SEASON_2 EPISODE_2

52 3 0
                                    

🧟‍♂️🧟‍♀️☠️☠️🧟‍♂️🧟‍♀️

    
        *RUHI BIYU*
  _[a gaangar jiki daya]_
                       *RETURNS*

                       🧟‍♀️🧟‍♂️☠️☠️🧟‍♀️ 🧟‍♂️      ‍

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
      _Kungiya d'aya tamkar da dubu._

        *_SPECIAL EDIT 2021/2022_*

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*Phone no:*
+2349077974042

         *REPORTS*

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*📣📣📣SANARWA SANARWA📣📣📣*
_Ga masu Bin littafin Kofar aljali littafi na biyu Ina Mai Baku hakuri game da rashin posting da kuka ga ba'ayi gaskiya abubuwa ne sukayi yawwa..._
_dan hakan Ina Mai Mika sakon ban hakuri ga fans inshallah bada jimawa ba zaku jini love you all_

*😷😷STAY SAFE...  STAY AT HOME😷😷*

*FREE BOOK💯✅*
*📚LITTAFI NA BIYU*
*EPISODE_0️⃣2️⃣*

🔮
*Raihana ce* ke tafe hannun ta ko wasu manyan ledodi ne tariko,dalilin daya saka ta rike wayar datake magana ciki da kafada kenan.....

"Eh hakane nasani,nasan da hakan"

Hakan ta furta sa'annan kuma ta sake da cewa

"Yanzun haka shiga zanyi wajen *Yaya mu'azz* domin *yau* throughout Dad ne ya zauna tare dashi,shine na sayo masa abinci, domin shima ya samu ya huta."

"Okay toh sai da safe,nagode"

Shiga clinic din tayi tana taku cikin sauri,nanfa taji kamar takun mutum ya wuce ta bayanta.
Saurin tayi wajen waigawa baya,amma ta tadda gurin babu kowa,nanfa tayi ajiyar zuci hade da duba lokaci kafinan ta cigaba da tafiyar ta har takaiga Dakin da Mu'azz ke kwance ciki.

Shigarta dakin ko wannan abun daya kifta ta bayan nata, ya bayyana wanda hattani mai baku labari bansan ko meye bane wannan.🙄Domin nima da kaina ban iyya gane wace hallutta bane wannan......

   *BANGAREN HARUN KUWA*

Zaune yake a gurin da suka saba haduwa da Nainah.....
daka ganin yadda yake zaunen kuwa kasan yana cikin kunci dankuwa yayi tagumi kai kace rashi yayi.
Zaunen yake sai yaji an dafa kafadar sa ta baya,dashike zaman jiran dawowan Nainah yake sai zuciyarta ta cike pal da farin ciki a tunaninsa itace ta dawo.

Cikin sauri ya waiga baya hade da furucin *nasan zaki dawo gare ni* amma kuwa bayan ya juya yaga akasin haka....
ido hudu yayi da abokin nan nasa.....da ganin hakako ya hade fuska sannan ya sake juyawa ya cigaba da tagumin da yake.
Ajiyar zuci abokin nasa yayi hade da cewa

"Gaskiya bazan hanaka bakin ciki ba *Harun* domin kai kasan kunar da kakeji tacikin ranka....."

Bayan ya furta hakan ya Zauna gefensa inda suke fuskantar juna sa'annan ya cigaba da zazzago labari kamar haka.

"Nasan kayi babban rashi arayuwar ka Harun, domin ka rasa both friend and girlfriend at thesame time,amma zama cikin kunci bazai magance komi ba Harun,yakamata kasan da haka"

Haka abokin nasa ya furta shiko Harun din ya share kwallar dake zubowa daga fuskar sa,sannan ya Daga Kai ya kalli cikin idanun abokin nasa yace dashi......

"Nakasance daya daga cikin wayenda sukayi sanadiyar rushewar rayuwar Nainah da kuma safras.....
inda ace ban bayyana a wancen gurin ba da bazasu sami damar kamasu ba.....
Amma domin yakareni ya sadaukar da tasa rayuwar"

RUHI BIYI (a gangar jiki daya)Where stories live. Discover now