Dazu ina cikin typing hannuna ya danna publish button din, ina lura na maza na cire sai dai har notification din ya tafi🙈😹 Na san na sa muku rai (inata ganin comment chapter 28 baya budewa🤣) shi yasa na dage na gama typing, ko editing banyi ba. So enjoy 🎉~
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
~Zafi a ke yi na fitan hankali, gashi an tara su a cikin lab sun fi su dari.
"Wai su malaman nan in sun san baza su zo ba ai sai su fada tun wuri. Yanzu ba abun ka fita ba ya zo." Rukayya ta ce ta na tsaki.
Dariya Maimoon ta yi ta cigaba da danna waya. Kiran sunanta aka yi ta dago, wata abokiyar karatunta ce. "Akwai Khumra da Kajiji?"
Ciro su ta yi daga cikin jaka ta mika mata, a nan ta ke ta yi mata transfer. Godiya ta mata.
"Nima fa Khumra na ya kusan karewa." Inji Rukayya.
"Sai ki zo ki siya wani ai kafin su kare."
Lecturer dai bai zo ba sai ana saura minti talatin lokacin shi ya kare. Sai da ya yi awa biyu da ya kamata ya yi tun farko. Awannin su hudu kenan a zaune. Kafarta har zugi ta ke yi, ga bayanta da ya rike.
Da kyar ta isa daki, wata irin yunwa ta ke ji na fitan hankali. Ta yi rashin sa'a babu kowa a dakin kuma babu sauran abinci da ta bari da safe. Daya daga cikin su ta dawo dan ga plate nan. Indomie ta maza ta daura ko neman albasa da attarugu ba ta yi ba, haka ta dafata ita kadai.
Ta na gama ci ta hau gado, a nan barci ya dauketa. Cikin barci ta jiyo karan buga kofa. Tsaki ta yi ta tashi ta bude, bata ma ga waye ba ta juya.
"Sorry," Anwara ta ce. "Na manta key dina."
Duk yanda ta so komawa barci ya gagareta, ta dai yi kwance ta rumtsa ido. Ta na ji Anwara na hidimar daura tukunya, a gajiye ta ke da ta taya ta.
Adda Salma ta kirata, shi ya ida farkar da ita. Sun yi hira sosai. Hutun da taje ma ba su hadu ba saboda ta yi tafiya.
"Yauwa Maimoon muna da maganar da zamu yi ma."
"Magana akan me Adda?"
"Ba zata yiyu a waya ba, sai mun hadu."
"Toh shikenan, Allah Ya kaimu. A gaida su Ikram."
Ganin kwanciyar ba zai amfane ta ba, ta mike ta hau gyaran daki. Da yake yau kowa tun safe ya fita ko ina kacha kacha. Anwara ta tattara tarkacen da ke tsakiyar dakin, shara kawai ta yi ta goge dakin.
Dakin su na burgeta, su kadai babu wata kazamta. In ta je dakin su Rukayya har Allah Allah ta ke yi ta fito dan ita kam bata yi sa'a 'yan daki ba, gasu su takwas ne a dakin. Tulin kaya ba'a magana.
"Moon sauko mu ci abinci."
Tsam ta tsaya jin sunan da Anwara ta kirata da shi. Da sauri ta girgiza kai dan kar ta fada tunanin da baida amfani.
"Haka na ji Sadiya na ce miki, Adda Moon. Kin san kuwa idanunki na resembling moon din."
Dariya ta yi. Spoon ta dauko ta zauna su ka fara cin shinkafar da Anwara ta dafa.
DU LIEST GERADE
Rayuwar Maimoon.
RomantikRayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka. Me yasa suke g...