BABI NA HUDU

1.4K 281 35
                                    









~~BABI NA HUDU~~






Yau Maimoon ta tashi bata jin daɗin jikan ta, zazzabi na nema ya rufe ta. Tsaki ta dunga yi dan ta san period dinta ne yake kan hanya. A daddafe tayi aikin gidan. Ummi tayi tayi ta bari amma taƙi. Daga ita sai Ummi a gidan, Baffa yayi tafiya tun shekaran jiya amma In Allah ya yarda yau zai dawo. Sadiya da Mimi kuma na makaranta. Haka dai ta samu ta gama komai, kafin la'asar zazzabi ya rufe ta.

A ɗaki ta kwanta, taƙi taje ta faɗa ma Ummi. Sai da su Mimi suka dawo wurin ƙarfe hudu su ka ganta a kwance tana juye juye.

"Adda lafiya?" Sadiya ta tambaya, hankalinta a tashe. Maimoon ko magana bata iyayi saboda azaba.

"Mimi, kira Ummi da sauri." Da gudu Mimi ta fita, ba'a ɗaɗe ba sai gata ta dawo da Ummi. Sadiya har ta fara hawaye, ganin Addan su a halin nan kullum tada mata hankali ya ke yi.

Ummi ma duk ta ruɗe. "Kin cika taurin kai, tun ɗazu baki da lafiya amma baza ki faɗa ba. Kin san yanda abun nan yake miki amma baza ki tanada magani ba. Mai yasa kike haka Maimunatu?"

Ita dai azaba ta hana ta magana, haka take fama ko wani wata. Duk lokacin watan ta haka za tai ta fama da ciwon mara, ciwon baya, ciwon kai, zazzabi da sauran su, wani lokacin harda su suma.

"Sadiya je ki haɗa mata ruwan wanka, Mimi duba cikin jaka ki dauka kudi ki siyo mata magani."

Ko waccen su da sauri ta tafi yin abunda maihifiyar su tasa su, ita kuma Ummi ta gyara wa Maimoon kwanciya, ta daura kan ta a cinyar ta tana shafawa a hankali.

"Ummi na haɗa," Da taimakon Sadiya, Ummi ta kai ta banɗaki. "Ki tabbata kin gasa jikin ki sosai."

Ita dai bata san yanda akayi tayi wanka ba har ta fito lafiyar ta ƙalau bata fadi ƙasa ba, dan harta cinyoyinta ciwo suke, har wani karkarwa suke yi. Ummi ce ta taimaka mata ta shirya, sannan ta kawo mata abinici. Ɗan kaɗan taci abincin dan kwatakwata bata sha'awar ci, dan ma Ummi ta tsare ta.

Duk a takure take, kunya ta lullbe ta. Da dai sun barta ta ji da kanta, wannan ba sabon abu bane amma ko yaushe sai sun tada hankalin su, yaci ace sun saba yanzu ai.

"Tashi ki sha magani." Maimoon kaman tayi kuka, ta tsani haɗiyan magani, gwara a mata allura. Haka dai ta daure ta sha, a hankali bacci ya dauke ta.

Ummi kusan gadin ta tayi, duk sanda Maimoon ke ciwon nan hankalin ta tashi yake. Sunje asibiti, likitan tace ba komai bane, kashi araba'in cikin ɗari ana samun mata da menstral cramps din su ke tsanani.

Da ta tashi ta ɗan samu sauki, tasan ita da dawowa dai-dai sai nan da ƴan kwanaki. Gashi tasan Ummi bazata barta tafita ba. Dole ta kira Habiba ta faɗa mata abunda ake ciki.

"Wayyo, Allah ƙara sauki. Zan kira in faɗa dalilin rashin zuwan ki."

"Yawwa Habiba, nagode."

"Bakomai, Allah ƙara sauki, sai nazo dubiya."

"Ke dallah ba ciwo nake yi ba, kaji fa, wai dubiya. Sai kace wata mara lafiya."

"Lafiyar ki ƙalau yanzu?" Maimoon shiru tayi, bata ba ta amsa ba. Ƴar hira suka ɗan taɓa sannan suka ma juna sallama.

Tana zaune taji muryan Ummi ta na sallama, hannun ta dauke da tray. Murmushi Maimoon tayi tana kallon mahaifiyar ta har ta zauna. "Sannu Maimu, ya jikin?"

Ita abun ma kunya yake bata, ba dama ace lokaci yayi sai kowa ya sani, har Baffa da.... Wani zugi taji zuciyar ta ta fara, da sauri ta kawar da tunani.

Rayuwar Maimoon.Where stories live. Discover now