BABI NA HAMSIN DA DAYA

995 163 45
                                    







Thank you for coming this far🥹❤️









~
BABI NA HAMSIN DA DAYA
~





Rike take da kanta tana murza shi saboda wani irin sarawa da ya yi. Ƙara kara wayar ta yi a kunnenta. "Yanzu yaya a ke ciki? Har ta iso?"

Sam Maimoon ba ta ji dadin zancen ba da Ummi ke fada mata Inna zata zo.

"Ba ta dade da isowa ba," Mimi ta amsa mata ta dayan bangaren. "A bangaren Jaddati za a sauke ta."

"To," ta ce tare sa sakin ajiyar zuciya. "Keep me updated. Baffa fa?"

"Yanzu ya fita daga falon zai isa chan."

Kai ta gyada daga nan su ka yi sallama. Cillar da wayar ta yi kan gado. Ba ta lura da Sayf ya shigo ba sai da ya yi magana.

"Lafiya Noor?" Ya tambaya yana isa gabanta inda ta ke zaune a bakin gado.

Daga kai ta yi ta kalle shi. "Inna ta iso."

Kai ya jinjina. Tunda ta ji labarin Inna zata zo ta daga hankalin ta. "Anjima da dare sai mu je ko?"

"Ba yau ba gaskiya sai gobe," ta ce tana zumbura baki.

Bai ce komai ba ya sa hannu ya mikar da ita sannan ya ja ta gaban madubi. Itama kuma tana bin shi kaman rakumi da akala. A gaban madubin ya tsayar da su ita a gaba shi a baya. Ya rankwafo ya daura habar shi a kan kafadar ta ta dama, ta cikin madubin su ka hada ido.

"Raihanatul Qalb," ya kira a hankali yana sumbatar gefen wuyan ta. Hakan ya sa ta runtse ido. Sai da ya bari ta bude kafin ya cigaba da cewa. "Ina son kin manta duk wasu kalamai da Inna ta taba fada miki, ki goge su sannan ki saurare ni da kyau. You. Are. So.Beautiful."

Juyo da ita ya yi suna fuskanta juna, idon shi cikin nata. "Kin taba fita da dare garin ya yi duhu amma hasken wata na haskawa? That's exactly how I see you Mahnoor, like the glow of moon light on a dark night."

Murmushi ta yi idanunta cike taf da kwalla. Sayf ya girgiza kai ya na share mata hawayen kafin ma su sauko. "I fell in love with your eyes. Fa tabarakallahu ahsanal khaliqeen. Mahnoor idanunki na rikita ni."

Daya bayan daya ya sumbaci idanunta sannan ya hade bakunan su wuri daya. Sayfullah ya tabbatar Maimoon ta haddace duk abunda ya fada mata.

***

Sam babu dokin da ta saba ji idan zata gida, kaman ta yi zamanta a fasa fitan ta ke ji. Wato ba zaka san yanda wani ya cutar da kai ba sai kana bada labari, a lokacin ne zaka gane tsananin  yadda aka cutar da kai.

Tana cikin mota Sayf ya rufe gidan. Bai ce mata komai ba da ya shigo mata sai riko hannunta da ya yi. A haka su isa Asokoro. Gidan Ummi su ka nufa Maimoon ta bar Sayf a falon kasa ta haura sama.

Ummi na zaune a dakin ta Maimoon din ta iso. Da murmushi Ummin ta tarbe ta. Ita ko Maimoon ta kura mata ido tana son ta ga ko akwai alamun damuwa tattare da mahaifiyar ta.

Ummi da ta gane kallon na me ye ta yi dariya. "Ni daina mun kallon kurilla. Ina Sayfullah din, mu je in gaisa da shi."

"Ummi...."

Rayuwar Maimoon.Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin