BABI NA TALATIN DA HUDU

988 168 61
                                    






~
BABI NA TALATIN DA HUDU
~






A hankali ta mike zaune ta jingina da kan gadon. Ta na ganin nos ta shigo ta bata rai. Nos din bata san lokacin da dariya ya kubce mata ba.

"Haba Maimunatu, wannan hada rai haka." Dariya sauran 'yan dakin su ka yi.

Anwara, Nanah da Rukayya kenan. Dan Sayf kudin (private ward) ya biya.

Fuska Maimoon ta kara tsukewa. Tsakanin zuwanta asibitin da yanzu an yanzu an yi mata allurai sun fi biyar. Allurai biyar a cikin awa arba'in da hudu ai ba wasa ba ne. Ga nos din da ke mata zafin hannu gareta.

Ashe rashin sani ne ya ke sa ta cewa gwara a yi mata allura da a bata magani. Dan yanzu da gudu za ta hadiyi ko kwayoyi nawa ne da wannan alluran da ake mata.

Haka dai rai a bace nos ta yi aikinta ta gama. Kwanciya ta koma ta yi dan zaman na takura mata.

"A zubo abinci?" Anwara ta tambaye ta.

Kai ta girgiza mata. Sam bakinta babu dandano, komai ta ci kaman ta na cin dussa. "Zan dai sha tea."

Cikin kayan da su Nanah su ka kowa da safe ta bude ta dauko kofi da cokali, sannan ta hada mata tea din. Ita ta kwana da ita. Idan ba'a sallameta yau ba kuma Rukayya zata kwana.

Tea din shima ta na sha ne kawai amma ba wai dan ta na jin dadin shi ba. Tana cikin sha wayarta ta yi kara daga cikin jakar Nanah. Ita ta sha ma wayar ta fadi ne.

Ummi ce ke kira. Maimoon na amsawa Ummi ta fara jero mata tambayoyi.

"Ummi.... Ina wuni?"

Duk wanda ya ji muryarta ya san bata da lafiya.

"Ba ki amsa ni ba? Me ya same ki? Asibitin na da kyau? Ana kula da ke? Ko dai za ki taho gida ne, ko kuma ni in taho."

"Haba Ummi," ta jiyo muryan Baffa. "Ba su Anwara sun fada miki komai ba, ki kwantar da hankalinki. Maimu ya jikin?"

"Da sauki Baffa. Ina wuni?"

"Lafiya lau. Allah Ya kara sauki. Kina dai shan maganin da aka baki ko? Nasan halinki."

Dariya Maimoon ta yi. "Ina sha Baffa."

"Toh Allah Ya kara sauki. Duk abunda kuke bukata ku kira ku sanar dani. Jiya mun yi magana da Anwara na tura mata kudin magungunan da na daki."

"Mun gode Baffa. Allah Ya saka da alkhairi, Ya kara budi."

"Ameen Maimu, Ameen. Ki kula da kan ki kin ji? Ki sha magani akan ka'ida, kuma ki dage da addu'a. Ga Umminku nan ta na son tada hankalinta."

"Maimu," Ummi ta kira.

"Ki kwantar da hankailinki Ummi. Na ji sauki ai. Zuwa anjima ma wata kila a sallame ni."

"Toh Alhamdulillah. Idan kun koma hostel din dan Allah a kiyaye. Hala baki kwana cikin net ne har sauro ya jiye ki."

Tunda ta cire net din ta wanke, bata maida shi ba. Shiru ta yi, ai ko Ummi ta dago ta.

Rayuwar Maimoon.Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt