~
BABI NA TALATIN DA SHIDA
~Gaba daya dakin ya dauki ni'imtaccen kamshi. Dawowarta kenan daga tasha inda ta amso kayayyakin hada turare da aka aiko mata daga Maiduguri. Hajiya Laila ta hada ta da mutumin bayan ta gama aji a wurinta, kayan shi ingantattu ne da kuma saukin kudi.
Wuri guda ta ware ma kayan a cikin wardrobe dinta. So ta ke yi ta gama ayyukan cikin gida sannan ta fara aikin. Aikin turare ba karamin abu ba ne, ya na da cin lokaci sosai.
Duk da kasuwar yanzu ma sai a hankali. Amma ta san kasuwanci ya gaji haka. Akwai wasu sababbin turare da ta ke so ta gwada hadawa dan jin ya kamshin su zai kasance. Ta na so kuma ta hada kullacham ta jarraba ta gani ko zai amsu wurin mutane.
Tunda aka yi hutu ba ta saida turare ko daya ba. Rabonta da saida turare ma tun kafin ta kwanta rashin lafiya. Hakan kuma ya na damunta sosai.
Ta san harda laifinta, dan tsakani da Allah bata tallata hajarta yanda ya kamata. Amma kuma harda rashin sanin kan (social media).
Ita kadai ce cikin gidan. Sadiya na makaranta, Mimi ta na wurin Jaddati. Ummi kuma ta raka Baffa asibiti check up. Tun dawowar su nan aka hada shi da kwararren likiti, yanzu haka ya daura shi kan magunguna da treatments na wani lokaci. Ya na lura da yanda jikin Baffan ke karban maganin, idan komai ya tafi dai-dai ba sai an yi mai aiki ba.
Su dai addu'ar su komai ya tafi yanda ya kamata.
An share gidan an goge, an kuma kunna turaren wuta ya bade ko'ina. Da ya ke akwai masu aikin da ke zuwa yin shara kullum safe da rana. Ma'aikata ne na musamman wanda sun dade suna aiki a gidajen gaba daya.
Sai dai ma'aikatan iyakar su kasa, sama su ke gyarawa. Ta gama gyara dakin Baffa dama shi kadai ne abunda ya rage mata. Store da ke cikin kitchen ta nufa ta fito da kayan aikin turarenta. Su tukunya, robobi, abun juyawa da sauran su. Ba ta ga camping gas din da ta ke aikin da shi ba, saboda haka ta kira Mimi a waya.
Ba'ayi minti biyu ba sai gata. Cikin store ta shiga ta fito da wani kwali sau ga gas din a ciki. "Adda ina za ki yi aikin?"
"Inaga kawai gwara in yi a waje." Akwai yar farfajiya bayan kitchen din da ya ke a zagaye.
"Toh," Mimi ta dauki kayan ta fara fitar mata da su waje. "Kin san da an baro miki kayan nan a Kaduna."
"Gwara da kuka taho mun da su, dan ko kudin su ban gama maidawa ba. Ku wai ya maganan kayan makulacen, kun watsar ko."
"Ba haka bane. Ba mu samu lokaci mun zauna ba ne. Ni ina chan, ita tana nan. Amma in sha Allahu kafin in koma makaranta zamu san yanda za'ayi. Kinga kuma bamu gama sanin kan garin ba. Ni inaga ma kawai zamu rika siyo kayan aikin daga Kaduna sai a sa mana a mota dan garin nan kaman za'a kwace maka kudi a hannu wallahi."
Maimoon ta yi dariya. Da gaskiyarta wannan. Tana son ta hada turare hudu yau ko sama da haka a yau. Mai saukin ciki ta fara da shi, shine na jikawa, duk ciki ya fi sauki.
Katon drum irin wanda ake sa ruwa ta dauko. Da farko ta zuba kilishin sandal dinta a ciki, sai ta dauko ruwan turare ta zuba, sai garin misik, ambur da jawi da aka daka. Sannan turare na mai (oil perfume) da madaran turare.
Duk sanda ta zuba abu sai ta juya. Bayan ta gama ta rufe shi gam saboda shi turare ana so ya kasance a rufe ko yaushe. Kuma yawan dadewan turare a aje, yawan kamshin shi saboda kayan hadin sun jiku sosai.
YOU ARE READING
Rayuwar Maimoon.
RomanceRayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka. Me yasa suke g...