👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻
Story and written
By Fatima Msr Ahfat
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
Page 16
_______________________ Lumshe idanunsa yayi lkcn da idanunsa suka masa arba da wata beautiful girl tanà tsakin murmushi, d'an ware idanunsa yay don tabbatar da a'bunda yake da gaske ne kodai gizoce idonsa ke masa"
Ya dauki 5 second yana kare mata kallo,
Ganin da gaske itan ne ba idanunsa bane, ya tsashi jan tsaki, d'aya sa Momy juyuwa tanà kallonsa tace " lafiya kake kuwa?"
Fuska a d'aure yace " ba komai, wucewa part dinsa yayi da mamaki a zuciyar sa na ganin yanda Fatu ta canja masa lkc daya tayi kyeu k'amar ba itaba, wani zuciyar yace masa yarinyar da ko kwaila ma bata kai ba kake wani tunani akanta,tsaki yaja a fili ya furta Allah tsare ni, yana isah ya bud'e part dinsa wani k'amshi ne ya bugi hancinsa, Lumshe idanunsa yayi tare da bud'esu yana bin ko ina da kallo murmushi k'awai yayi ya wuce bedroom dinsa, k'ayan jikinsa ya rage ya d'aura towel ya shige toilet, 30 minutes ya dauka a toilet din ya fito d'aure da towel, gaban dressing mirror ya tsaya gyara suman kansa yayi ya dauki body lotion dinsa ya shafa a jikinsa tare da feshe jikinsa da body spray sai k'amshi yake, wardrobe dinsa ya bud'e three Quarter da T_shirt ya fitar ya sanya a jikinsa wanda yay mugun amsar jikinsa bakin sajen fuskar san nan a kwance' sai shek'i yake, k'ara feshe jikinsa da turarunruka yay, wayar sa ya dauko number SONA ya kira tanà dagawa yace" had'amin abinci ki kawo min, yana faɗ'an haka ya kashe kiran bejira cewar tab'a"
SONA dake kitchen tanà aiki da Momy"
Kallonta Momy tayi tace "had'a masa komai ki b'a Fatu ta kai masa, domin taji duk abunda ya fad'a k'asan cewar wayar a speak tasa"
Had'a masa komai tayi cikin tiren ta mikawa Fatu d'ake tsaye tanà jiranta zuciyar ta sai uku ²yake,tunawa da dukan da ya mata dazun, karb'a tayi ta fice d'aga kitchen din jiki ba k'wari ta nufi part dinsa"
************ Bangaren Ruky kuwa tanà fita direct gidan su Sumy ta wuce, tanà isa me gad'i ya bud'e mata get ta shiga, parking tay ta tanà fita d'aga Motar cikin gidan ta shige kai tsaye, sallama tay a parlor Sumy d'ake zaune ita kadai ta amsa mata tare da mikiwa da sauri suka rungume junan su suna dariya, Sumy tace " gaskiya nayi missing dinki sosai, murmushi Ruky tayi tace " Nima nayi missing dinku sosai, ina Ammi ko bata nan ne?"
Sumy tace" ba wani wlh yaushe rabon da muyi k'oda call ne, Ammi dai bata nan taje gidan Yaya lameer"
Lameer kuma yayi Aure ne?"
Eh Yayi bakin ki Auren saba ba, ta fada tanà hararan ta batare d'ata sani ba"
Kauda zancen tayi da cewa " yanzu dai mubar wanan zancen, nazone ki taimakamin ina cikin damuwa sosai,tabe baki Sumy tayi tace " wanan wacce irin damuwar ce haka?"
