🧟♂️🧟♀️☠️☠️🧟♂️🧟♀️
*RUHI BIYU*
_[a gaangar jiki daya]_
*RETURNS*🧟♀️🧟♂️☠️☠️🧟♀️ 🧟♂️
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
_Kungiya d'aya tamkar da dubu._*_SPECIAL EDIT 2021/2022_*
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
+2349077974042*REPORTS*
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*📣📣📣SANARWA SANARWA📣📣📣*
_Ga masu Bin littafin Kofar aljali littafi na biyu Ina Mai Baku hakuri game da rashin posting da kuka ga ba'ayi gaskiya abubuwa ne sukayi yawwa..._
_dan hakan Ina Mai Mika sakon ban hakuri ga fans inshallah bada jimawa ba zaku jini love you all_*😷😷STAY SAFE... STAY AT HOME😷😷*
*FREE BOOK💯✅*
*📚LITTAFI NA BIYU*
*EPISODE_0️⃣9️⃣*"Did you need some help?."
Haka Alhaji ya jiyo,yayinda ya Dago idanunsa ko sai yayi arba da mu'azz tsaye gabansa.."Yes."
Aiko Saida ya furta hakan kafin ya tuno wannan fuska...
Mu'azz ko sauka yayi yasa hannu a wuyarsa ya d'aga shi ahankali har saida kafarsa ta daina taba kasa.
Sauke idanun da mu'azz yayi a wannan gurin ko sai Ramin ta Marne...
Alhaji Sunusi ko akayi jifa dashi...gefe guda,daga Idanu da zaiyi ya soma bada hakuri.Cikin kasaita Mu'azz din ya karasa wajensa inda ya tsunkuya ya sake saka hannu Hala yadda ya d'aga shi da farin,ya Kuma Yi jifa dashi Amma Kuma banbancin wannan jifa Dana farkon ko shine Bayan yayi jifa dashi saiya bude tafin hannun sa ya soma taku a hankali yana binsa.
Aiko shi Alhaji Sunusi daya fasa bangon dake bayansa Mai makon ya Fadi kasa A'a sai ya tsaya still yayinda yake karasawa duk bangon daya Tarar Yana yima Mu'azz hanya,ta hanyar Fasawa.Haka yayi ta fasa bago iri Daban Daban mu'azz na biye dashi bangon karshe daya fasa ko saiya fada cikin dakin Wanda cikin dakin ko boka bakin bawa ne ke ciki yayinda yake Shan azabebbiyar Duka a hannun Naina.
Fashewar bangon ne yasa Naina ta juya Idanu Haka zalika Bakon Nan ma...
Ido suka Kurawa wannan hanya da Alhaji Sunusi fasa yayinda ya fado cikin mayinwacin Hali.Aiko Bayan yayewar kura saiga Mu'azz ya sako Kai cikin wannan daki,ganin Haka da Naina tayi saita rikide ta dawo suffar Mu'azz itama.
Ganin Haka yasa Bokan ya zura idanu,bayan sun hada Idanu sai Wannan mu'azz din Daya shigo dakin ya dudi bakin bawa yayinda yace dashi.
"Bakin bawa barka da sake hadewa."
Ya Fadi hakan yayinda ya hade fuska ya Kuma d'aga tafin hannu sama,bayan ya d'aga hannun saiya dungule yatsun bayan Nan ya saukar da hannun cikin zafin nama.Karan Nan da suke jiyowa yayinda Alhaji Sunusi ke farfa bangon Haka suka sake jiyowa tana sauka ta saman su.
Boka bakin bawan daga Idanu yayi Yana jiran Mai zai fado daga saman dakin Aiko daga karshe Faruq yayi arba dashi,shima dai cikin mummunar yanayi ya fado dakin.
ganin Haka yasa Bokan yaje da saurin wajen gangar jikin Faruq din,Zuwan nasa keda wuya saiya ji ya tashi sama,yayinda yake jujjuyawa a hankali kaikace a duniyar taurari yake.
YOU ARE READING
RUHI BIYI (a gangar jiki daya)
HorrorHakan ya furta cikin kasar zuci,amma ko cikin karfi irin ta tsatsuba Nainah ta saurari komi....... Gajeriyar murmushi tayi,daga karshe ta hade fuska......nanfa ta soma tunano abinda ya faru a wancen lokacin.....da kuma abinda yayi sanadin sumewar Ha...