Sahla Dear!

277 10 0
                                    

002...Sahla Dear...

Gidanmu yana da ɓangarori dayawa. Gini ne na da amma Alhaji ya gyara, an zamanantar da shi. Matan Alhaji kowacce da ɓangarenta, falo, kitchen da ɗakuna biyu, store da kuma banɗaki.
Ita Mama akwai son girma da shegen son nuna kai. Lokacin da aka aurota Kaka tana yawan mata gori da tsohuwar matar Alhaji wato Gimbiya Maryam. Wannan yasa ta ki jinin ka haɗata da duk abinda ya shafi Maryam ɗin, 'ya'yanta ma da suke kasar waje ko sun zo gidan ba ta yi da su. To ba ma zuwan su ke ba. Dan ni dai hana karya tun dana taso sau biyu na taɓa saka Anty Hasina da Anty Sayyidah a ido. Dan ko bikin Anty Hasina da aka yi shekara biyu da suka wuce a fadar Maimartaba akayi komai. Shi kuma Uncle Faruqu a hotunan biki kawai na ganshi.
To kamar yadda na ke baku labari. Mama dai kullum fitinarta mi za ta saka a ɗakinta da zai fi na sauran kishiyoyinta. In kuwa sutura ce ko bashi sai ta ciwo ta siya dan kawai ta saka ta fi sauran matan.

Ummi kuma ga kwaɗayi, roko da kuma rowa. Har yau tana zaran abinci a store ɗinta ta siyar ta kashe kuɗin. Kullum cikin rikici ake da ita akan kayan abincinta baya taɓa kaiwa karshen wata. Bayan waɗannan halayen indai wajen gulma ne to sai dai a shafa mata Fatiha. Radiyo ce mai jini. Wallahi duk gulmar Hajiya Kaka ta sallame mata. Tana da kazanta gaskiya dan da zaka duba karkashin gadonta za ka iya samun ruɓaɓɓen Albasa da aka ɓoye tun shekara biyu da suka wuce. Bara da ta haihu ɗan bai zo da rai ba wata Babarta ta zo yi mata wanka ta sharo mushen kyankyasai sun fi hamsin a kasan gado, inaga maganin sauron da ta ke sawa ne ya ke kashe su. Ga su ledar taliya su macaroni su ledar maggi da ta ɓoye ɓeraye sun ci na ci sun bar na bari. Gaskiya ranan girkinta anfi jin jiki. Ba zata taɓa girki tsakani da Allah ba, duk irin cefanen da za a bata ba zata taɓa amfani da shi duka ba. Gara Mama takan yi girki mai kyau sai dai ba zaku koshi ba, amma yaranta zasu koshi. Ita Ummi har a yaranta mugunta take musu. Duk wannan halayen nata fa tafi kowa zuwa Islamiyya a cikin matan Alhaji. Sai ka rasa mima ta ke koyowa idan taje chan dan sama da shekaru goma tana zuwa Islamiyya amma babu wani abu daya gyaru cikin halayenta. Da lokacin Azumi ma ita ce gaba-gaba wajen zuwa sallar taraweeh da tahajjud.

Umma Bilki. Hmm. Umma Bilki. Allah ya yafemu dai kawai amma ni kam gara Ummi sau dubu akan Umma Bilki. Ita Ummi duk halayenta a fili su ke sai dai kai ka sha maganin zama da ita, amma Umma Bilki hawainiya ce, yau kalarta fari gobe ja jibi kuma shuɗi. Munafuka ce mai lasisi. Tsabar iya munafurcinta har haɗa Alhaji take da Hajiya Kaka faɗa. Tsaf za ta shirya tuggu mai wuyar warwarewa. Kafin ka kamo bakin zaren ta riga ta cire hannunta a ciki. In dai za a yi faɗa biyu uku tsakanin Mama da Ummi to idan ka bi silsilan maganan za ka ga Umma Bilki ce ta haɗa su. Shiyasa sam bana shiga safgarta. Tun sau ɗaya da ta haɗa min wani sharri a wajen Alhaji na ja baya da ita. Gashi idan ka zo gidan ta maka wani tarba mai kyau sai ka ɗauka tafi kowa kirki amma...a bar kaza a gashinta.

Anty Amarya dai babu ruwanta da kowa. Bata shiga sabgar da ba nata ba. Duk da bata taɓa haihuwa ba bata irin nuna son yaran nan kamar yadda masu son haihuwa ke yi. Idan yaro ya shiga sashinta ya mata shirme zane yaro take sosai. Tana da tsabta har dana Allah ya isa. Idan ka shiga falonta ka ɗan jima. Kana fita za ta fara mopping. Duk wacce za ta kawo saurayinta na musamman to sashen Anty Amarya za ta sauke shi dan kuwa ba za ka ji kunya ba.

Ina ta muku gulman matan Alhaji ko. Idan ban muku gulman ba ba zaku gane abubuwan da zasu biyo baya ba. Ni da yake 'yar gaban goshin Hajiya Kaka ce duk wani abinda yake gudana a gidan ina sani. Dan idan aka je aka dawo duk a ɗakinta ake jibgewa.
Hajiya Kaka tana son Anty Amarya amma kullum korafinta wai bata girmamata yadda ya kamata. Wai itama halinsu ɗaya da Gimbiya Maryam wato jiji da kai.
Amma sauran matan 'yan ayi daɗi ayi faɗa ne.

***

Yau ina kwance a cikin ɗaki ina karanta wani littafin hausa mai suna 'Maraici' na ji muryan Alhaji yana sallama. Kaka ta shiga wanka dan haka ni kaɗai ne a ɗakin.
Na yi saurin jefar da littafin na jawo bargo na rufe fiskata amma ban gama rufuwa ba na jiyo muryansa a cikin ɗakin yana faɗin "Sahla taso nan"

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now