Wlh k'awata na kamu dason wani handsome guy ne, amma shi da alama K'ota² k'amar bai damu dani ba, nikuma gaskiya ina matukar sonshi ba kad'an ba, ina cikin wani halin wlh"
Murmushi mugunta Sumy tayi tace " indai wanan ne karki tsawa kanki damuwa" k'amar yaya karna damu?" B'ayan na fad'a miki shidin ba sona yake ba"
Ai wanan abu mai sauki ne indai kin shirya kina da money toh da kafar sa zaizo ya tsameki har inda kike"
A shirye nake wlh ko me zanyi indai abunda nakeso zan sameshi"
Toh kwantar da hankalin ki Yar uwa akoi wajen wani Bokan da zan kaiki a miki aiki, wlh aikinsa t'amkar yankan wuka ne"
Dan Ya tsina fuska Ruky tayi tace " nifa gaskiya kinsan ban cika son irin wadan nan abubuwan ba, amma idan bukata ta zai biya wannan ba komai bane zan iyayi"
Sumy tace " insha Allah zakiji dad'in aikinsa, kinga ma bari na dauki handbags dina sai muwuce, kafin Ammi ta dawo"okay" mikiwa tayi ta wuce bedroom dinta ta shiga tanà murmushin mugunta, handbags dinta ta dauka da wayoyinta ta sauko"
Mikewa Ruky tayi suka ficewa d'aga parlor tana bata lbrn Bokan, jin yanda take yabon sani ya sata jin karfin guiwa, shigewa Motar ta sukayi suka fice d'aga gidan suka dauki hanyar zuwa wajen Boka"A hankali ta tura kofar parlor tashiga da sallama,
Yana zaune saman kujera yana aiki cikin laptop dinsa, d'ago da kansa yayi da niyar amsa sallamar sukayi ido biyu da Fatu da itama shi take kallo,
Tsaki yayi ya kauda kansa, ya amsa sallamar a dak'ile, yana ya musa fuska k'amar wanda yaga kashi"
Binshi da kallo take tana mamakin yanda yake ta wani ya musa fuska k'amar kashi yaga ajikinta, tabe baki tayi cikin borin rashin kunya tace " toh idan ka gama yasine ²naka sai ka fad'amin inda zan ajiye maka abincin" Asaman kaina zaki ajiye"
A fusace tace " nifa banson rainin hankalin kan nan ka fad'amin inda zan ajiyema,
Baice mata komai ba yaci gaba da abunda yake, harara ta wasa mishi tare da k'arasawa inda yake zaune ta ajiye tiren a saman table din dake kusa dashi" ta juya da niyar zata fice d'aga parlor, a hankali taji cool voice dinsa yana cewa " waye baki izinin fita ne"
Cak ta tsaya tare da juyuwa tace " ba sai an bani izinin fita ba, kafin na fita"
Fuska d'aure yace " uban wa zai bani abincin"
Yanda yayi mgnr sanda ta tsorata,
Batace komai ta dawo inda yake domin yadan bata tsoro, ganin yanda ya murtuk'e fuska kar ya tsake mata duka k'amar na dazun"
A hankali tace "Toh me zan maka?"
A tsayen zan fad'a miki abunda zakiyi, baki gaba ta turu tare da dan rintsina wa,
Murmushi yay wanda bai wuce saman lips dinsa bane yay idan mutun bai kola sosai ba bazai ce yayi ba,yace " had'amin abincin"
Ahade yake ta bashi amsa,
Okay dauko min ruwa a fridge, mikewa tayi ta dauko mishi ta ajiye masa a gaban sa, ta dawo gefinsa ta zauna tana kallonsa, ture laptop din gefe yayi ya fara cin abincin, bai maci sosai ba ya tura plate din gefi, ruwan ya dauka, yace " da idonki zansha ruwan?"
Mikewa tyi ta dauko masa cup dake zaune saman fridge din ta kawo masa, karba yay yazuba ruwan yasha, yace " dauko min drink wanda bai da sanyi sosai ba"
Tana k'unkuni taje ta dauko masa"
Cup din dake ahanunsa ya mika mata yace " bud'e ki zubamin"
Wani irin bakin cikine ya rufe ta, k'amar ta falle mishi mari haka takeji, cike da b'acin rai ta bud'e marfin goran da karfi, ai kuwa bata zubewa drink din yayi ajikinta har da shima sanda ya zube masa ajiki, saurin mikewa yayi don kar ya bata mishi jiki, Fatu kuwa a tsorace ta kuma baya,ai kuwa taka drink din d'aya zube tayi, baya tayi luuuu! Har zata fad'i kenan taji anyi saurin k......Share fisabilliah Habibaty 🥰