Sahla a Paris

478 10 3
                                    

015...✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

***

Ban ɗauka zaman jirgi akwai wahala ba. Na ɗauka kaman yadda nake gani a film ne, wato kowa zai zauna ana kallo ana cin abinci, fuuuu sai ka ji har an yi landing. Probably irin awa biyu ko uku ɗin nan.

Gaskiya na zaunu. Ko dai dan ban taɓa zuwa wani waje mai nisa bane. Iyaka dogon tafiyata Gombe to Abuja ne. Na yi bacci na tashi amma jirgi bai sauka ba.
Kaka kam ko ajikinta, ita da ta saba shiga jirgi kenan.  Lokacin da fitsari ya matseni sosai sai na ɗaga hannu sama. Kaka tayi bacci. Wata flight attendant ta zo wajena, nace mata zan yi fitsari. Ta raka ni banɗaki. Ina shiga banɗaki sai amai, duk abinda na ci a cikin jirgin nan sai dana amayar da shi.

Na gama aman na wanke fuskata na fito. Ina takowa a hankali muka haɗa ido da shi. Littafi yake karantawa amma yana ganina ya sauke littafin yai min tambaya da ido irin 'are you OK' ɗin nan. Na girgiza masa kai alamar babu komai. Na koma wajen zamana na zauna, har yanzu Kaka bacci take nima na gyara zama na mike kafafuwana na kwanta.

Kusan awanmu tara ko goma a sararin sama kafin jirginmu yai landing. Zuwa lokacin na yi wani laushi. Gaba ɗaya na kagu mu sauka. Har wani zazzaɓi nake ji.  Ga yunwa kamar hanjina zasu tsinke. Na kasa cin komai a jirgin nan har muka isa
Charles de Gaulle airport.

Mun isa Paris da dare. Ina tunanin zan ga anzo an ɗaukemu da wani babban mota amma da muka fito sai naga Uncle Faruku ya tsaida mana taxi.
Aka shigar mana da kaya cikin boot muka fara tafiya.

Ni dai zuciyata ta fara raya mun anya Uncle Faruku na da kuɗi kamar yadda mu ke hasashe. Taya za a ce mun sauka a airport ba za a zo a ɗaukemu ba kaman yadda ake a littafi ko film.

To ko dai direbansa baya nan ne?

Inata sake-sake har mai taxi ya tsaya a a wani katon gida.
Daga korafi sai na koma sake baki galala ina kallon mansion ɗin da aka kawo mu.

"Yanzu wannan gidanka kenan ko Otal?" Kaka ta riga ni furta wannan tambaya dan abinda ke raina kenan.

"Kaka gidana kenan"

"Ya Subhanallahi! Faruku shekara da shekaru kana zama a wannan ɗimemen gida kai kaɗai. Gaskiya ba zai yiwu ba idan na koma dole mu yi zama da iyayenka, dole ne ka ajiye iyali"

Shine a gaba muna biye da shi har muka isa kofar gidan ya buɗe mana kofa.
Muna shiga wani ɗan corridor muka fara gani sannan muka karisa cikin wani makeken falo. Kai! falon nan zai yi falon Alhaji biyu. Falon na haɗe da dinning area. Daga ta jikin dinning ɗin akwai staircase da zai kai ka sama. Komai na falon fari ne da ruwan toka. Curtains ɗin ash ne kujerun kuma farare. Babu wani tarkace a falon dan akwai enough space a wajen. Akwai paintings dayawa da aka saka a jikin bango.  Wasu paintings ɗin na flowers ne ko na bishiyoyi sai guda biyu wanda suka fi girma suka fi ɗaukan hankali. Ɗaya painting ɗin na wata tsohuwa ce ɗaure da zani wanda bai gama rufe mata kirjinta ba, tana zaune a bakin wani bukka idanunta cike da  damuwa kamar zata yi kuka. Zanen ya tsaya min a rai domin ya fito raɗau kamar hoto Black and white ɗin nana.

Zane na biyu na wani yaro ne da aka rufewa baki daga ta baya. Yaron ya zaro ido kamar yana ihu aka rufe bakin.

"You should go and rest"
Na waigo a tsorace dan ban san yana bayana ba.
Kai Uncle Faruku dogo ne, dana juyo sai dana ɗaga kaina kafin na kalleshi da kyau. Fiskarsa babu fara'a ko kaɗan, kamar dai ba a son ransa muka zo Paris ba.
To ko ma yanene ni kam na zo kenan babu komawa.

"Uncle F Kay wannan zanen yayi kyau" na nuna masa zanen yaron.

"Yayi kyau?" Ya faɗa a fusace.

"Yayi kyau? Ya sake nanatawa. Kamar ya damu sosai da zanen.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 26, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now