SEASON_2 EPISODE 1

44 6 0
                                    

🧟‍♂️🧟‍♀️☠️☠️🧟‍♂️🧟‍♀️

    
        *RUHI BIYU*
  _[a gaangar jiki daya]_
                       *RETURNS*

                       🧟‍♀️🧟‍♂️☠️☠️🧟‍♀️ 🧟‍♂️      ‍

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
      _Kungiya d'aya tamkar da dubu._

        *_SPECIAL EDIT 2021/2022_*

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
+2349077974042

         *REPORTS*

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*😷😷STAY SAFE...  STAY AT HOME😷😷*

*FREE BOOK💯✅*
*📚LITTAFI NA BIYU*
*EPISODE_0️⃣1️⃣*


🆕
*30 MINUTES LATER*
*Shiru kakeji* a wannan guri....Babu abinda ke motsi illa iska dake kadawa sai kuma kukan kananun halluttu,irin su kwari da sauran su.

Wannan waje dai tayi tsit,kamar ba'a nan bane suka gwabza wannan gagarumar fada..
boka bakin bawa da sauran mutanen sa duk sun bace cikin kankanin lokaci.

Haka lokaci ta cigaba da tafiya babu bayyanar boka ballantana sauran mutanen.

➡➡Bangaren Nainah kuwa taku take cikin kasala inda wani santalelen saurayin aljani ke rike da kafadar ta...
Kaita gidansu dake cikin bishiyar kuka,yayi inda wata tsohuwa take kula da lafiyarta.

Kwana tayi a gurin bata cikin hayyacin ta,sai daa rana tsaka ta dawo barki.
A wannan lokacin ko ta rikide ta dawo *safras*
Dukda hakan ko ba abun mamaki bane ga *al-jannu* amma yan wannan kabila kuwa, sukayi ta mamakin yadda take rikede ta dawo wani janshi cikin awanni shabiyu.

Hakan kuwa suka yini suna jiran ya farka amma kuma har rana ta fadi bai farka daga wannan baccin ba.

Haka 6:00Pm tayi ya sake rikidewa ya dawo Nainah,abinda ya sake sakasu cikin mamaki kenan akaro na biyu....
Zaman jiran farkawar ta sukayi har dare ta raba,suka watse suka kyaleta kwance.

Haka zalika bangaren *Bil-adama* wannan lokaci dai ta kasance tsakar rana🌄ce.
Mu'azz ya kasance shima yana cikin yanayin da Safras yakasance ciki danko shima kwana daya da yini guda bai farfado ba,daga sumar da yayi.

Dukda wannan yanayi daya kasance ciki *Faruq* da wannan *Boka* basu kyalesa ba,saida suka saka masa hankwa suka daura jikin gadon dayake kwance a Kai.

Haka Raihana da Harun sukayi ta dakon dowowar safras hade da kuma fatan farkawar wanta mu'azz domin ko suna da tambayoyi masu dimbin yawa da zasu so ya ansa musu.

Amma kuwa ko daya babu wanda ta faru danko ba zuwa safras din yayi ba kuma ba farfadowa mu'azz shima yayi ba,har shudiwar kwanaki hudu da d'auriya.

*Zaiyi wuya d'an adam yayi kwanaki bakwai babu ci babu sha ya kuma rayu,amma idan Allah yaso hakan ta faru babu wanda zai iyya hanawa*

Safras cikin kwana na biyun ya farka inda kuwa ya tsinci kansa cikin wannan kabilar...
Mu'azz kuwa sati biyu tsor yayi yana wannan yanayi harma mutane suka fara radi radin cewa ya mutu.

10:00mp na dare cikin filin kwallo,wasu gayu ne ke aikin dare.....rike suke da manyan ledodi suna tsintar shara a wannan waje.

Bayan sun gama tare komi sukayi wajen zubar da ita sharan,nanfa daya daga cikinsu tayi arba da gangar jikin safras a kwance cikin wannan guri.

Buga ihu tayi inda dukkan ninsu suka razana,nan da nan suka fara tambayan ta meke faruwa...

Nuna musu tayi da yatsa inda suko suka tarar babu komi a gurin.....
Nan da nan suka gudanar da aikin daya kaisu gurin suka juya,ahanyar su ta komawa ko daya daga cikin su yaga jini na bulbulowa a kafadar wannan abokiyar aikin su data buga ihu alamar taji rauni.

