan ta tashi akan kafafunta da kyar ta tura kofar ofishin ta shiga fuskar nan tata a make kuma a cune waje guda. Kai daga ganinta kasan kaga wadda kiris take jira ta fara zuba ruwan rashin kirki.Ofishin nashi madaidaici ne, ko'ina a share kal sai tashin kamshin freshener mai dadi yake yi.
Ta ja kujerar da take fuskantarshi ta zauna ba tare da uffan ta fita daga bakinta ba, sai shine ya daga baki ya furta mata, "afuwan, wasu muhimman abubuwane suka tsayar dani... Me ke tafe dake ne?".Bata da zabin da yafi ta daga baki ta fara zuba mishi bayanin transfer din da aka yi mata zuwa nan, a nutse take bayanin nata daki-daki, sai dai kana ji kasan cewa akan dole take yi ba wai don ranta yaso ba. Shi kuwa kallon yadda dan bakinta yake motsi kawai yake yi, da yadda kananun fararen hakoranta suke dan fitowa idan tana maganar.
Sai data gama yaga ta tsaya tana kallonshi sannan ya ankara da cewa ta gama koro bayanin nata, nan ya ja fuska kamar ba shine wanda yake kare mata kallo yanzu-yanzu ba, ya duba jerin sunaye har ya binciko sunan nata, "Haneepha Safiyanu, right?".Ji tayi kamar ta kai hannu ta shakoshi don takaici, ta dai daure bata aikata danyen aikin da zai jefata bayan kanta a take-yanke ba, ta gyada mishi kai.
Sai shima ya gyada kan nashi cikin alamun fahimta. Bai kuma kara cewa da ita komi ba sai ya cigaba da daga files-files yana cike wasu, tsayin mintuna fiye da biyar, bata ce mishi ci-kanka ba, amma fa ta gama shaka yadda yakamata.Sai zuwa can ya maida files din ya rufe, yace "muje ko?", ya na tashi tsaye tare da gyara maballan lab coat dinshi. Ta mike ta bi bayanshi har zuwa inda taga nurses sun taru, anan ya gabatar da ita a matsayin wadda za tayi aiki dasu na yan satittikan da zasu biyo baya. Daya gama wannan kuma sai ya dubeta yace, "idan kun tashi ki zo ofishina kafin ki tafi".
Ko kallon inda yake bata yi ba ma ta dage kanta sama. Dan murmushi kawai yayi ya juya abinshi.Wata sister Maryam ce tayi mata jagora da nuna mata wajaje, nan da nan ta fara aikinta cikin kwarewa da sanin makamarshi don kuwa tana son aikinta kwarai da gaske Su kansu nurses din wajen sai da suka ga bambanci.
Bata kara tashi tunawa da wani Dan Malam ba sai bayan da suka tashi taje zata shiga motarta ta hangi tashi sannan, taja wani dogon tsaki har da hadawa da murguda baki kamar yana wajen, ta shige motarta ta tasheta a sukwane ta tafi.Gidan nasu yan aiki kadai ta samu, da alama mahaifinta ya tafi wajen harkokinshi, ita kam bata wani damu ba don dama ba son haduwa take yi dashi ba.
Haka kawai cikin yan kwanakin take tsintar kanta cikin matsanancin faduwar gaba idan ta hadu da mahaifin nata, ga wani shakkarshi da take ji haka kawai siddan.Kai tsaye dakin mahaifiyarta ta wuce, ta sameta jiya-i-yau, yadda ta barta da safe babu wani cigaba. Ta shiga bandakin dake manne da dakin ta watsa ruwa tare da yin alwala, kicin ta wuce ta sanarwa yan aiki abinda take bukatar a kai mata kafin ta koma dakin Umman. Anan tayi sallah, kafin ta gama sun kai mata faten doya da yaji manja da vegetables da busasshen kifi, ga lemun tataccen kwakwa da abarba daya dau sanyi. Ta zauna ta ci abincin sosai, yar aiki taje ta dauke kayan. Ita kuma ta koma kan kujerar hutun dake gefen gadon ta zauna.
Wayar Ummah ta daga ta kira babban hadimin gidan wanda yake kula da sayen abubuwan da babu, ta sanar dashi tana bukatar sabuwar waya da kuma kalar wadda take so, kafin ta kashe ta kara kiran Anty Hannatu kanwar Ummah dake aure a Abuja. Sunyi da ita a ranar zata zo saboda babu kowa a wajen Umman nata. Dangin ma sai daidaiku ne ke shigi da ficin dubata saboda Daddynsu yayi kane-kane ya hanata hulda da mutane, da ba don ta kasance mai matukar son zumunci bama da hatta da yan uwanta na jiki ma ba za tayi zumunci dasu ba sam.

YOU ARE READING
TSAKANINA DA MUTUWA...!
HorrorA dunƙule labarin ƙaddarorin rayuwa mabanbanta daga mabanbantan taurari