👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻
Story and written
By Fatima Msr Ahfat
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
Page 14
____________ Murtuk'e fuska tayi yace "ba kece kikace kina son kwayun iskanci ba?"
Ai duk wacce ta iya mgn haka dole kuma ta iya shara, dan gidan ku d'auki tsinsiyan nan ko na Karya ki gida biyu mara hankali k'awai"
Ya tsina fuska tayi tare zunburu baki tace" Allah bazan iya shara nan ba ka tausaya min ka barni na huta, wlh wand'a nayi dazun ma sai k'aji yanda jikina yyi tsami, jikina duka ciwo yake min"
Da K'auye nake d'a yanzu Saude tanamin tausa wlh"
K'o zaka min tausan ne kona samu saukin jikina, ta fad'a tare da rike gugunta tace 'washhh Allah na gaji sosai, k'amar bacci² ma nakeji wlh"
Ka mgn yayi sai binta da kallo yake zuciyarsa banda ta fasa babu abinda take, haushi da bakin ciki duk ya cika shi,
Kallonshi tayi tace" tausan zaka minne naga sai wani bina da kallo kake ka k'amar sabon maye"
Murmushi mugunta yayi Yace "tausa k'awai kike so?"
Yace"Sosai zaka minne?" Wlh da kuwa taimaka min sosai k'aga ma sai na babban ce tausan K'auye d'ana birni wanne yafi dad'i"
Yace " okay"
Ai kuwa batayi auni ba taji Saukar b'ulala ajikinta, k'urma uban ihu tayi tace" tausa fa nace kamin bawai ka kashe niba"
Yace " No tausa zan miki sai ki tattance ko?"
Yaci gaba da zabga mata b'ulala,
Gani da gaske yake sai ya kasheta anan ba wanda ya sanine, zagaye parlor ta fara yi tana k'urma ihu wayyo Allah, taimako jama'a za'ayi kisan a gidan nan, taimako² b'acin rai ne ya k'ara kamashi yaci gaba da zabga mata b'ulalan, yana cewa ba tausa kike so ba?" Yau sai naga me kwace ki ai"
Cikin kuka tace" don Allah kayi hakuri tsubur baki ne, yasa ni cewar kamin tausa"
Be kulata ba yaci gaba da zabga mata b'ulalan suna zagaye parlor"
Momy da SONA ne suka k'araso cikin parlor da gudu, domin ihun da Fatu take ya karad'e gidan gaba d'aya"
Tsawa Momy ta d'aka mishi tace " baka da hankali ne Saif?" Ko kasheta zakayi?"
Cak ya tsaya
Yace "No Momy ki d'uba ko ina na parlor nan kiga yanda ta batashi, bama nan kad'ai ba har cikin bedroom bata bari ba sanda ta b'ata, gashi sai fad'amin wani banzan maganganu take"
Sai a lkcn ne Momy ta lura da inda parlor ya koma duk a hargitse K'ota ina"
Fatu d'ake boye b'ayan SONA tanà shenshekan kuka tace "Karya yake Momy d'aga k'awai nace masa yamin tausa, shine fa mai makon naji tausa sai naji saukar b'ulali ajikina"
dariya SONA tayi tace" haba bro's d'aga tausa sai ka tausas'a mata jiki da duka"
Kusan dry abin yaba Momy tace" Ashe duk abunda ya miki ke kika wayowa kanki"
Turu baki gaba tayi batace komai ba"
Kallon Saif Momy tayi tace " last warning ka sake dukar yarinyar nan sai ranka ya b'aci"
tana fad'ar haka ta fice d'aga parlor ta barsu tsaye"
dariyar ta SONA ta had'eye ganin Yaya nata yanda ya murtuk'e fuska, jan Fatu tayi sukabi b'ayan Momy, kafin su fita sanda ta masa Gwalo tare da burgud'a masa baki"
Ta kaici da b'acen rai, da bakin ciki ne ya k'amashi, ji yake k'amar ya mutu,
ficewa yyi d'aga parlor direct parking space ya wuce shigewa Motan sa yayi yabar gidan"
*******************A parlor suka tsami Momy zaune saman kujera, kara sawa sukayi suka zauna, kallo Fatu Momy tayi tace" yata na nimi wani Alfarma a wajen ki zakimin?"
Sunkuyar da k'anta tayi tace" ki fad'i kome zan miki ba sai kin nemi wata Alfarma ba"
Murmushi tayi tace" ina son ki fita d'aga harkan my son, idan ya saki wani abu ki masa idan kuma ya tsaki abunda bazaki iya ba ki fad'amin"
Kuma d'aga yau karki sake ce babba yayi k'arya kinji ko?"Fatu tace " insha Allah Momy zanyi duk abunda kika ce"
Murmushi jin dad'i tayi tace" ki shirya d'aga gobe zaki ringa tafiya islamiya SONA, kafin ki shiga school, ina son ki mai da hankali sosai kinji diyata"
Murmushi tayi tace" insha Allah ngd sosai Allah ya kara girma, Amen ta amsa dashi tace " toh idan kun huta SONA kuje da ita ku gyara masa part dinsan, tunda baya son mai aiki suna shigar masa part"
Okay Momy SONA ta amsa mata dashi, mikewa tayi ta haura sama"
Kallon Fatu SONA tayi sai kuma ta fashe da dariya tace" gaskiya Yaya ya iya tattausa jiki fa"
Shugub'e Fuska tayi k'amar zatayi kuka tace" Allah bana son mgn d'ake"
Ohhh! Sorry dear tashi mu tafi mu gyra barnan da kikayi, mikewa tayi suna tafiya tana k'ukbure²"Direct gidan su Hafiz ya wuce, hon yayi a bakin get, lekawa me gad'i yayi ganin Motan Saif ne ya sashi bud'ewa da sauri ya shigo, parking yayi ya fito suka gaisa da Baba me gad'i, ya wuce part din Hafiz, a bakin parlor yay knocking, bai jira amsa ba ya shigo ciki, b'akin shi dauke da sallama, ciki² iya lips dinshi ya tsaya, idan ba kunnen maciji ne da kai ba bazaka jiba"
Hafiz dake zaune saman kujera ya d'aura kafa d'aya kan d'aya yana lasar wayar sa, d'ago da idanunshi yayi ya kallesa tare da tsakin murmushi yace "wata sabon gani, yau kai kaine agidan namu?"
Banza yayi dashi bai ce masa komai ba,ya zauna a'kan kujera"
Murmushi yayi tare da mikewa ya d'auko mishi drink da ruwa me sanyi da cup ya ajiye masa a gaban, daukan goran ruwan yyi ya kafa a bakin shi sanda ya kusa shan rabi kafin ya sauke yana sauke ajiyar zuciya"
Murmushi Hafiz yayi yace " ya akayi a minina yau kuma waya bata maka rai ne haka?"
Numfashi ya tsauke yace " wlh yarinyar nan sai na k'arai rayata, zannu na mata ita din k'aramar mara kunya ce"
Dariya Hafiz yayi yace " wace yarinya ce ta b'ata ma rai yau kuma?"
Hmmm bari k'awai wata village girl ne ta ba....!Kuyi hakuri wlh nayi typing sai ya goge shiyasa kuka samu guntun page
07061204735
Msr Ahfat ✍️