Nanko yayi saurin sanar da'ita suka wuce clinic su biyu bayan sunyi sallama da sauran abokan aikin nasu.

Tarar da gurin babu kowa illa wasu likitoci biyu da suke aiki a gurin,nan da nan suka nuna musu raunin inda likitocin sukayi masa list na kayan aiki da ake bukata gashi kuma sundin basu dashi a wannan lokaci.

Shiko yace dasu,
"a ina ne zan sami wayen nan abubuwan"
sukayi masa kwatance ya fice ya kelesu ciki.

Takawa yayi izuwa wajen wannan dataji rauni yace da ita...

"Zaki jirani anan guri,zan sayo masu magunguna anan kusa"

"Mai zai hana muje tare"?
Haka yarinyar ta tambaye sa....

Shiko yace da ita....

"Idan kinyi tafiya rauni zai dad'a,zubar da jini kuma ba'a bukatan hakan dan haka kawai ki zauna ki huta ni zanji da komi".....

Bayan tajiyo hakan ta saki fuska ta dubi hagun ta da kuma dama alamar tsoro sannan tace dashi

"Okay babu damuwa,saika dawo"

Fitarsa keda wuya,lantarkin gurin ta dauke nanfa zuciyarta ta soma bugun uku uku....
A hankali ta mike ta soma cewa..... *Da wanine a nan gurin* haka take taku a hankali tana ta dafe dafe hartaje ta bude wani daki wanda wannan dakinne *Mu'azz* ke kwance ciki......

Budewarta keda wuya saifa lantarkin gurin ya kawo,nan tayi arba da Mu'azz na kwance a wannan gado,ganin lantarki yadawo ne yasa tayi niyar fita.
Amma data juya tayi Ido hudu da madubin dake jikin kofar fita ko sai ta tarar da safras ya shigo dakin Yana taku,da ganin haka ta waiyawaya da niyar ta ganshi azahirance.

Amma kuwa sai ta tarar da mu'azz ne kwance gurin shi daya,haka ta sake Duba cikin madubin.

Nanko sai tayi arba da safras din na kokarin kwantawa a jikin mu'azz....
Danko shidin ruhi ne,haka ta ajeye hankali saidata ga safras ya dawo haske ya shige mu'azz.

Nanfa ta zura idanu alamar mamaki,cikin abinda bai wuci dakika guda ba saitayi mu'azz ya dafa kafadarta ta baya.....

Juyawar dazatayi kuwa sai taji an kirawo sunan ta.....
Ana cewa

"maiya kawoki nan gurin ne,friend" haka wanda yaje sayo maganin yace da ita...

Itako da ganin fuskarsa ta juyo da niyar duba mu'azz dake tsaye bayanta.
Abin mamakin ko shine gani tayi gurin komi normal babu abinda aka taba a gurin......
Alamar babu abindaya faru kenan,Kuma still mu'azz na kwance a kan gadon.

"zainab lafiya,ina ta tambayar ki kinyi shiru"

"Lafiya nake muje"

Nanfa suka fice suka bar dakin,mu'azz ko ya bisu da kallo hade da murmushi bayan sun fice daga dakin.

*NEXT EPISODE ON RUHI BIYU RETURN🧟‍♂️🧟‍♀️*

_*Bagaren Mu'azz*_
Mu'azz na zaune a saman silin a dakin safras kaikace *spiderman*
Inda wani dalibi ya shigo dakin sukayi ido hudu dashi awannan hali.

_*Bagaren Raihana*_
Cewa tayi "ni gaskiya bana ganema Mu'azz,duk yabi ya sauya,komi nashi daban dana mu'azz din dana sani"

*Harun ko*
"Gaskiya akwai sarkakiya cikin rayuwar Nainah da safras ya kamata mu binciko labarin hakan a kan lokaci"
Buge kofa Ramlah tayi ta shigo dakin inda ta ce dasu
"Ni zan taimaka muku ku sami abinda kuke bukata"

*Boka baki bawa*
"Faruq Karka sake su Raihana su binciko wannan labari dan ko idan suka binciko wannan kashin mu ya bushe"

😲😲😲😲😲😲
*_Mu hadu a next Episode_*

RUHI BIYI (a gangar jiki daya)Where stories live. Discover now