asirina ya tonu

188 8 0
                                    

004 Asirina ya tonu...

Shekaranshi huɗu rabonshi da zuwa Nigeria. Wannan karan ma Mustafah ne ya dage akan lallai sai ya zo bikinsa, ga kuma Alhaji da yake ta damunsa akan maganan auren Sayyidah. "Kai namiji ne Aliyu akwai lokaci a gabanka, amma Sayyidah fa. Tayi degree tayi masters mi kuma take jira?"

Ya san dalilin da ya hana Sayyidah aure, amma kuma ba zai iya faɗawa Alhaji a irin wannan yanayin ba, so yake idan an gama bikin yaran nan kafin su tafi sai ya zaunar da shi ya masa bayani, ya rage na shi yaiwa Sayyidah zaɓin daya dace.

Bai taɓa zuwa garin nan yayi irin wannan kwanakin a gidan Alhaji ba. Duk yawancin zuwansa a Fada yake sauka. Wannan karan ma Mustafah ne yayi sanadin zamanshi a gidan har zuwa wannan lokaci. Duk da ya sani Mustafan yayi hakane saboda wata manufar shi. Duk inda za su shiga haka zai dinga faɗawa mutane wai a UNESCO yake aiki.

Bai taɓa zuwa garin nan ya tsinci kansa cikin nishaɗi ba irin na yau. Tunda suka zo bai taɓa yin dariya ba ma sai yau. To him wannan luncheon da aka haɗa duk shirme ne, shiyasa ma da farko ya ce ba zai attending ba, amma da Mustafah ya nace masa dolensa ya hakura yace zai leka wajen kona minti goma ne.
Kamar yadda Mustafan ya faɗa kuɗine babu a hannun Alhaji shiyasa ya dage akan ba za ayi wani hidima ba.
Dinner da aka saka ma shi ya hana ayi, shine su Anty Rafee'ah suka ce to ayi luncheon a cikin gida tunda akwai fili da zai ɗauki mutane.  Ba karamin kuɗi suka tatsa a wajensa ba saboda wannan hidima. But to think that minti takwas da zamansa a wannan waje Awaki zasu invading wajen su kori mutane ya sa shi jin daɗin wannan luncheon da aka haɗa. Ba ma mutanen da ke gudu ne suka sa shi dariya ba. Wata yarinya ya hango sai daɗa kora Akuyoyi take cikin mutane. Ga chan wasu maza a gefe suna poli da Akuyoyin suna koransu ita kuma yarinyar idan suka iso ta wajenta sai ta sake kora su baya, gaba ɗaya dabbobin sai suka ruɗe sai ihu suke Meeeh Meeh Meeeh suna kokarin shiga cikin mutane tunda an hana su karisawa can cikin filin sannan an hana su fita.
Yana gani yarinyar ta shiga kaɗa wata Akuya wacce takalmin wata mata ya makale mata a kaho, takalmin sai reto yake kamar wani crown. A wannan lokacin ne ya ga fiskar yarinyar da kyau. A wannan lokacin ne kuma ya shiga dariya harda kyakyatawa.
Tabbas yarinyar nan ce da wannan aiki, ya sani sarai ita ce ta kaɗo Awakan nan zuwa wajen taron nan. Karfin halinta ya burge shi. A ce yarinya mai shekarunta  za ta iya aiwatar da irin wannan abu tabbas abin jinjinawa ne, she's a freaking genius.

Kokarin tuno sunanta yai da kuma 'yar waye ce a gidan tunda ba wai ya gama sanin fuskokin kannen nashi bane. Baya iya banbance asalin kannensa da kuma cousins ɗinsa. Shi duk yaran da aka haifa shekaru shabiyar baya ba zai iya banbance kamanninsu da sunayensu ba.
Cikin sakanni goma kwakwalwarsa ta tunar masa sunan yarinyar da kuma ita wacece. SAHLA ce, Fatima Sahla 'yar marigayi Uncle Sulaiman.
Ai dole ma yarinyar nan ta yi karambani. Allah ya jikan Uncle Sulaiman kawai...

Sai yanzu ya tuna yarinyar da kyau. The last time da ya zo garin nan itane ake bashi labarin wai a wata sallar layya Alhaji ya sa anyiwa matansa da Kaka layya kowacce rago ɗai-ɗai. Kawai dan an ɓata mata rai sai ta je ta kira wasu miskinai guda biyar tace su zo Alhaji zai musu kyautan ragon layya. Malamai suka shigo ana tsaka da yanka raguna, suka shiga yiwa Alhaji godiya suna masa kirari. Alhaji ya nemi bahasi Sahla tace ai ita ta kira masa su tunda ya yiwa Allah alkawarin yin sadaka da raguna biyar wannan sallar. Abunka da mai sarauta baya son girmansa ya faɗi a gaban mutane sai kawai ya yarda da haka. Aka gama yanka rago aka mikawa mutanen da Sahla ta kawo sadaka. Allah dai yasa dama akwai Sa da Alhajin ke son yankawa wanda za a rabawa mabukata.
Bayan sun tafi da raguna Alhaji ya tambayeta dalilin wannan karya tace wai Kaka ce tace bana ba zata ba ta naman sallah ba, su kuma sauran matan kowacce da laifin da ta mata shiyasa ta ce bana babu wacce za ta samu naman layya. Maimakon Alhaji yai faɗa kawai sai yayi dariya yace shi kenan kuwa kowa zai karɓi ladan sadakar da aka yi ranan gobe kiyama. Da matan gidan suka ji labarin abinda Sahla ta aikata sai da su ka ji kamar su daɓawa Sahla wuka a ciki ta mutu kawai kowa ya huta. Amma Alhaji ya hana a daketa, yai Allah ya isa wa duk wanda ya daki Sahla akan maganar ragon layya.

