*MIJIN YARINYA*
*By Fatima Mrs Ahfat*
*Elegant online write's*
*Bismillahir rahmanin Rahim*
Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I'm
selling MTN data with this cheap price**MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month**Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*Page 31
_____________Asalin mahaifin saif da Fatu yan uwane na jini, mahaifin Saif shine babban wato Alhaji Aminu mahaifin Fatu shine mai binsa Malam Ibrahim su uku mahaifinsu suka haifa akwai Mace ke bin mahaifin Fatu amma Allah yyi mata rasuwa saka makon brea's cancer data fama dashi ba tare da tasan hakan ba har yaci karfin ta koda sukaje asibiti ba irin faman da bayi ba amma shine Ajalinta sosai mutuwar tata ta shigesu ba yanda suka iya sai dai su bita da addu'a
Mahaifin Saif Babban dan kasuwane" yana da company nayin gidaje na gida dana waye"yana daya daga cikin masu kudi a garin kano duk da kasan cewarsa ba dan cikin garin bane" itama mahaifiyar sa haifanfiyar garin Kano ce Hajiya AISHA, Saif shine dansu na farko sai kanwarsa SONA sosai suka basu ingantanciyar ilimin a'ddini dana Boko,... ah America Saif yyi karatun sa, a school suka hadu ta Ruky tun da ta kwolla idanunta a kansa taji duk duniya ba wanda take so inba shiba, duk da cewa shidin ba kulata yake ba domin ya kasance miskiline ajin farko shi idan mutun bai san shiba zai aza wulakanci ne dashi amma ba haka bane tun taso warshi haka yake, sosai Ruky take cusa kanta a wajen shi don ya sota but ganin bai da niyar hakanne ta fitoh fili ta fada masa ita fa Sonsa take domin bata da wani sukuni a ko yaushe Sonsa da sha'awar sa kawai ke addabar ta" saif bai buye mata ba ya fada mata shifa ba soyayya bace ta kawosa dun haka taba zuciyar ta hakuri ta manta dashi amma taki...sai ma kara shige mishi da take fuskarta sa da tayi yana da mugun feeling ne ya sata take kara shenshege masa da yawan zuwa kusa dashi, da haka har ya kammala digree amma bai dawoba sbd wani aikin da yake.Mahaifiyar Fatu haifanfiyar kauyen WANGARA ce Malama maryam sun hadu da Malam Ibrahim ne a cikin kauyen ne lokacin da yake dawowa daga kasuwancin sa ganin ta na farko yaji ta kwanta masa a rai zuwa yyi ya fada mata bata wani ja ajiba ta aminci domin yaba tarbiyan su da ake da haka suka fara soyayya har Allah ya nufa ta zama Matarsa, sun dad'e a basu samu haihuwa har abun ya fara damun Maryam ta kasa hakura tawa mijinta mgn akan ya kara Aure wata kila itace bata haihuwa yace mata karta damu Allah ne mai bada haihuwa ba shiba, hakadai tayi ta hakura bayan wasu shekaru Allah ya bata ciki cikin yazo mata da abubuwa da dama tayi rashin lafiya sosai daga baya ta warke da haka taci gaba da rainon cikinta cikin kwanciyar hankali har watan haihuwar ta ya tsaya yau ko gobe gashi mijinta baya nan sbd kasuwancin da yake yana tafiye ² ne, sai su Inna dasu mata hidimo mi kala ² sunanan zaune da Inna suna hira aka kirata a waya ganin number mijinta ne ya sata sakin murmushi tare da amsawa, abunda aka fadane ya sa hankali ta tashi nan take taji cikinta na wani irin murdawa, dafe cikin tayi tana innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n!!" Sosai hankali Inna tashi ta mike tana cewa meke faruwa maryam?", ta fada tare da daukar wayar tasa a kunnenta tana sawa taji ance Allah ya masa rasuwa sakamakon hatsari da sukayi a hanyar su ta dawowa' kasa motsi tayi sai Innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n! da take mai maitawa har wani irin hajijiya take gani, karan da maryam ta sake ne ya dawo da ita tunanin da take ganin jini na bin kafarta ne cikin tashin hankali da baza a mitsilta shiba ta kira ma komta suka kai maryam daki domin haihuwace ta tasu mata, tunda suka shiga da ita daki suke fama da ita domin sumewa take Sosai yar karbar haihuwa suka tsorata jikinsu yyi sanyi domin wahalar da take ciki sunsha fama sosai da ita kafin ta haihu amma ko ganin yar tata batayi Allah ya karbi ranta, sosai tashin hankali ya samu iyalan gidan da rasuwar Mata da miji a lokaci d'aya ranan Inna kamar mutu, kiran Daddy sukayi suka fada masa abunda ya faru , shima a hankalin ba k'aramin tashi yyi a ranan ya tahu ta Matar sa da yarsa SONA domin lokacin Saif baya kasar, bayan an musu suturu aka kaisu gidansu na gaskiya. bayan dawowar ne ya