BABI NA HAMSIN DA BIYAR

1.7K 188 134
                                    









~
BABI NA HAMSIN DA BIYAR
~







A kwana a tashi babu wuya wurin Ubangiji. Sayfullah da Maimoon suna rainon cikin su cike da kauna da kulawa. Kaunar da Sayfullah ke nunawa Maimoon a baya ba komai bane idan aka hada da yanzu, kaman ya hadiye ta dan so. Da ta motsa zai ce lafiya. Kafin ta bude baki ta ce tana bukatar wani abu har an kawo mata. Duk wani abu da ya zan zata bukata ko kuma zata nema saboda yanayin da ta ke ciki ya kawo ya ajiye.

Ta kan tsokane shi ta ce, "Habibi anya kuwa," sai dai ya yi murmushi ya girgiza kai ya ce, "Noor kenan."

Cikin kaman jira ya ke a san da zaman shi. Laulayi ta ke yi sosai har ya kai ga wani lokaci dole ta ke hakura da zuwa makaranta. Sayfullah ya so daukan hutu wurin aiki Maimoon ta ce sam maganan haka bata taso ba.

Yanzu ta gama amayar da duka abunda ke cikin ta. Sayfullah ya kawo mata da gurasa da ya dawo daga wurin aiki. Ba ta dade da gama ci ba ta dawo da shi, ko matsawa bata iya yi ba a nan falon tayi.

Sayfullah na tayi mata sannu yana shafa mata baya har ta gama. Hawaye ne suka cika mata ido musamman da ya je ya dauko kayan da zai gyara wurin da su. Babu alamun kyama ko takaici ya tsaftace wurin tas. "Tashi mu je ki kuskure bakin ki," ya ce mata bayan ya gama. Kawai sai tasa kuka. Sayfullah yayi tsaye yana kallonta. Kuka ta ke yi kaman wanda aka yi wa duka.

"Noor menene?"

"Dama gurasan bai isheni ba kuma gashi yanzu na amayar da shi. Kuma bakina babu dadi."

"To ki yi hakuri, yanzu zan sake siyo miki gurasar."

"Bana so, ni ice cream zan sha."

Dariya ke cin shi amma ya san idan ya kuskura yayi ze janyowa kan shi ne dan haka ya gimtse abun shi. Kayan zaki da basu dameta a da ba su suka zama abincinta yanzu. Da zai kyaleta su kadai za tai ta ci. Yanzun ma bai kamata ta sha ice cream ba amma idan ya ce a'a shima ya san sauran.

"To mu je ki kuskure bakin sai in dauko miki."

A kicin ta kuskure bakin Sayfullah ya bude freezer ya dauko babban robar ice cream. Cikin satin nan ya siyo amma har ta sha rabi. A nan kicin din ta shanye abunta tas harda sude bowl.

"Shikenan?" Ya tambaya. "Babu wani abun da kike so?"

Kai ta girgiza. "Babu. Nagode Habibi."

Hancinta ya ja a hankali. "Mu tafi."

Falo su ka koma inda yake aikin shi kafin ta yi amai. Laptop din shi ya dauka ya cigaba da aiki ita kuma tana zaune a gefe tana kallo.

Sayf yana ta aiki bai lura da tayi barci ba saida ya ji ta daura kanta a kafadar shi. "Daga shan zaki sai barci as usual," ya ce yana girgiza kai. Laptop din ya ajiye gefe ya dauketa ya kaita daki.

A gefen gadon ya zauna yana kallon fuskarta. Hannu yasa ya shafa kumatunta yana ji sonta da tausayinta na ratsa shi. Murmushi yayi yana hango da ko 'yar zata haifan musu. Kafin ya iso duniya son shi ya cika mai zuciya. Babu shakka babyn zai samu duk wani kulawa da Sayfullah bai samu ba. Sumbatar goshinta yayi sannan ya koma ya cigaba da aikin shi.

Bayan sati daya su ka je asibiti awo. Tana cikin sati na sha uku ta kusan fita daga (first trimester) anyi gwaji komai na tafiya daidai yanda ya kamata sai dai har yanzu (morning sickness) din na nan duk da likitar ta ce zai tafi.

Rayuwar Maimoon.Where stories live. Discover now