~
BABI NA ASHIRIN DA TARA
~Wani lokacin, Allah Ya kanyi jinkiri saboda Ya kare bayinSa daga musiba. Lallai jinkiri ba hani bane, kuma ba rashin amsar addu'ah bane. Wani lokaci jinkiri yana zuwa ne da shiri mai kyau, wanda zaizo da alkhairi, amma sai lokacinsa yayi.
Allah yasan abinda bayinSa ke rokonsa, dare da rana, zai amsa da mafificin abu. Allah Ya kan bawa bayinSa abu a lokacin da ya dace. Idan alkhairi ne, zai sameshi. Idan sharri ne, zai jinkirta zuwa wani lokaci na daban.
Kada dan Adam ya yi shakka akan Mahaliccin shi, yasan buqatunka, kuma zai amsa alokacin da ya dace. Lallai Mahalicci, yasan abinda ke zuciyoyin bayinSa tun kafin su furta.
Babu kalaman da za su yi bayanin yanda wannan bayin Allahn ke ji. Duk lamarin da zai sa manya uku dattawa zubar da hawaye kaman haka ba karamin lamari ba ne. Daya a cikin su ya rike hannuwan Baffa gam sai kuka ya ke ya na kiran sunanshi.
Ko ba'a fada ba da an gansu tsaye tare an san akwai dangantakar jini tsakanin su mai karfi. Dukkan su ukun kaman an kwafi fuska daya ne an manna musu sai dai kowa da na shi banbancin kalilan.
Dole su Anwara su ka rika kallon Baffa ranan da su ka zo. Duk da yanayin jikinsu ba daya ba saboda banbancin halin rayuwa, kallo daya ya isa ka gane tsananin kama da su ke yi.
Suna shigowa Baffa ya mike zumbur! Ko ba'a fada mai yasan 'yan uwanshi ne da ya ke ta nema. Tun a waje daya ya fara hawaye. Da kyar aka samu su ka saita kan su sannan su ka shiga cikin falo.
Daya a cikin su da ya gabatar da kan shi a matsayin Alhaji Nasir Lamido, ya yi addu'a mai tsayi. "Alhamdulillah, Alhamdulillah. Ba mu da abun cewa sai godiya ga Ubangijinmu da ya nuna mana wannan ranan da mu ka dade muna jira na tsawon shekaru. Kaman yanda na fada, sunana Nasir Abdulkarim Lamido, wannan kuma kanina ne Abdullahi, shine maihaifin su Anwara."
Nan ya fada yanda Anwara ta turawa mahaifinta hoton Baffa, ganin hoton nan ya sa su ka bar abunda su ke yi su ka taho.
"Mahaifin mu har ya bar duniya bai daina neman ka ba Ya Muhammad. Wasiyar da ya bar mana ita ce mu tabbata mun nemo ka. Mahaifiyar mu na nan da rai, a kullum addu'anta ta sa ke ganin ka kafin Allah Ya dauki ranta."
Wani sabon shafin kuka Baffa ya bude. Ashe ya na da gata haka?
"Mahaifinmu na da yara da dama, amma mu bakwai ne wurin Mama, Allah Ya yi wa biyu rasuwa."
Alhaji Nasir ya fadi kadan daga tarihin dangin su. Sannan aka kira Mama, mahaifiyarsu aka hadata da Baffa. Babu wanda ya iya magana cikin su sakamakon kukan da ya ci karfin su gaba daya.
Maimoon ma kuka kawai ta ke yi. Ganin yanda Baffa ke kuka sosai ya karya mata zuciya. Sai dai wannan ta san kukan farin ciki ne ba irin wanda ya dade ya na yi ba.
Yaran sun tashi sun bar falon dan manyan su yi magana. Su na shiga ciki Maimoon ta rungume Anwara, bata san da wasu kalamai za ta yi amfani da su ba dan gode mata ba. Ta yaye wa Baffanta abunda ya dade ya na damun shi har ya kusan hallaka shi.
"Adda Moon shi ya sa ke da su Nanah kuka shaku sosai haka, ashe mu 'yan uwa ne." Inji Sadiya ta na murmushi mai hade da hawaye.
Dariya du ka su ka yi. Mimi ta ce: "ban san ya zan yi muku bayanin yanda na ke ji ba. Gani na ke yi kaman mafarki."
Ummi ce ta leko ta ce ma Maimoon ta kawo abinci. Fuskarta itama duk ta yi ja, musamman saman hancinta.
YOU ARE READING
Rayuwar Maimoon.
RomanceRayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka. Me yasa suke g...