ta'aziyya

195 9 0
                                    

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

009...Ta'aziyya...

Tun talatainin dare na tashi, na kasa komawa bacci sai juye-juye nake akan gado. Idan na juya ta wajen Kaka ta sa hannunta ta makeni.
Ina SS 3 mun kusa fara rubuta jarrabawar WAEC. Har wannan lokacin ban gama nitsuwa akan abinda nake son zama ba. Ina tunanin zama Lawyer ko kuma 'yar jarida. Yayinda chan kasan zuciyata kuma ke min kwaɗayin zama matar Affan AbdulKarim Ubandoma.  Ina yawan mafarkin mun yi aure, gamu nan mun koma Egypt da zama, gamu nan mun haifi kyawawan 'ya'ya masu dogon gashi irin na larabawa.

Har zuwa wannan lokaci hiranmu da Affan ya karkata ne ta chatting a  facaebook.  A yanzu bana tunanin kowanni ɗa namiji sai Affan. Wancan wawan dake turomin text tuni na blocking ɗinsa, sai daya chanja nambobi har uku yana turomin sakon ban hakuri amma ban unblocking ɗinsa ba.

Abin mamaki ko Kaka ban gayawa soyayyata da Affan ba. Duk yadda hakan ke cina nayi shiru na ki gaya mata. Affan yace kar na bari kowa ya sani dan za a min faɗa tunda ban gama sakandare ba.

An kawo kuɗin auren Zuhriyya. Wannan yasa sauran matan suka buɗe chapter Anty Asiya wai ta fara tsufa babu mashinshini. Duk da Ummi tana jin daɗin bikin Zuhriyyar da za a yi hakan bai hanata damuwa da rashin saurayin babbar 'yarta mace Asiya ba.

Dake Asiyar boarding school ta yi tun daga JSS 1 har ta gama shiyasa bata  wani saba da 'yan gidan ba. Lokacin data gama kuwa tashi ɗaya ta ci Jamb ta samu admission a ABU Zaria, ni ban ma san mi take karantawa ba sai kwanan nan da ake tseguminta wai itama idan ta gama karatun likitancin nata karshe ko ta yi aure ba haihuwa  zata yi ba tunda ga zahiri sun gani, Anty Rafee'ah ta karashi dogon karatun bokonta yau aure samaa da shekara goma amma ko ɓari bata taɓa yi ba.

Ta wani ɓangare na ji daɗin yadda matan gidan suka kauda hankalinsu daga kaina. At least nima zan samu sa'ida.
Wani ɓangaren kuma sai na ji tausayin Anty Asiya. Gata mace har iya mace amma babu wanda ya taɓa zuwa gida nemanta koda cikin 'yanuwa ne. Kila tanada samari a can Zaria, to amma in dai akwai, ya kamata ace yadda aka tsangwama matan nan ta turo wani ya zo gida.

Oho, ni kam dai bani da matsala, tuwona maina za a yi. Ko yanzu muka buɗa baki muka faɗa yanzu za a fara shiri...

"Sahala nace ki tashi ki dafa min ruwan shayin nan ko baki ji bane"

"Kaka ke kam da shayin nan sai kace an miki jifa. Ba dama mutum ya zauna sai ki ce shayi"

"Zan make ki Sahala. Tashi ki kawo min shayi ko na haɗa ki da Yusufa"

" kai Kaka. To barin gama tura sakon nan"
Na turawa Affan reply sannan na mike idan ba haka ba sai Kaka ta ɗaga min hankali akan shayin nan. Tinda suka dawo daga Egypt ta kawo saran shan shayi safe da rana da dare. Wani lokaci sai ta sha shayi sau biyar a rana.

Dana dafo shayin na kawo na tarar da Kaka ta zabga Uban tagumi.

"Kaka miya faru? Baki da lafiya ne?"

Ta ja numfashi "hmm"

"Kaka dai"
Na ajiye shayin na hawo gadon na sakala hannuna a kafaɗanta. Duk iya shegena ina son Kakata sosai, bana so na ganta cikin damuwa.

"Kaka wani abu kike so ne?, kaza kike son ci?"

"Ana ta mutuwa wa ke ta kaza Sahala. Ni yanzu ki dubeni. Sadiye ta rasu, Laminde kawata ta rasu. Goggonku A'i ma ta rasu. Jiya-jiyan nan Kabiru ke faɗa min wai Asabe ta cika a kasa mai tsarki. Asabe fa. Yadda mutuwa ke ɗauki ɗai-ɗai ɗin nan yaushe na san zan zata ɗaukeni"

"Haba Kakaaa, ai da sauran shan ruwanki a duniya. Ai sai kinga 'ya'ya har da jikokina kafin ki tafi"

"Munafuka. So kike na ruɓe a raye ko"

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now