BABI NA GOMA

1.2K 228 23
                                    







~~ BABI NA GOMA~~




Sauri take ta kammala abunda takeyi saboda yau gidajen da zata je kitso da yawa. Tana gama shiryawa, suka karya tare da Mimi da Sadiya. Farar doya ce suka soya, sai kunun tsamiya. Tare suka zauna suka ci abinci, bayan sun gama su ka ma Ummi sallama, Baffa yau da wuri ya fita.

"A dawo lafiya, Allah ya kiyaye, Allah ya bada sa'a." Cike da farin ciki ko waccen su ta amsa da Ameen.

"Adda Moon yanzu ina zaki?" Sadiya ta tambayi Maimoon inda suke tsaye a bakin titi suna jiran abun hawa. "Wannan wani irin kitso ne da sassafe." Mimi tace.

Kafaɗu Maimoon ta daga. "Kaman tafiya zasu yi anjima."

Suna tsaye keke napep ya tsaya, Maimoon ta ce Mimi da Sadiya su shiga, ita zata tare wani. Sallama ta musu tare da musu fatan alkhairi. "A maida hankali."

Bai fi minti biyu ba, wani ya kara tsayawa. "Unguwan sarki zaka kai ni," ta ce, sannan ta mai kwatancen gidan.

A ƙofar wani babban gida aka aje ta sauka tayi sannan ta mika mai kudin. A hankali ta taka gaban get din, dutse ta dauka ta fara bugawa. A ladabce ta gaida tsohon da ya bude mata ƙofa, shi ma ya amsa mata cikin sakin fuska, kasancewar ta ɗan ɗaɗe tana zuwa masu kitson, ya shaidata.

Palon babu kowa a ciki,  ta dinga sallama amma ba'a amsa ba. Wajan mintin ta biyu a tsaye kafin wata matashiya ta fito. Ba fara ba ce chan chan, amma da ɗan haskenta. "Haba Maimoon, gidan sai kace bakon ki, ai da kin hayo. Ina ma Amira wanka ne shi yasa banji ki ba. Sannu da zuwa."

Murmushi kawai ta yi. "Ina kwana Anty Salma."

"Lafiya qlau Maimoon, ya su Ummi?"

"Suna nan lafiya."

Murmushi Anty Salma tayi.

Maimoon tayi wata shida tana mata kitso, ita da ƴan matan ta guda biyu. Sun haɗu a gidan ƙawar Anty Salma, tana ganin kitson ta yi maza ta amshi numbanta. Matar na burgeta, babu ruwanta, kullum cikin fara'a take, ga janyo mutum a jiki. Yanda take mata sai ka rantse sunyi shekaru da sanin juna. Dan ma dai miskilancin Maimoon na hanata sakin jiki da ita, da sabon su yafi haka kam.

Palon da ke sama ta kai ta. "Bari in kawo maki breakfast Maimoon."

Da sauri ta ce. "A'a, ki bar shi kawai. Naci abinci."

Ƴar hararar ta tayi, "Ai dama nasan ba ci zakiyi ba, mun kusan faɗa dake wallahi. Ko ruwa ban taɓa gani kin sha a gidan nan ba."

"Ba haka bane Anty Salma," tayi saurin cewa, ta naji a ranta bata kyauta ba. "Kiyi hakuri."

"Dama abunda kike cewa kenan kullum ai. Bari in turo miki Ikram a fara mata."

A hankali ta zare hijab da niqabi dinta. Bayan minti ɗaya a kayi sallama. Yarinya ce ƴar shekara biyar, sanye take da doguwar riga ta kanti me gajeran hannu. Da gudu ta shigo. "Anty Maimoon ina kwana."

Murmushi mai faɗi Maimoon tayi sanda yarinyan ta zauna gefenta. Yaran Anty Salma na burge ta, kullun dagwas zaka gansu, cikin tsafta, da babban abokin nata, ƙamshi. Maman su ma haka, shi yasa bata ƙi tayi awanni cikin gidan ba. Yanzu haka burner dake jikin bangon a kunne take, wani sanyayyan kamshi ya gauraye dakin gaba ɗaya.

Rayuwar Maimoon.Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon