my goal

269 6 0
                                    

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

013...My goal..

***
Wayata Gionee ta dawo ga kuma iphone 6. 'Yan bakin ciki sai su mutu arzikin Sahla ya zo.

lokacin dana ɗaura layina a sabuwar waya. Naci karo da texts ɗin Affan guda uku.

1- Sahla dear, i didn't mean to. Ba halina bane, soyayyar dana ke miki ya sa na rasa nitsuwata a kanki. Dan Allah ki kunna wayarki mu yi magana.

2- i'm sorry Amal ta dawo ta ga abincin da kika kawo, na san za ta gayawa Mom. Kiyi hakuri da faɗan da Mom za ta miki. Ki amsa wayata please...

3- kin san ke kanwata ce ba zan taɓa cutar da ke ba. Abinda ya faru  was a mistake Dan Allah kar ki gayawa Abbanmu ko Alhaji...

Shege ashe ya ji tsoro. To ko na faɗawa Alhaji ne. To na ce me ?

' Alhaji na kaiwa Yaya Affan abinci shine ya tsareni a ɗaki wai zai ciremin kunya'
Wata zuciya tace min 'Hmm Sahla ki yiwa kan ki faɗa ki rike abin nan a ranki'
Allah zai saka min. Kuma sai na rama koba daɗe koba jimawa...

Ban san ana min bakin ciki ba a gidan nan sai da iphone ta shigo hannuna. Takanas na je falon Alhaji na nuna masa wayar da aka bani na ce ya tayani yiwa Uncle Faruku godiya. Ya ce sai in yi hankali da ita dan iphone ba Gionee bane.

Wallahi ko zaman minti biyar a ɗakin Kaka ba aka aiko wai a kirani.

Mama da Ummi ne suka haɗa zama.
Amal, Hanifah da sauran duk suna nan.

Ina shigowa Mama tace
"Yawwa. Sahla zo nan. Ance Faruk ya aiko miki da waya ko?"

"iphone 6 ya siya mata fa" Hanifah ta faɗa. Da wani katon bakinta a wajen.

"Lokacin da aka chanja muku waya duk tare aka haɗa aka siya muku. Dan haka ba zai yiwu yanzu ace ke kina da sabuwar waya su kuma basu da shi ba. Hanifah kin ce kuɗin wayar ya kai  nawa?"

Kafin ta bada amsa Amal tace " Mama wallahi shige masa ta yi, na san rokon Uncle F Kay ta dinga yi. Sahla ba dai kwaɗayi ba. Haka ta samu Akhi wai tana son shi harda kai masa wani shirmen abincinta"

Raina yai matukar ɓaci. Ga ɓacin ran Affan ga kuma wannan fin karfin da ake son yi min.

Na ɗaga musu wayar nace " ga dai wayata nan original iphone 6 ne kamar yadda kuka gani" na nuna musu tambarin gutsirarren apple dake jiki.

"Wacce ta ke ganin roko nayi aka bani Dan Allah itama tayi rokon ta gani ko za a siya mata"

"Waya kuma in banda Alhaji banga wanda ya isa ya hanani amfani da ita"

"Sahla rashin kunya zaki mana. To wallahi sai kin bayar da wayan nan"

"Ayya! Ummi ina ce akwai Likita mai zuwa wajen Hanifah. Ku ce masa ya siya mata iphone"

"Wannan wayar dai farar kafata ce ya kawo min".

Na juya na tafi abina ina jinsu sunata masifa ko a jikina.
Dana shigo ɗaki na fara mamakin ya akayi suka san Uncle Faruku ya siya min waya.

Ikon Allah. Ashe munafurfur ɗin gidan ne. Lokacin da naje Umma Bilki na falon tana yankawa Alhaji lemo.
Munafuka ta je ta gulmata musu ta makale a ɗaki kamar ba ta yi komai ba. Kai ta Allah ba taki ba Umma Bilki...

***
Lokacin da Alhaji ya shigo ɗakin Rafee'ah a zaune ya sameta akan sallaya ta ɗaga hannu tana addu'a tana kuka.

Ya samu bakin gado ya zauna yana jiranta. Bai taɓa nuna mata ba amma ya damu kwarai da rashin haihuwarta. Musamman ma da ya san har yanzu da lafiyarsa tunda ga shi  Zainab (Ummi) tana nan da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe.

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now