~~BABI NA BIYU~~Sunan ta da aka kira yasa ta tsayawa. Waye ke kiran ta haka? Dan sam bata ba samarin layin su fuskar da zasu tare ta a hanya ba, bama a layin nasu ƙadai ba, a ko ina. Bata tsaya ba, ta cigaba da tafiyar ta.
"Maimoon?"
Cak ta tsaya, dan taso ta gane muryan. Mamaki ya kamata ganin wanda kwakwata batay yi tsammanin ganin shi ba. Ko yaushe ya dawo ƙasar?
"Maimoon din ce kuwa, ga idanun nan."
Murmushi tayi amma shi ba zai ga hakan ba saboda niqabin ta. "Hamma Ashmaan?"
"Maida idanun kar su faɗo," yace cike da zolaya. "Nasan kina mamakin gani na, jiya da daddare na dawo."
"Sannu da zuwa. Ina wuni, ya hanya?"
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah, ina zaki haka?"
Cike da rashin gaskiya ta bashi amsa akan cewa Ummi ce ta aike ta.
"Muje to in raka ki."
Da sauri ta girgiza kai; "ba sai ka raka ni ba Hamma, ba yanzu zan dawo ba, aiken da yawa."
"Rowa ake mun ko?"
"Ni na isa, ba haka bane."
Murmurshi yayi, yana jinjina kai. "To shikenan, sai kin dawo. Anjima zan shigo muyi hira, nayi missing dinki sosai."
Dariya tayi, kunya na kamata.
Tsare da yayi da idanu. "Ke bakiyi missing ɗina ba kenan?"
Girgiza kai tayi. "Ni bance ba."
Murmushi yayi yana kaɗa kai. "Ƙar in tsaida ki, bye."
Sallama ta mai itama sannan ta juya ta cigaba da tafiya. Ashmaan bai motsa daga inda yake tsaye ba har saida ya bar ganin Maimoon. Murmushin da ke dauke da ma'anoni daban yayi kafin shima ya ƙarasa inda yake da niyan zuwa.
Ta na tafiya tana murmushi ita ƙadai. Duk cikin abokan wasan ta (cousins) sun fi shiri da shi sai ƙanwar shi Jasrah. Rabon da ta ganshi har ta manta, tunda ya tafi makaranta a America ƙaro karatu.
Alhaji Bello (Daddy) da Hajiya Suwaiba (Mommy) na da yara shida, maza biyu da mata huɗu. Ashmaan ne babba yanada shekaru ashirin da tara, sai Hasina da tayi aure da yarinya ɗaya, shekarun ta ashirin da shida, Fauziya mai shekaru ashirin da hudu, sai Radiya sa'ar Maimoon, sai Jashrah mai shekaru sha shida sannan ɗan auta Auwal da ake kira da Khalifa yana da shekara goma.
Dukkan su halin su ɗaya da iyayen su, har da Khalifa da bai wuci ka ƙaryashi da hannu ɗaya ba. Har ma sun so sufi iyayen nasu, Hausawa na cewa magaji mafiyi.
Hasina halin ta sak irin na mahaifiyar ta, koma fiye da nata. Duk cikin su tafi takura ma Maimoon, musamma bayan wani babban lamari da ya faru tsakanin su. Da yake itama Maimoon ɗin ba kanwar lasa bace, tana taka mata birki sosai.
Mommy na da son yara ba ƙadan ba, duk abun da suke so koda kuwa bai dace ba zata basu dan a wurin ta bataga amfanin dukiyar da uban su ya tara ba in har baza'a basu abunda suke so ba. Sun tashi kuma da ƙiyayyar ƴan uwan su kaman yanda ta koya masu tun suna ƙanana.
Ashmaan da Jasrah ne ƙadai suka fita daban a cikinsu. Mommy tayi faɗan tayi faɗan har ta gaji. Har cewa take Rabi'atu ta asirance mata yara.
Maimoon ba ta dawo daga inda taje ba sai wurin ƙarfe uku. Nan ma ba gida ta nufa ba, gidan su Habiba—babbar aminiyarta— ta wuce dan akwai abu mai mahimmanci da ya kamata su tattauna akai.
ESTÁS LEYENDO
Rayuwar Maimoon.
RomanceRayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka. Me yasa suke g...