iphone 6

188 8 0
                                    

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

012...iphone 6...

Na gama soyayya. Na dena soyayya har abada. Koda yake laifina ne ai. Ni ce wawuya. Ranan da ya tambayeni numbar bra ɗina dariya nayi. Na tura mishi emoji na rufe ido haɗe dana dariya.

"I'm serious dear. Na san tiny boobs ba ɗinki ba zasu wuce size 32 ba, ko 34 ne, kai 32/34 nema?"

Dariya nayi ina mamakin ya akayi ya san size ɗina. Ban ɗauki irin wannan hiran a matsayin wani abu ba.
Lokacin da yace yana son mace ta saka jan bra da pant. Har nima na ji ina son jan underwear. Da Anty Amarya ta bamu kuɗin underwear muka je kasuwa da su Safiyya maimakon na sayi bakake kamar yadda na saba sai na sayi jajaye guda shida.

Allah ya tsinewa soyayya. Ba zan sake soyayya ba.
Ni ban gane ba. Dama haka soyayyar take? ko kuwa dai nawa ne ta zo a hakan.

Ɗan iska kawai.

Na cire kayan jikina gaba ɗaya na turasu karkashin gado, anjima zan je na kona su. Rufin asiri na lokacin dana shigo ɗaki Kaka ta shiga banɗaki. Dan haka na samu na ɗaura zani kafin na nemi abinda zan saka.

But it hurts. Ina son Affan. Irin soyayyar da Sharukh Khan ke yiwa Kajol a Kabhi Khushi Kabhi Gham, irin soyayyar da Jack ke yiwa Rose a film ɗin Titanic.
Tunda na amince da Affan ban sake tunanin kowa da soyayya ba.

"Sahala?"

"Lafiya kike kuka?. Wani ne ya dake ki. Faruku ne? dan yanzu ya bar nan"

Na girgiza kai. Idan na faɗa mata gaskiya za ayi tashin hankali a gidan nan. Sannan na san kowa  zai yi min dariya. Laifina ne ai, ni na kai masa abinci har ɗaki.

"To miya sameki?"

"Faɗuwa nayi shine abincin dana ɗauka ya zube"

"Shine zaki yi kuka. Hawaye ne ya miki yawa. Matsa ki bani wuri ni sallah zan yi"

Bayan na saka kaya na fara neman wayata dan na jona a chaji. Na duba ɗakin kaf babu waya.  Wayyo Allah na! Ko dai na bar wayan a ɗakin Affan ko kuma ya faɗi a hanya.
Ba zan iya komawa ba, ba zan iya komawa ba. Na dafe kirjina saboda wani tsoro daya shige ni lokaci guda.
Ba zan iya komawa ba.
Ba zan iya fita ba.
Na zauna a kasa daɓas ina tunanin abinyi. Ya Allah! Sai yanzu ma na fara jin tsoron abinda ya faru.  Da ace Affan ya ci galaba a kaina da shikenan fa. Ba zai taɓa aurena ba, ba zan samu miji ba.

Ko Sallah ban yi ba na kwanta na rufe kaina, ina kwance sai zazzaɓi ya rufeni.
Chan dare Amal da Hanifa suka kawo mana abinci tunda ban je na karɓo ba kamar yadda na saba.

"Hajiya Kaka wai ina Sahla ne?"

"Ku shiga ciki tana kwance zazzaɓi ya rufeta"

Inajin suna shigowa na sake rufe fiskata da kyau.

Hanifa tace "Sannu Cook. Abincinki yayi daɗi fa"

Amal tace " And the donuts..."
Suka kwashe da dariya.

Allah yasa ba su ga wayata ba, dan na san zasu ga texts ɗin dana turawa Affan. Wani lokaci idan na tsinci kalaman soyayya a littafi ko film sai na kwafa na rubutawa Affan na tura masa.

"Mun sani sarai kina jinmu"
"Wai ke duk haukanki ma baki san cewa Affan ba sa'anki bane. Affan yana da budurwa 'yar jami'a, wayayyiya"

"Girlfriend ɗin Akhi a Boston take karatu, sunanta Sarah. Like iyayenta are damn rich. Ki dena bibiyan Akhi ba abinda zai yi dake"

Innalillahi! Wai ni nake bibiyan Affan. Abinda ya gaya musu kenan.

Suna fita daga ɗakin na buɗe fiskata.
Ba zan taɓa Yafewa Affan ba. Kuma sai na ɗau fansar abinda ya min ko ba yau ba.

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now