🧟♂️🧟♀️🧟♂️🧟♀️
*RUHI BIYU*
_[a gaangar jiki daya]_🧟♀️🧟♂️🧟♀️ 🧟♂️
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
_Kungiya d'aya tamkar da dubu._*_SPECIAL EDIT 2021/2022_*
*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
+2349077974042*REPORTS*
*FREE BOOK💯✅*
*EPISODE_0️⃣6️⃣**In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*UPDATE*
*_APRIL_3ST_2020_**Ramlah* zaune take a falo.......tana kallon tashar *Starlife*
10:45Pm ita kadai,ke zaune cikin falon....nanfa sai taji an kwankwasa kofar daki....
Cikin sauri ta yunkura ta taka izuwa bakin kofar ta bude.....
Inda tayi arba da *Harun* a tsaye bakin kofar......"Au daman kaine?.......shigo daga ciki"
Nanfa suka shige dakin inda ta bashi abinci yaci yadan tayata fira kafin nan ya wuce dakin sa....
Hmm abin al'ajabi a nan gurin ko shine.....cikin university Nainah ce ke zaune...gefenta kuma Harun ne ke kwance....
Alamar a sume yake......😲😲😲😲😲
Toh abin mamaki idan har yanzu *Harun* yana cikin makarantar toh waye wannan wanda yaje gidan a suffarsa?
😲😲😲😲😲Cikin kasala *Harun* ya bude idanu inda yayi ido hudu da *Nainah* zaune gefensa....
Abinda ya soma fitowa daga bakinsa ko shine....."Nasan zamu ga juna......Nainah"
Cikin kasaita Nainah tace dashi.....
"taya kasan sunana?.....sannan waye kai"
Dajiyo haka yayi yunkurin cewa wani abu amma daga baya ya janye.....
Itako ta sake tambayarsa a karo nabiyu...."Baka cedani komi ba....taya kasan sunana"
"uhmmmmmmm Kawai naji tazomin ne"
Bayan ya furta hakanne ya soma waige waige.....alamar bai gane gun da yake ba.
Da ganin yadda yake ta jujjuyawar yasa ta tace dashi...."Dan saurayi.....karka zurfafa tunani,nasan kana mamakin ganin kanka dakayi a nan gurin......
Bari na sanar dakai abinda ya faru....na tarar da kai kwance ko nace asume bakin hanya shine na dan taimaka maka"Da jiyo hakan fa *Harun* ya tuno da wannan farar abin daya diro masa a gaba....
Cikin sauri ya yunkura...inda *Nainah* tace dashi......."Kayi a hankali.....Kuma tunda ka farka ni zan wuce"
Da jiyo haka sai ya juyo ya tambayeta cewar...
"Shin baki tarar da wata...wacce take sanye da farar kaya a gurin ba....?"
"A'a babu wanda na gani....amma lahiya kuwa? Mayya saka ka tambaya?"
Haka ta bashi ansa shiko ya sake da cewa...."Sanye fa take da farar kaya,gashin kanta kuma har kugunta ya tsaya....."
"Nidai babu wanda na tarar a gurin"
Dajiyo haka ya dafa goshi hade kuma dayin wani batu kasar zuci....."Shin ko mafarki nake ne ne ne?".....
Hakan ya furta cikin kasar zuci,amma ko cikin karfi irin ta tsatsuba Nainah ta saurari komi.......
Gajeriyar murmushi tayi,daga karshe ta hade fuska......nanfa ta soma tunano abinda ya faru a wancen lokacin.....da kuma abinda yayi sanadin sumewar Harun.
YOU ARE READING
RUHI BIYI (a gangar jiki daya)
TerrorHakan ya furta cikin kasar zuci,amma ko cikin karfi irin ta tsatsuba Nainah ta saurari komi....... Gajeriyar murmushi tayi,daga karshe ta hade fuska......nanfa ta soma tunano abinda ya faru a wancen lokacin.....da kuma abinda yayi sanadin sumewar Ha...