Cikin naman Sa da aka yanka aka yankawa kowacce mata kasonta sauran Alhaji yai sadaka da su kamar yadda ya saba.
Ita kuwa Sahla da Kaka ta isheta da mita sai ta tattara kayanta ta wuce gidan Kawunta sai bayan Sallah da sati biyu ta dawo gida.

Gaskiya the girl is  incredible ya faɗa a ransa yana daɗa murmusawa.

***

Allah Sarki! Allah Sarki!

A falon Anty Rafee'ah aka killace Amare sai kuka suke kamar wanda aka musu mutuwa. Anty Firdausi kam da warin takalmi ɗaya ta bar wajen taro. Ana ta basu hakuri. Masu Allah ya isa na yi. Ni dai ina gefe ina murmushi. Sai tambaya ake garin yaya Awaki suka shigo gidan ba tareda an sani ba. Nan Adda Sabuwa take faɗin ai har wajen da ake girki Awakan suka shigo. Sai da suka saka aka yi ɓarin miya da kuma kullin masa da aka ajiye na gobe da safe.

"Wallahi ana wannan hayya-hayya ɗin nema. Wasu mata suka shiga store suka sace daron soyayyen nama"

Anty Rafee'ah ta fusata " na shiga uku. Adda Sabuwa ba cewa nayi da an karasa suyan naman nan a kai sashen Mommyn Affan a ɓoye ba. Ba saboda haka ta baki key ba"

"Anty Amarya cewa na yi mu karisa suyan sai a haɗa a kai duka lokaci guda. To muna faman koran Akuyoyi
Wasu sheɗanun mata marasa imanin suka kwashe daron nama biyu"

"Innalillahi. Wannan wani irin abu ne. Allah ya tona asirin wanda ya aikata wannan abu"

Gaba ɗaya falon aka amsa da Amin. Ni kuma a zuciyata na ce ba Amin ba. Sai dai ban gama sauke numfashin Amin ɗina ba Abbas ɗin Ummi ya shigo falon yana kwala sunana.

"Kai kuma miye zaka shigo cikin mutane kana ihu"

"Anty Amarya Sahla ce fa ta shigo da Awakan nan. Yanzu Almajiran da aka kama suke gayawa yaya Mustafah"

Ai kafin ya karisa maganar Anty Amarya ta yo kaina tai min wani damka tareda kifa min wani mari.

Ni: "Allah, Wallahi"

Anty Amarya: "Yi mana shiru"

Anty Firdausi: "Allah ya isanmu Sahla"

Anty Aminah: "Sahla wai mi muka miki ne da zaki mana wannan zalincin?"

Anty Karima: "tashen balaga mana"

Adda Sabuwa: " Ai Sahala farar kafa ce da ita. Kun tuna abinda tayi sallar layyar bariya"

Ban iya tanka musu ba har aka tisa keyata wajen gate inda su yaya Mustafah suke tsare da Almajiran nan.

Ina zuwa aka sake haɗa mini kyawawan maruka guda uku. "Sahla ke wacce irin sheɗaniya ce kam. Kin san irin asaran da aka yi kuwa? kin san mutane nawa suka ji ciwo a dalilinki. Kin san wayoyi nawa aka sace a dalilinki.

"Oya fara tsallen kwaɗo dan ubanki"

Duk da kukan da na ke bai hana ni amsa masa ba. "Ubana Sulaiman? ko Ubana Kabiru?"

"Ke!" Ya kaimin duka na kauce ina shirin guduwa Abbas ɗin Ummi da Abbas ɗin Mama suka kamo ni.

Dana fara tsallen kwaɗon nan na ga ba halin guduwa sai kawai na faɗi yaraf na fara birgima ni a dole Aljanu.

Ina ji yaya Yusuf yana faɗin wai aje a ciro bulali wai yau sai na lahira sun fini jin daɗi. Da na ji batun bulala sai na mike na cigaba da yin tsallen kwaɗon. Yaya Yusuf mugu ne na karshe, gara Yaya Mustafah sau dubu a kansa. Duk cikin gidan shine discipline master. Idan ya kama yaro jibgarsa yake kamar babu gobe.

Tuni Yaya Mustafa ya bar wajen saboda raka wasu abokansa da zai yi. Ina cikin tsallen kwaɗon sai haki nake kamar na yi gudun mutuwa. Tun ina ganin hasken fitilun da suka haska farfajiyan gidan har na koma ganin duhu, har ma na rasa inda na ke, na dai ji kamar a sama na ke tafiya, kamar tafiya nake akan iska.
Kila Babana ne ya zo ɗaukana. "Sahla ki zo mu tafi, tunda ba a  sonki a wannan duniya"

"Baba" na furta a hankali sannan idon ya sake rufewa gaba ɗaya...


Complete book is available on Okadabooks and Arewabooks or DM 08137311900

#vote
#comment
#follow

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now