~
BABI NA TALATIN DA TARA
~Motar tsit, babu karan komai sai na AC da ke busawa a hankali. Dukkan karfinsa Sayfullah ya ke amfani da shi dan kar ya juya ya kalleta a gefen shi, duk da yanzu ta rufe kyakkyawar fuskarta.
Fa tabarakallahu ahsanal khaliqeen. Abunda kawai ya rika nanatawa a zuciya. Duk yanda ya so dauke idon shi daga kanta a lokacin ya kasa, saida ta mike da sauri ta yi kicin.
Bai taba tsammanin ganinta ba da ya je ajiyewa Habib sako ba, da kamar ba zai zo ba ashe alkhairi ne ke kiransa.
Tunda su ka shiga mota bata ce kala ba, asali ma kanta a duke ya ke tana wasa da yatsunta. Murmushi ya yi, ya na tuna yanda aka yi ta yarda ya maida ta gida. Da kyar Salma ta shawo kanta, ya na jin su daga kicin din.
Tunda ta fito ta gaida shi bata sake ce mai komai ba. Saka da warwara ya ke a ran shi akan yanda zai fara yi mata magana. Mai zai ce mata? Ta ina zai fara? Zata fahimce shi?
Idan ba ka gwada ba ta ina zaka samu amsoshin tambayan ka? Wata zuciyar ta ce da shi.
Boyayyar ajiyar zuciya ya sa ki, daidai lokacin ya tsaya cikin (hold up). Jin motar ta daina motsi ya sa Maimoon ta dago kanta su ka hada ido, da sauri ta kauda kanta.
"Noor, ba za ki mun magana ba?" Shiru ba ta ce komai ba. "I'm sorry, ki yi hakuri. Yanzu na yi mi ki bayani za ki fahimce ni?"
Kai ta gyada ba tare da ta kalle shi ba. Bai san ya daina shakar lumfashi ba saida ta ba shi amsa, a hankali ya yi ajiyar zuciya. Sai dai matsalan ta ina zai fara?
"Kin taba jin inda uwa ta yarda dan ta?"
Janye idanunsa ya yi daga kanta ya maida su kan motocin da ke gaban shi. Ba zai iya kallonta ba dan sai karfin gwiwar da ya samu ya tafi. Ya na jin idanunta na yawo a kan fuskarsa.
"Iyayena sun rabu ina da shekara uku. Tunda mahaifiyata ta bar gidan ba ta sake bibiyar wani hali na ke ciki ba. Aure ta sa ke yi ta bar kasar gaba daya. Ba dan Ammah da Mami ba da ban san a wani hali zan taso ba. Su kadai su ka zame mun inawuna a lokacin da gidan mahaifina ya zame mun tamkar gidan kurkuku saboda azaba. Alhaji ya sake aure, shima ya yi watsi da al'amarina ya bar ni hannun matarsa. Azabar safe daban ta rana daban. Ban sake ganin mahaifiyata ba sai da na kusan shekara ashirin. A lokacin na koma wurin Mami saboda karatu."
Kallon Maimoon ya yi, dukkan hankalinta na kan shi. Bai tsawaita kallon ba ya sake dauke kan shi. Kallon da ta ke mai ya karya mai zuciya.
YOU ARE READING
Rayuwar Maimoon.
RomanceRayuwa na cike da ƙalubale kala kala. Allah na jarabtar bayinSa a duk yanda Ya so, hakan ba yana nufin ba Ya son su ba. Kyawun halitta, tarin dukiya ko mulki ba shi ke nuna son Allah akan bawanSa ba. Amma dayawa mutane kan manta haka. Me yasa suke g...