sausage

192 8 0
                                    

007 Sausage...

***

Kowacce rana rana ce ta ambaton Manzo Rasulillahi. Kowacce rana rana ce da za a gode, ayi murna da haihuwarka Aminullahi. Kowacce rana rana ce da za a yabeka ai maka salati sannan a sake yabonka Habibullahi.
A yau ina kara jaddada Salati da yabo gareka ya Manzon Allah.
Allah Albarkacin Sayyidul Mursalina kuma Khatimul Anbiya'i ka amsa mana addu'o'inmu, ka karemu daga dukkan bala'i da jafa'i. Ka kawo mana shuwagabanni na gari masu tausayinmu, masu rikon Amana.
Ya Allah albarkacin LAA'ILAHA'ILLALLAH MUHAMMADUN RASULULLAH, ka sa albarka a rayuwarmu, ka sa albarka a kasuwancinmu, ka yiwa 'ya'yanmu albarka, ka kara mana  ilimi, basira, arziki da kuma imani. Ka rabamu da son zuciya da zalunci. Allah ka shiga lamurranmu. Allah ka jikanmu, ka gafarta mana zunubanmu, ka karbi tubanmu ka kuma sa mu mutu cikin imani. Ya Allah kuncin talauci, kuncin zuciya, kuncin matsi, kuncin bashi, kuncin karayar arziki da asara, kuncin jahilci, kuncin rashin aure, rashin haihuwa, rashin kwanciyar hankalin gidan miji ka raba mu da su Yaa Rahimal Masakin, Ya Rabbu Muhammad...

***

Ina sauri zan shiga sashen Alhaji na ji an kira sunana. "Sahla"
A meeting da aka yi watan daya wuce Ummi tayi maganar ya kamata a siyawa Zuhriyya waya shine Alhaji yace zai siya har da nawa da Safiyya. Hanifah ta ɗaga hannu wai ita fah. Alhaji yace sai wani shekara.
Ni Sahla guda zan yi waya, tawa ta kaina bata aro ba.

"Yaya Yusuf"

Rankwashi yai min a ka, a raina nace Allah ya isa.

"Za ki fito tun daga ɗakin Hajiya Kaka babu hijabi. Idan akwai baki a falon Alhajin fa"

"Yaya kuma sai na saka hijabi kamar wata matar aure, ɗan nan da nan ɗin"

Ya sake kai min rankwashi na kauce sauri.

"Ki dinga saka hijabi Sahla. Kinga yanzu kin girma.

"To na ji ɗin"

Na sauri na wuce shi. Mugu kawai, shi komai sai ya taɓa lafiyar mutum.

Ina zuwa na samu Alhaji yana zaune a falo yana ta lissafin wasu kuɗaɗe.

Na tsugunna na gaishe shi fiskata cike da fara'a.
Bai yi magana ba. Su Safiyya sun riga sun karɓi wayansu tun ɗazu, nima kitso na je shiyasa ba a bani tareda su ba.
Na zauna fa ina wangale ta hakora kamar mai tallen MacClean amma Alhaji bai ko dubi inda na ke ba. Ya cigaba da irga kuɗaɗen dake gabansa yana saka su a wani jaka.

"Alhaji nan ga an bawa su Safiyya waya"

Ya ɗago kai ya kalleni yace " iyi"

Na ɗan sosa kaina nace "Alhaji ba ka ce harda ni zaka siyasa ba"

"Ayya ashe ba su faɗa miki ba. Ai kaf gidan nan sun kawo karar ki sun ce ba kya jin magana. Dan haka ke da waya sai kin nitsu"

"Allah a nitse nake. Wallahi na nitsu. Tunda Kaka ta tafi Umura ba randa bana aiki a gidan nan. Jele na ke tsakanin wajen su Mama, Ummi da Umma Bilki"

"Ao haka ko?"

"Allah ka tambayi su Fadilah ka ji za su gaya maka gaskiya"

"Ina kika tsaya a haddar ki"

Na yi shiru na sunkuyar da kaina. Kusan wata biyar kenan na kakare a suratul Hudu. Da tare muke tafiya tare da Zuhriyya gashi ita har ta kusa karisa suratul Tauba.

"Kin tsaya wasa ko?"

"Alhaji Allah ba haka bane. Ka yi hakuri zan kara himma"

"Kinga iyayenki Allah ya jikan rai duk mahaddata Qur'ani ne. Kinga Sulaiman babu wanda ya kaishi nacin karatun addini. Ba dan Allah bai yi zai yi tsawon rai ba na tabbata da yanzu ya zama babban Malami"

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now