BABI NA DAYA

3.4K 354 83
                                    








~~BABI NA DAYA~~




Sanye take da doguwar hijabi kalar sararin samaniya har ƙasa, ƙafafuwan ta rufe da safa. Haka fuskan ta ba'a ganin komai sai manyan fareren idanuwanta da suka sha kwalli saboda baƙin niqabin da take sanye dashi.

Sauri take ta isa gida dan gab ake da kiran sallan Maghrib, bata ankara ba kawai taga lokaci ya ja, bata son kuma Baffa ko Ummi su mata faɗa.

Daidai an fara kiran sallah a masallacin kusa da gidan su ta isa. Da sauri ta tura kofar wani makeken get, ta samu Baba maigadi yana arwala, nan ta gaishe shi cike da girmamawa.

"Ahh ahh, ƴar gidan Baffa an dawo?"

"Eh Baba," Ta amsa tana murmurshi.

"To sannu da zuwa. Ni bari in tafi masallaci."

Da to ta amsa mai sanna ta cigaba da tafiya.

Katafaren gida ne babba na alfarma wanda aka cika shi da kayan alatu na zamani. Ginin gidan da ya kasance gidan sama a tsakiya yake sai fili da ya zagaye shi. Ko ina shimfiɗe yake da ciyawa dake kwance luf saboda kulawan da ake bata na mussamman, da kuma shukoki da suka sake ƙayatar da gidan.

Hanyar da akayi dan wucewar motoci da mutane ne kadai babu ciyawa, shimfiɗe yake shi da interlocks. Daga chan gefe kuma gareji ne da motoci biyar anyi parking dinsu.

Ta bayan gidan akwai gini biyu matsakaita da gidan lambu da aka ƙayatar sosai domin shaƙatawa. Ɗaya ɓangaren babban yaron gidan ne, ɗayan kuma BQ ne.

BQ ɗin ta shiga, a zagaye yake da ɗakuna biyu kowanne da bayi a ciki, sai kitchen da ɗan ƙaramin tsakar gida. Babu kowa a tsakar gidan da ta shiga, kowa ya tafi yin sallah kenan. Niqabin ta cire, sannan ta cire hijab ɗin.

Maimunatu Muhammad, wanda aka fi sani da Maimoon, budurwace mai shekaru ashirin da biyu a duniya. Doguwace sosai, baƙa, baƙin ta mai kyau ne domin kuwa fatar ta har sheƙi take yi. Baƙin ta ya fi kama da na mutanen Somalia, da ka ganta kasan bafullatana ce saidai kallar fatar ta da ta fita daban. Tanada diri mai kyau da ɗaukan hankali.

Allah Ya albarkace ta da idanu masu haske kaman nono da girman gaske, sun kuma yalwatunna da zara zaran gashin ido, Tana da gira mai duhu da cika kaman an zana shi a fuskanta, sai dan siririn hanci da ɗan ƙaramin baki.

Ɗakin dake chan gefe ta shiga, ɗakin ba babba bane chan ɗan matsakaici ne dan ba za'a kira shi ƙarami ba. Babu gado a ɗakin sai katifu uku girman ƴan makaranta dake jingine a bango, sai kuma wardrobe, ƙasan kuma shimfiɗe yake da ledar ɗaki da ta rufe sumintin.

Bayi ta shiga tayi arwala, ta fito ta tarda ƙannen ta biyu, Amina da Sadiya suna sallah. Itama ta kabbara tata Sallan. Bayan ta idar, tayi adhkar, sannan tayi nafila raka'a biyu.

"Sannu da zuwa Adda, ina wuni," Amina ta gaishe ta cike da fara'a bayan dukkan su sun idar da sallah.

"Lafiya qlau Mimi," Ta amsa ita ma tana murmushi.

"Adda mai kika kawo mun?" Sadiya ta tambaya tana ƙokarin janyo jakar da yayarta ta dawo dashi.

Da sauri ta dauke jakar sannan ta buge mata hannu. "Ke fa tsiya ta da ke kenan, da mutum ya dawo sai ki dinga mai bincike kamar kin aike shi, to ban dawo da komai ba. Kin bani kudin?"

Rayuwar Maimoon.Where stories live. Discover now