TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.
✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈
010...Coustaliye...
***
A inda Faruk ya ajiye key ɗin mota ko kallon wajen Alhaji bai yi ba.
"Aliyu aure nake so kayi. Duk wani Alheri da zaka min ba zan ji daɗi ba kamar ka ajiye iyali. Ka kalleka, ka kalli kaninka Mustafah. Ba ka ganin nitsuwa a tattare da shi. Kwanan nan ya saka Kamal ɗinsa a makaranta. Aliyu ba mota nake so ba, ba gida nake so ba, ba kuɗi nake so ba. Aure nake so kayi. In dai farin cikina kake so to aure zaka yi."
"Dad ka dena comparing ɗina da Mustafa. Kowa da kaddararsa. Zan yi aure idan Allah ya nufa"
"Haka kake faɗa duk shekara. So kake sai an yi auren su Abbas kafin kai kayi aure. Minene matsalar ne?"
"A kara min lokaci. Zan yi aure"
"Al'amarinka Faruk sai addu'a. Ni kam babu abinda za ka yi ka burgeni sama da aure. Da Allah nake rokon ka idan akwai wata matsala ne da bamu sani ba ka gaya mana"
Faruk ya girgiza kai.Alhaji ya cigaba "An nuna maka 'yan mata cikin dangi da abokai amma duk babu wacce ta maka. Ance ka fitar da mace ka ki. So kake da girmanka mu maka auren dole ne"
Faruk yai shiru. Babu abinda zai iya cewa. Ba za su gane matsalarsa ba. Kila aure baya cikin kaddararsa.
Yana fitowa daga sashen Alhaji ya wuce sashen Kaka. Itama ɗin ya san duk kanwar ja ce. Dan duk abinda Alhaji ya faɗa itama shi zata maimaita. Amma dolensa ne ya je ya mata ta'aziyya tunda shine musabbabin zuwansa kasar.
Ya so zuwa a lokacin rasuwan amma babu dama saboda aikinsa, infact a South Africa yake lokacin da aka yi rasuwar.Kaka na kishingiɗe akan tabarma hannunta da mafifici tana fiffita. Ya tsugunna ya gaisheta.
"Faruku ne?"
"Kaine a gidan namu. Sannu da zuwa"
Ina Sahala take ta ɗauko maka kujera a ciki.
"Sahala" ta kwala mata kira. Amma shiru"Haka nake fama da ita fa, yanzu haka kallo ta je yi a ɗakin Rafee'atu"
Ta ɗan tashi ta zauna tareda mika masa mafificin hannunta.
Gaskiya rasuwan 'ya'yanta biyu ya taɓa Hajiya Kaka. Gaba ɗaya ta rame masa compared to wancan zuwan da ya ganta.
"Na ce ko zaka zauna a tabarma kafin Sahala ta zo"Ya girgiza kai, bai saba zama a kasa haka ba. Yana mamakin yadda mutane ke iya zama a kasa har su harɗe kafafunsu. Shi idan ka ga ya zauna a kasa to sallah ne.
"Hajiya yaya hakuri"
"Hmm Umaru da Bintu sun tafi saura ni. Ance Umaru da shahada a bakinsa ya cika. Kaga kuwa ya huta. Allah yai musu gafara"
Faruk ya amsa da Amin.
"Yanzu Faruku kai kenan haka zaka cigaba da zama babu aure. Ko dai.. Sahala, ya haka?"
"Wallahi sai dai ayi asaran abinci a gidan nan. Haka kawai ku maida ni 'yar iska. Wallahi sai anyi meeting a gidan nan yau. Babu 'yar iskar da zan sake yiwa aiki"
Tana tafe niki-niki da katuwar tukunya akanta ta yi wani katon gammo da gyalenta.
Shi da Kaka suka zuba mata ido. Tana zuwa tsakiyarsu tace Kaka Dan Allah tayani na sauke wannan tukunyar.
Kaka ta mike da sauri ta kama mata suka sauke tukunya.Kaka ta buɗe marufin tukunyar, tururi ya baza wajen.
"Minene wannan Sahala?"
"Ba Mama bace za ta maida ni taɓaɓɓiya. Na dawo daga wajen registration ɗin JAMB da uban yunwa wai abinci ya kare. Tace na je na dafa mana couscous guda biyu ni da su Abbas da su Hanifa dan suma ba su ci abinci ba. Shinefa na ga ta ɗaura ruwan kayan miya a wuta yana tafasa. Da farko dana zuba ledan couscous biyu a ciki sai naga yayi ruwa, shine na shiga store na ɗauko biyu na kara a kai, shima couscous ɗin kamar magani ya ki shanye ruwan. Ni kuma na ɗauko ledan taliya guda uku na juye a kai.
YOU ARE READING
SAHLA a Paris (Hausa novel)
RomanceRashin ƙarfin mazaƙuta matsala ne babba da zata iya hana namijin daya doshi shekara 40 yin aure. Sai dai a ɓangaren FKay Ubandoma bai taɓa tunanin samun sauƙinsa yana tare da yarinyar da ya girme mata da shekaru ɗai-ɗai har 18 ba. SAHLA dai ta shiry...