*MIJIN YARINYA*
*By Fatima Mrs Ahfat*
And
*Asmeety**Elegant online write's*
*Bismillahir rahmanin Rahim*
Ta fado jikinsa Numfashin ta ya tsaya cak.
cikin tashin hankali ya ɗuka yana fidda kwalla yana jijjiga ta yana kiran sunan ta amma ba numfashi a tattare da ita.Ruky na ganin haka ta fara yunkurin guduwa security wajen suka zagaye ta, nan take aka kira yan sanda suka fita da ita,
Saif kuwa daukar Fatu yyi da wasu security din suka bar Mall din, diving yake cikin tashi hankali har Allah ya kaisu asibitin,
suna isah aka shiga da ita emergency room bata taimakon gaggawa ganin jinin da take zubarwa,Zama Saif yayi ya dafe kansa sbd sarawar da yake masa har wani jiri_jiri ke dibarsa,ya dauki 5 second a haka kafin ya zaro wayarsa ya fara kiran layin Momy bugu biyu ta dauka, tace "hello son" shiru yyi baice komai ba sai lumshe jajayen idanunsa da yyi, jin shirun yyi yawa ne yasa Momy cewa" lafiya kuwa kana jina kayi shiru?" bude jajayen idanunsa yyi a hankali ya fada mata abunda ya faru, cikin tashin hankali Momy tace " gamunan zuwa, tana fad'ar haka ta kashe wayar"
kallonta SONA dake zaune tayi tace" lafiya Momy?" Girgiza kai Momy tay tace " watace ta tsukawa Fatu wuka yanzu haka suna asibiti" tana fad'ar haka ta haura sama tana kiran layin Daddy" innalillahi wa inna ilaihi rajiu'n!, SONA ta fada cikin tashi hankali itama ta wuce bedroom ta dauki hijab dinta ta fitoh ta samu Momy harta fitoh, fita sukayi suka shiga Mota mai gad'i ya bude musu get suka fita da gudu,suna fita direct asibitin suka wuce, suna isah SONA tay parking k'asan cewa itace tai driving dinsu, Suna fita da sauri suka wuce ward din da suke, suna zuwa suka samu har daddy ya k'araso suna jiran fitowar dr. Cikin tashin hankali Momy tace" har yanzu basu fitoh ba" ta fada tanà kallon dan nata cike da tausayawa" da eh Daddy ya bata amsa, zama sukayi suna jiran fitoh warsu, sun dauki 5 minutes zaune sai babban Dr ya fara fitowa sai Fatu da aka fitar daga emergency kwance take idanunta a rufe suka wuce da ita ɗakin hutu
saurin mikewa dukan su sukayi da sauri Saif yabi bayan su suka shige room din a tare
kallon Daddy Dr yyi yace"ku kwantar da hankalin ku ba wata masalar fatar ta k'awai wukar ya taba ba komai nan da anjuma insha Allah muna sa ran zata farka"
ajiyar zuciya suka sauke Daddy ya masa godiya suka wuce office dinsa tare k'asan cewar Dr abokin Daddy ne, suna daga tsaye wata Nurse ta fito tana kallon Momy tace"Hajiya zaku iya shiga wajan ta yanzu"
Murmushi Momy tayi tace"Eh Bara Mijin nata ya fito tukun nan"
"Ok" tace kafin tayi wucewar taSaif suna shiga bayan Likitocin sun fice daga ɗakin yaja kujera daƙe gyafen gadon ya zauna yana kamo hannun ta
Kissing ɗin hannun yayi yana kallon Kyakkyawar fuskarta Murmushi yayi yana shafan gyafen fuskar tata kafin a Hankali ya motsa Lips ɗin sa yace"I'm so sorry Baby, Ni na jayo Miki , ɗuk a sanadiya ta hakan ta faru kiyafewa Mijin ki kinji?"Yana faɗa yana kwantar da kansa bisa gyafen hannun ta
Kamar daga sama yajiyo Muryar Fatu tana faɗin"Yaya Zafi"
Ɗagowa yayi da sauri yana kallon ta gani yayi idanun ta lumshe suƙe
Hannu yasa yana shafan fuskarta cikin jin tausayin ta yace"Sorry Baby da Zafi ko wajan ?"Lumsassun idanun ta ta ware tana kallon sa ta turo baki cikin shagwaɓa tace"Eh da Zafi"
Murmushi yayi yace"Sorry zai warke zuwa gobe kinji kiyi hakuri"
Tana kallon sa tace"Yaya babu abinɗa ya same ka ko?"
"Eh babu komai"yace yana shafan hannun taMurmushi ta sakar masa tana lumshe idonta
Su Momy ne da Sona suka turo kofar suka shiga
Saif na ganin su ya miƙe tsaye
Momy zama tayi kan kujerar da Saif ya tashi cikin tausayin Fatu tace"Sannu Daughter yaya jikin naki kike ji yanzu?"
"Da sauki " tace tana kallon Sona daƙe tsaye tana kallon ta ciƙe da tausayin ta
"Allah ya kara sauki"cewar Momy tana shafa kan FatuSona ma yaya ji tayi mata
Daddy ne suka shigo da Dr nan ya dubi jikin Fatu gaya Alhmdllhi da sauki yace wa su Daddy "sai gobe da safe idan Allah yakaimu zamu sallame ku "
Saif badan yaso ba ganin su Daddy yasa yaki yin Magana dan shi babu abinɗa yafi tsana kamar wai kwana a HospitalDa Daddare
Daddy ne ya kalli Momy yace"Hajiya zaku wuce gida sai Shi Son ya Zauna anan ko?"
"A a Alhaji suyi ta fiyar su Ni zan zauna da ita zuwa goben"
Kallon Saif Daddy yayi yace"Son to muyuce kadda dare yayi mana"
Saif Yana tsosa kyaya yace"To Daddy"
Murmushi Daddy yayi sarai ya ganewa dan nasa baya Son Zuwa gida
Kallon Momy yayi yace"Hajiya taso mu wuce kai Son Zauna da Matar ka"
Momy zatayi Magana Daddy yayi Mata nuni da ido ta kalli Saif
Momy na ganin sa tayi Murmushi tace"To mu tafi"
Saida safe sukayi musu kafin suka fice daga ɗakinSuna fita Saif ya rufe kofar dakin harɗa sa masa key kafin ya nufi kan gadon inɗa Fatu daƙe kwance tana kallon sa
Zama yayi bakin gadon yana kallon ta yace"Baby Muje kiyi wanka ko?"
Tana turo baki tace"Nidai sai gobe"
Bai kulata ba ya gyara mata kwanciya ya shige Toilet daƙe cikin ɗakin
Bai ɗau lokaci mai sawu ba ya fito
Wajan gadon ya nufa yana zuwa ya kwanta gyafen ta yaja ta zuwa jikinsa ya rufe su da Blanket
"Ashhhhhhh ciwo na Yaya "
Kallon ta Saif yayi cikin tausaya mata ya shafi wajan ciwon yana hura mata iska a kunnen ta cikin wani irrin salo yace"Zai warke kinji Sorry"
Lumshe idon ta tayi tana kara shigewa jikinsa
Shima lumshe idonsa yayi nan taƙe bacci yayi Wuff dasuSu Momy suna zuwa gida Mai gadi yace musu sunyi bakuwa
Aikam yayi musu kwatancen matan nan taƙe Momy tasa salati
Sona tana kallon Momy tace"Aiko Inna ta karitso.......More Comment
More Comment
Share Fisabidillah