~~BABI NA GOMA SHA UKU~~Rabon da tayi dariya haka har ta manta, cikinta har wani daurewa yayi ga hawaye na zuba daga idanunta saboda tsabar dariya. Duk yanda taso dannewa ta kasa saida akayi da ita.
"Ammah yanzu har ɗaki kuka bita?" Ahlaam ta tambaya murya na rawa saboda dariya.
"Har ƙasan gadon tsohuwarta kuwa. Har mu za'awa sharrin satar gyada? Gyada fa! Daga ranan aka kiyaye mu a garin nan."
Kai Maimoon da girgiza na sake gimtse dariyarta. Ta ɗaɗe bata haɗu da mutum mai ban dariya kaman Ammah. Tunda tazo gidan kawai taji tsohuwar tayi mata. Gata da faran-faran da son mutane. Sai taji ina ma ace haka suke mu'amala da Inna.
Kaman yanda Adda Salma tace mata, washegari tazo ta dauke da safe wurin sha ɗaya. A hanya Adda Salma ke fada mata dangantakar su da Ammah. Ashe ba dangantakar jini bace kaman yanda tayi zato. Mijin Adda Salma, Habib ne abokin jikan Amma, wato Sayf. Tun suna yare suke tare har izuwa yanzu.
Abun ya ba Maimoon matuƙar mamaki. Ashe dama akwai mutanen da suke daraja abokantaka haka? Wasu kam ƴan uwantaka na jini ma sun kasa riƙewa balle aje wani abuta. Ko dayake da yawa sunfi ba abokai mahimmanci akan ƴan uwansu.
Sun isa wani katafaren gida da ya so tsorata Maimoon. Gidane babba na alfarma, gidan da ya amsa sunan shi gida. Idanu kawai ta zuba tana kallo ikon Allah. Irin gidajen da ake ce ma aljannar duniya. Abunda ya fi burgeta shine inda ko ina yake kore da bishiyoyi da fulawowi.
Ba cikin main building din suka shiga ba. Wani sashe ne daban dake gefe sai dai shi ba gidan sama ne ba kaman wancan.
Wata matashiya suke iske a kofan shiga inda ta sanar dasu Ammah na ciki. Sun same ta zaune cikin falonta da ya ƙayatu da kayan alatu na zamani, tana zaune kan kujera tana kallon tashar Sunnah TV. Tana ganin su murmushi ya bayyana a fuskarta, suka gaisa sosai cikin sakin fuska. Daga gani akwai shaƙuwa sosai tsakanin ta da su Adda Salma, dan su Amira suna shigowa suka haye ta.
Yanda ta tarbi Adda Salma, haka ta tarbi Maimoon. Abun ya bata mamaki kwarai. Ammah doguwace sosai duk da dai ta dan tankware saboda shekaru, jikinta a mulmule yake, sai sheki yake yi kaman ba na tsohuwa ba.
Tunda suka zauna in banda sasu dariya babu abunda Ammah keyi. Bayan an gama gaisawa, Maimoon ta fara mata kitso. Kaman sauran jikinta, shima a gyare yake tsatsap dashi. Daga gani ana ji da wannan tsohuwa.
Basu ɗaɗe ta fara kitson ba wata matshiya da bazata wuce sa'ar Maimoon din ba ta shigo. Doguwace itama, tana ɗan haske kaɗan. Sunanta Ahlaam kaman yanda taji Ammah ta kirata. Kaman yanda Ammah take da sakin fuska, itama haka take. Zama tayi aka dasa hirar da ita.
Ita dai Maimoon iyakarta murmushi, sai kuma in Ammah ta ce mata "ko ba haka ba Munari?" Sai tace mata, "haka ne Ammah."
A cikin hirar ne Ammah ta dauko labarin kuruciyar da inda take basu labarin wata yarinya da ta mush sharri ita a ƙawarta.
"Ammah ai ko mutuwa na jin kunyar idon mahaifiya." Inji Adda Salma.
"Hakane. Amma mu ranar kam bamu ji ba."
"Sai me ya faru?" Ahlaam ta tambayi kakarta.
Ammah zama ta dan gyara, haka ya sa Maimoon ta sakan mata kan da ta zauna da kyau. Bayan ta gyara zama Maimoon ta cigaba da yi mata kitso. Kitson hannu take mata duka baya kaman yanda ta buƙata.
DU LIEST GERADE
Rayuwar Maimoon.
RomantikRayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka. Me yasa suke g...