👧🏻 MIJIN YARINYA 👧🏻
Story and written
By Fatima Msr Ahfat
ELEGANT ONLINE WRITERs 📚
Bismillahir rahmanin Rahim
Page 18
_____________ Idanunsa suka sauka k'an Fatu d'ake zaune saman kujera tama TV k'uri da ido sai murmushi takeyi, Narkakkun idanunsa ya zuba mata, yana binta da wani irin kallo, kallonta yake bako k'iftawa, cikin ransa kuwa yace" wow so beautiful, k'aramar yarinya ce amma komai tay yana burgesa, lips dinta da take dan motsawa yabi da kallo, murmushi yay yace " magana disu sai rashin kunya"
Idanunsa ya maida Saman k'anta yabi sumar kanta da kallo wanda ke kwance lup dashi"
Lips dinsa ya ciza yace " hmmm k'yawunta na banza tunda nidai ba sonta nake ba, tsaki yaja yace " ina ma abun son anan"
Da wanan tunanin da yake a ransa ya sauko parlor, dining area ya nufa yana taku a hankali ² har ya karaso ya zauna, savings din kansa yay ya tsoma ci"
Fatu ma najin k'amshin turaren sa ta lumshe idanunta a ranta tace " gaskiya wanan turaren ba dai k'amshi, daina kallon TV tay ta bishi da kallo k'amar maiya har ya karasa dinning din ya zauna"
Murmushi tay haka k'awai ta tsinti kanta dason zuwa ta takura masa,
Cikinta ta dan shafa tace " yunwa ma nakeji wlh dole naci abinci idan ba hakaba akoi matsala"
Mikewa tyi a hankali, kallonta SONA tayi tace" ina kuma zuwa?"
Fuska shugub'e tace " nadan fara jin yunwa ne zanci abinci"
SONA tace " ko dai kice bin mijinki zakiyi ba"
Murgud'a mata baki tay tace" Allah tsareni, ina ma mijin yake?" Ai wanan baza'a kirashi d'ana miji ba, domin na miji baya tab'a daga hannunsa ya doki mace"
Murmushi SONA tayi tace" sorry hakane fa dear jekici abincin ki, nidai nasan wataran duk abunda ake boyewa zai fito fili, taci gaba da kallonta"
Tabe baki tayi tace " ohoo dai ai sai kiyi tayi, don ni yunwa nakeji masu bacci da ido d'aya kawai, tayi shigewar ta abunta"
Duk abunda ta fada duk ya shiga kunnen Saif, murmushi k'awai yay amma kuma har cikin ransa Kalmar data furta ya dukesa"
K'araso wa tayi ta zauna kan kujera tanà kallonsa, ganin yanda ta zuba masa idone ya sashi daga da kansa sukayi ido biyu da ita, zare masa ido tayi tana murmushi, tsaki yaja ya dauke kansa yace "wlh idan na tsake k'amaki kina kallona sai na k'wakule meki idanunki"
Lah da gaske Yaya?" da kuwa wlh nayi dad'i k'aga kuwa zaka zamomin dan jagora ko"
Naga kuma ai kai ka fara kallona har muka had'a ido,ni bance zan kwakule maka ido ba sai kai"
nifa jiran ka nake ka zubamin abinci naci yunwa nakeji"
Wani kallo ya watsa mata, har zaiyi mgn sai kuma ya fasa, aransa yace " wato wanan yarinyar duk abunda ka fada mata sai ta baka amsar sa"
tsaki yaja yaci gaba dacin abincin sa hankali kwace yama manta da wata zaune a wajen"
Ganin ya mata banza ne ya tsata dibar abincin ta faraci tana ya tsina fuska"
Ko kallon inda take bai tsake yiba har ya gama cin abincin sa ya mike yabar wajen, rai ba dad'i domin mgnr data fada masa"*Bayan sati daya*
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya inda Fatu ta fara zuwa islamiya ita da SONA ba laifi kuma tanà dan gane karatun sbd idan suka dawo SONA na kwaya mata duk abunda bata ganeba" rashin kunya kuma ba abunda ya ragu ko d'aya sai tsulawa Saif tsiya take son ranta, duk da yanzu ya daina kulata sosai domin mgnr data fada masa ranan"
**************Bangaren Ruky kuwa bayan kwana uku suka koma wajen Boka, inda ya bata wasu magungunan kusan k'ala bakwai na wanka dana hayaki, na kwana uku, idan ta gama kuma akoi wani turaren daya bata akan ta shafashi, kuma ta tabbatar idan ta shafashi Saif ya shaki k'amshin, idan tay haka dai shikenan aikin ta ya biya, karb'a tayi tana zuba godiya suka bar wajen, tana komawa gida ta jika magungunan ta fara amfani dashi"
Kwance take saman bed dinta tana tunanin gobe ne maganin ta zai cika, amma ta yaya zata samu ta hadu da Saif gobe dun cika aikin Boka"
Murmushi tay tace " dolene nasan abunda zanyi nan da gobe,
Wayar tane yay ringin, kallon wayar tayi Iman yake kira answering tayi tace " Hello" daga can bangaren Iman yace " haba sweetheart tunda kikazo Nigeria kika manta dani ko call na miki baki dagawa why Baby"
Murmushi tayi tace" am sorry Baby wlh ina busy ne shiyasa amma don Allah kayi hakuri"
a ranta kuwa cewa take idan har na samu Saif a hannuna ma ai bazaka tsake jin k'oda murya taba"
Okay ba laifi amma gaskiya nayi missing dinki sosai"
Murmushi tay tace" nima nayi missing dinka sosai, murmushi yay sukaci gaba da hiran su cikin farin ciki"
********** Yau su Fatu basu dawo islamiya da woriba har karfe 6:30 domin sun biya gidan Hajiya Zainab sun bata sakon da Momy ta aikesu, suna dawowa, bedroom ta shiga, tanà shiga toilet ta fada tayi wanka ta fito domin yanzu dai Fatu ta fara zamuwa yar gayu sbd SONA tyi tsayin d'aka sosai kafin yanzu ta dage dayi" shiryawa tayi cikin kayan bacci wando da riga red color yay matukar amsar jikinta sai k'amshi takeyi, parlor ta sauko direct dining ta wuce taci abinci, kitchen ta shiga ta wanke duk abunda ta bata ta fito, bedroom dinsu ta wuce tanà shiga ta sami SONA na kwance, kallonta tay tace " meke damunki na ganki a kwance ko wanka bakiyi ba?"
K'asa mgn tayi sai murgususun da takeyi tana nunama Fatu cikinta, a rikice Fatu ta k'araso bed din tana mata sannu riketa tayi tanà mata sannu ganin ba abunda zata iya mata ne ya tsata fashewa da kuka tace " don Allah SONA ki tashi karki mutu ki barni, da sauri ta kwantar da ita tayi saurin fitowa don kiran Momy"duk ta rikice sai kuka take ,domin ba abunda yafi rikita ta kamar taga wuni nata bashi da lafiya"
Fitowa tay cikin sauri tanà kiran Momy! Momy!! Momy!!! Karo sukayi da Saif dake kokarin haurowa, kamata yay ganin yanda tabi ta rikice sai kwalla takeyi, jikinsa ta fad'a tare da zakin kuka me cin rai, shima cikin rikicewa ya dago ta daga jikinsa yace........Share fisabilliah Habibaty 🥰