Ɓarauniyar nama

565 26 8
                                    

Wannan littafi mallakar Azizat Hamza ne.  Ba a yarda wani ko wata su sarrafa shi ta kowani siga ba, ba'a yarda a karanta shi a youtube channels ba, ba'a yarda  a kwafa ko a juya labarin ba tareda hakkin marubuciyar ba.
©AZIZAT HAMZA 2022

Wannnan littafi ƙirƙirarren labari ne. Allah ya yafe min kura-kuren da suke ciki Amin.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

                                ***

001 Ɓarauniyar nama.

Duk ranan Lahadin karshen wata akan yi Family meeting a gidanmu. Wannan family meeting da ake yi ya banbanta da wanda ake yi na gaba ɗaya iyalen marigayi Alhaji Muhammadu Ubandoma wanda ya kasance Kakanmu, Duk wanda ya haɗa jini da familyn Ubandoma walau ta wajen mace ko namiji duk ana haɗuwa ayi meeting ɗin dashi, ana yin meeting ɗinne bayan wata uku-uku, watau sau huɗu kenan a shekara.
Kai akwai wani meeting ma da Hajiya Kaka ke shiryawa tsakanin 'ya'yanta duk sanda ta ga dama, musamman ma idan wani gagarumin abu na alkhairi koma na sharri ya samu 'yayan Hajiya Sadiyya. Matar nan ta kwana biyu da rasuwa amma har yanzu Hajiya Kaka ba ta dena kishi da ita ba.

Yau ma kamar kullum shirye shiryen meeting ake yi kuma Mama ce ke da girki dan haka duk wani kanshi da ke tashi a gidan daga kichen ɗin sashenta yake fitowa.
Karfe goma na safe zuwa shabiyu na rana ake meeting ɗi, dan haka duk wanda ya san yana cikin list na masu tayata aiki to dole ya kasance a kitchen a wannan lokaci.

A gidanmu wajibi ne a kammala abin karyawa kafin karfe bakwai na safe. Wannan jazaman ne dan kuwa in dai  mace ta bari yara suka makara zuwa makaranta saboda bata yi abin karyawa da wuri ba tabbas za ta haɗu da fishin Alhaji, in tai haka fiye da sau  ɗaya kuwa tabbas za ta bada bayani idan aka zo meeting na wannan wata.

Ina cikin masu aiki a kitchen amma tsabar lalaci sai da aka kusan gamawa   na shigo kitchen ɗin. Anty Firdausi ta ce maza na fita na bar musu kitchen tunda iskanci ne ya hana ni fitowa tun ɗazu.
"Anty Firdausi Allah Hajiya Kaka ce ta sakani aiki a ɗakinta" na faɗa ina zumɓura baki.

Mama da ke faman tsame  nama a cikin mai ta daka min tsawa "zaki samu abunyi ne ko sai na zo na ɓallaki a wajen"

Na shiga kitchen ɗin da sauri ina faɗin " Mama mi zan yi?"

"Uwarki za ki yi. Shashasha kawai"
Na yi raurau da ido hawaye na shirin zubo mini, ba dan komai ba sai dan bana iya juran a zageni da uwata koda kuwa a zahiri ba wai ita ɗin ake zagi ba, amma in dai za a yi zagi da uwa to kodai na yi kuka ko kuma na fusata na fara masifa. Mama ce tayi zagin dan haka ba halin masifa.
 
"Maza ki je ɗaki ki fito min da kulolin Alhaji"

Na tura baki ina faɗin 'wai sai ayita cewa mutum uwarshi bayan baiwar Allah ta jima a cikin kasa'

"Mi kike faɗa wai?"

"Mama ban fa ce komai ba"

"Karya nayi kenan"

"Mama to kullum ki dinga ɓoye kulolin Alhaji a ɗaki kaman da gwal aka yi su"

"Sahala zan ci mutuncinki a gidan nan"

"Sahla sunana" na faɗa tareda ficewa da gudu.
Ban kawo mata kulolin ba sai da na tabbatar ta ɗan huce, lokacin dana shigo da su ma masifa take yiwa su Anty Firdausi akan tun ɗazu basu gama haɗa zoɓo da kunun aya ba.

Ni dai ban yi wani aikin wahala ba illa ɗauko wancan miko wannan. Da aka gama komai kuwa aka barni da su Safiyya da Nasiba muna zuzzuba zaɓo a cikin gorunan ruwa na swan water.

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now