dauki al'kawari koda bayan ransa Fatu Matar saif ce domin tunawa da yyi da dan uwansa daya ce masa idan har Allah ya sauki Matata lafiya ta haifi ya Mace toh Matar Saif ce yariga da yamai zabi" haka dai rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin kunci da jimamin mutuwar dan uwansa wanda yafi so, kulawa sosai Fatu take samu a wajen su bayan kwana 40 Daddy yace "zai dauki Fatu ya riketa a gunsa, Inna tace" ah ah Fatu a wajenta zata zauna har sai lokacin da zata kai Aure hakan zai rage mata radad'in da takeji na rashin kowa a kusa da ita" ba yanda ya iya haka ya hakura suka dawo garin Kano sbd karatun SONA duk da tana kusa da matakin karshe" sosai Daddy yake zuwa yana dubasu da ma Fatu sayanya kala_kala" Fatu farace sol gata kwakawace ajin farko amma akoi ta da rashin masifa da rashin kunya da tsiwa bata barin ta kwana duk da tana da tsayi sosai amma akoi ta da karancin shekarun Saude ce Babban kawarta domin tasu tazo daya da iya makirci da rashin kunya domin ko da Inna ta shigar da ita karatun Arabic fasawa Malama kai tayi aka sallamuta, ta dawo Inna ta fara karan tar da ita amma abun baya tafiya kota_ kota domin bata zama daga safe ta fita sai Inna tabi kworaro ² tana neman ta ko koma in yunwa ta korota" zuwan Daddy da yayi yaga ta kata girma sosai ne ya sashi Yana komawa ya fadawa Hajiya akan yaka mata yanzu dai ya cika alkawarin daya dauka na Aura wa Saif Fatu, domin girmar da yaga tayi duk da cewa hankali bai zauna ba amma yasan da ta dawo nan dai komai zai zama normal" murmushi kawai Momy tayi tace " Haka shine dai_dai Allah ya bamu ikon riketa da Amana, gashi kuma Baba bayan ya zaayi kenan? " Murmushi yyi yace " munyi mgn dashi yacemin ya gama aikin da yake gara ya dawo ayi komai gashi company na bukatar sa" okay Allah ya zaba mana mafi alkairi" da Amin Daddy ya amsa suka haura sama"...
Wanan kenan
*Cigaban labari*
~~~~~~~~ Saif kuwa tunda ya isah ya fara aikin daya kai sa, zuciyar sa cike da kewar Fatu duk da wani bangaren na zuciyar sa yana jin dad'in rabuwa da Ruky domin yasan test din daya mata ko ita ce mara zuciya a dunita a yanzu ta hakura dashi.
Bangaren Fatu kuwa sosai ta zage da yin karatu gashi SONA na kwaya mata wasu abubuwan zamani daga girki, kwalliya, maganar zamani da iya takudai kala_kala duk da kasan zuciyar ta na kewar Yaya n nata sosai...gashi tana ji zai kira SONA suyi hira amma bazai tambayeta ba har ya kashe, wanan abun na kona mata rai sosai har kuka takeyi a boye, wato saboda ita ce baya so shiyasa ko tambatarta baya yi, tasha kuka harta gaji gashi.
A kwana a tashi an ce Asaran mai rai yanzu haka a school dinsu ita ce take zuwa na daya domin kokarin ta, a bangaren islamiya ma ba a magana, Fatu dai a yanzu ta goge tayi kyau ta zama Big girl me ji da kanta don har da turanci ta iya" domin ba karamin kokari Momy da SONA sukayi wajen canja mata rayuwa, kayan yaki take shiga na yar ubansu daka ganta bazaka dauka ita bace, yau ma kamar kullun tasha wanka cikin wando jeans blue da t_shirt orange color ta daure ta wani d'aure suman kanta a gefe ta dan zuwa wani ta gefe ta dauki wani dankwali ta zagaye shi dashi, fuskarta data sha make Up sai Kelli take, murmushi tayi lokacin data kalli kanta a madubi ita kanta tasan ta yi kyau ba kad'an ba, mikewa tayi ta fita sai baza k'amshi take, parlor ta sauka SONA na ganinta ta mike tana cewa" wow sister kinyi kyau sosai" murmushi tayi tace " thank u my lovely sister" picture SONA ta mata sosai tayi kyau, domin yau dai tason yin tsokana ganin Yaya Saif na online ne ya sata tura masa pic din sai ta sauka a online din tana murmushi."Saif daya dawo daga aiki duk yabi ya gaji, domin bai taba tunanin zai dad'e haka ba sai gashi sun rikesa amma yana tunanin ko nan da 4 day idan ya gama abunda yake zai dawo domin sosai zuciyar sa ke kewar Fatu kwana kinan ma har mafarkin ta yake, wanka yyi yaci abinci ya kwanta tare da hawa online yana duba wasu abubuwan ne yaga SONA ta turu masa da pic da kamar bazai budewa sai kawai ya bude ai bai san lokacin daya mike zaune yana k'urawa pic din ido tare da zuko shi, hannunsa ya kai idanunsa ya gogesu don ya tabbatar mafarkin daya saba ne ko da gaske, ganin da gaske ba mafarki bane ya sashi mikewa yana k'urawa pic din ido yace.......!
Mrs Ahfat ce ✍️