cire kunya

226 8 0
                                    

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

011...cire kunya...

Soyayya akwai daɗi. Ka so mutum sannan shima ya soka babu abinda ya kai wannan saka nitsuwa da farin ciki. Musamman idan wanda kake so ɗin ɗan'uwanka ne na jini wanda kake ganin duk rintsi zaku kasance tare.
Akwai daɗi ace bayan shekara ɗaya kuna soyayya ta waya zaku
sake haɗuwa da juna. Akwai farin ciki sosai.

Yau su Affan zasu shigo gari. Lokacin rasuwa basu samu sun zo ba sai yanzu. Ga shi wannan karan da su za ayi Azumi har ayi sallah domin sai bayan sallah zasu tafi.

Wannan shekaran Anty Rafee'ah ce da Anty Maryam autar Kaka zasu je Umurah.
Har yanzu Kaka bata huce ba da hukuncin da 'ya'yanta suka yanke mata. Alhaji da Abba sun ce ba zasu biya mata kujerar Makkah ba saboda ciwon kafarta. Kwanakin baya kafar ya sata a gaba sai da aka bata walking stick ta dinga amfani da shi. Ni yanzu ma neman sace walking stick ɗin nan nake, dan da na ɗan yi wani abu kaɗan sai dai na ji sanda a bayana .

Da Allah Annabi Kaka ta roke su akan su bari ta je Makkah bana ko Allah zai sa ta cika a can irin mutuwar Asabe amma sun ki.
Fushi take sosai da su dan har cewa tayi zata kai kararsu wajen Sarki amma ko ajikinsu. Sun tsaya akan babu inda za ta je. Saboda su kwantar mata da hankali ne ma suka biyawa autarsu Maryam kujera dan dama bata taɓa zuwa ba. Duk da hakan Kaka ba ta hakura ba.

Kaka ta zamo kamar mai Aljanu. Abu ɗaya biyu sai ta kawo zancen yanzu ace ta mutu a kasa mai tsarki mana, ai shikenan ta samu tikitin Aljannah. Ba za a tambayeta hakkin kishiyarta Sadiye ba. Tun ina mata bayani akan gafara da rahamar Allah tana iya samun mutum a duk inda yake har na zo na daina. Inaga tsufa ne ya fara taɓata. Kar na biye mata nima ta shafa mun. Yaushe na gama fama da nawa matsalolin. Yanzu ko me na taɓata sai an samu matsala.

Ranan da za ayi masan sadaka matan gidan basa nan aka bar mana ni da sauran 'yanmatan gidanmu. Hmm muka yi kullin masa taki tashi. Ni mai dabara na zuba ruwa a katon tukunyar da ake shinkafar sadaka a ciki na saka bokitin kullin a ciki dan ruwan zafin ya turarashi ya tashi.

Abunka da nayi sabuwar babbar waya. Na tsaya ina chatting a whatsapp ashe ruwan cikin tukunyar ya kone har tukunyar ta fara cin kasan roban shi kuma kulli ya fara dahuwa.
Lokacin dana buɗe tukunya na ga kullin kamar ya fara zama kunu. Hmm ranan dai sadakar buredi aka yi. Sauran kullin da bai lalace ba aka yi sinasir da shi.

*

Yauma dai Allah-Allah nake a raina kar a samu matsala a abinda na shiryawa Affan. Da ke ina taya Anty Rafee'ah aikin donut idan aka kawo mata aikin biki ni ma na iya kwaɓa donut.
Tun jiya na siyo flour da kayan haɗi na ɓoye a cikin akwatina.

Abinka da rashin amana hatta mangyaɗa sai da na siya da kaina. Couscous zan dafa masa da miyar kifi. Bayan na sha faɗa a hannun Alhaji akan Coustaliye dana dafa ranan na samu Anty Rafee'ah nace ta koya min yadda ake dafa couscous. Nifa ranan ɗinma zafin kan registration ne da kuma gajiya. Ɗanbanten wanda ya min registration ɗin ya kama ya min register da sunan Salah Sulayman maimakon Sahla Sulayman. Ɗan iska
Ya sakani asaran dubu biyu kuɗin green card da na siya aka gyara min sunan.

Dake matan gidan sun haɗe baki sun zama 'yan damfara, ni da Kaka ma muka maida ɗaya ɗakinta mini kitchen ɗinmu. Idan abinci bai ishemu ba na kunna stove na dafa mana indomie da kwai mu ci. Wani lokacin ma idan aka yi tuwo da dare bai mana ba sai na ɗan soya mana wainar flour mu ci da shayi.

Na buɗe fridge na fito da ice fish dana siyo jiya.

"Wai ni Sahala wa za ki yiwa girki ne? Saurayinki ne zai zo?"

"Eh. Saurayina ne"

"Yusufa?"

"Waye kuma Yusufa. Allah ya kiyaye na yi soyayya da Yaya Yusuf"

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now