I am so happy da comments din ku on the last chapter! Nagode 💕~~BABI NA ASHIRIN DA BIYU~~
Iyalan Baffa sun cigaba da rayuwa kaman da. Ba kaman da gaba daya ba amma sun kamanta. Babban tashin hankalinta shine Baffa. Mahaifinta na cikin damuwa ba kadan ba, duk ya rame ya yi baki. Hannunta a daure ya ke dan ba ta da abunda zata taimake da shi. Sai dai ta dage da yi mai addu'a.
Ta cigaba da sana'ar kitsonta kaman da. Su Sadiya ma sai cigaba su ke samu wurin kasuwancin su. Har yanzu bata san mai za ta yi da kudin da Hamma Ashmaan ya bata ba. Ta dai adana su a banki har sai ta yanke shawara.
Sakamakon jarabawar JAMB ya fito. Result ya yi kyau sosai, ta samu maki dari biyu da ashirin, Mimi kuma ta samu maki dari biyu da sha biyar. Baffa ya ji dadin haka sosai. Wata mai zuwa za su rubutu jarabawar Post UTME. Jarabawa ce da makarantan da ta zaba za su yi amfani da wurin tantance kwas din da za su bata.
Hamma ya turo mata text a waya ya na mata murnar cin jarabawa. Tunda ya tafi wannan ne karo na farko da magana ta shiga tsakanin su.
Duk sanda ta tuna ranan da zai tafi sai taji wani irin ciwo ya mamayeta. Ko kadan radadin rabuwa da shi bai yi sauki a wurinta ba dukda dama chan ba wai suna tare ba ne. Ummi ta zauna ta mata nasiha mai ratsa jiki, daga karshe ta ce zata samu wanda ya fi Ashmaan.
Ita ta cire rai da samun soyayya a duniya, wata kila rabonta a lahira ya ke. Tana sha bayan abunda ya faru da Fa'iz, ba zata kara tsintan kanta a wannan mawuyacin halin ba. Sai gashi na yanzu ya linka waccan naisa ba kusa ba.
Da rana komai lafiya sai cikin dare ta yi kuka kaman ranta zai fita. Shi wannan ciwon ba wanda za ka sha wa magani bane ya tafi lokaci daya. A'a, ya na nan cikin jikin ka, ya na bin jininka babu ta yanda za ka warkar da shi.
Ta maida hankalinta kan sana'arta da karatunta. Su kadai ne abubuwan da zata iya controlling.
Babban tashin hankalinta shi ne Baffa. Duk wani aboki na Ardo da ke raye sai da ya je ya same shi ko ya na da masaniya akan asalin shi. Kullum da amsa daya ya ke dawowa. Amsar da ke sa hasken idanunsa raguwa.
Abun da mamaki ace Ardo bai fadawa kowa ba. Ko me ye dalilinsa? Duk da Inna ta ce har ya mutu bai daina kokarin nemo 'yan uwan Baffa na jini ba.
Ita kam da Baffa zai hakura da ya fi. Da ciwo ganin shi ya na karaya haka kullum. Abu kusan shekara sittin nemo shi wuya, musamman da ba'a san ta inda za'a fara ba. Sai dai ta san mahaifinta ba zai taba hakura ba. Babban abunda za ta iya mai shi ne taya shi da addu'a.
Kamar kullum yau ta tashi da wuri har ta gama aikace-aikacen gida. Gida daya kawai zata je kitso yau amma sai bayan sallan la'asar. Kannenta sun tafi makaranta, Baffa ya tafi aiki, daga ita sai Ummi a gidan.
Gidan na nan yanda suka same shi. Baffa ya ce zuwa jibi za'a zo a fara wiring din wutar lantarki kuma a sa ceiling. Ruwa ba matsala bane tunda akwai rijiya. Bangaren bayan dama shi ginin bai yi nisa ba dan ko rufi ba'a mai ba. A cikin wurin aka buga langa-langa suke girki ciki.
Ta na cikin shara ta jiyo sallama kaman muryoyin kawayenta. Ajiye tsintsiyar ta yi ta fita. Habiba da Safara'u ne, ta same su suna gaida Ummi.
"Toh, ni na tafi." Ummi ta ce. Ta ce zaman gidan ya isheta ta fara koyarwa a wata islamiyan matan aure daga alhamis zuwa lahadi da yamma. Saura ranakun kuma ta na ma wasu mata karatu a gida.
YOU ARE READING
Rayuwar Maimoon.
RomanceRayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka. Me yasa suke g...