hujin ɗuwawu

243 9 0
                                    

008...hujin ɗuwawu...

Bacci mai daɗi nake aka ɗaka min duka na tashi a gigice. Zuhriyya ce tsaye a kaina.

"Iskancin banza, wa kika fi a gidan nan da zaki baje kafa ki kwanta bayan ga can aiki na jiranmu a kitchen. To Wallahi ki fito ko in haɗa ki da Yaya Yusuf"

"To kuma sai ki ɗake ni?"

"An ɗaka ɗin. Mtsw" ta wani juya ta fita

Ohhhhhhh. Ba dama mutum ya ɗan kwanta sai ace aiki-aiki.Allah dai ya dawo min da Kaka lafiya. Tunda ta dawo daga Makkah ciwon kafa ya sakata gaba. Yanzu haka satinsu ɗaya kenan da Abba ya zo ya ɗauketa zuwa Egypt.

Aikin gidan nan kuwa yanzu baya karewa, musamman yau Jumma'a da ake abincin sadaka.

Tashi nayi ina kunkuni, na ɗauki ɗankwali na ɗaura dan baka isa ka fita nan da nan babu ɗankwali ba yanzu zaka sha rankwashi a wajen Yaya Yusuf.
Doguwar riga na saka na atamfa. Atamfar ma ta ci na kyautar da ita amma na kasa rabuwa da ita. Duk ta koɗe.
Atamfar 'yar amana ce. Da na dawo daga makaranta ita ke saman akwati dan haka sai na ɗauka na saka, ga shi ɗinkin simple gown ne bata kama ni ba kuma bata yi buje dayawa ba, ina sakewa sosai ciki idan na saka.

"Sahlaaaa" ta sake kwala min kira

"Na'am"

Mtsw! Kai Zuhriyya akwai naci. Ni wallahi ban so aka haɗani aiki da ita ba. Gashi komai sai ta bar min ni zan yi.

Na ɗauki wayata na jawo kofar ɗakin na rufe. Na nufi sashin Umma Bilki dan ita ke da girki.

Ina zuwa na samu Zuhriyya tana zaune gaban kayan miyan da za a gyara tana danna waya.
Dama na sani ba zata fara komai ba sai na zo. Duk rashin son aikina Zuhriyya ta ninkani a son jiki.

Ina zuwa na ɗan zunguri keyarta kaɗan, sai ga wayarta ta faɗa cikin kayan miya.
Tasowa tayi ta shako ni.

"Shegiya kika jefa min waya cikin ruwa. Wallahi ba zan yarda ba"

"To nina ce ki tsaya danna waya. Ba aiki aka ce muyi ba"

"Dama Sahla kin rena ni a gidan nan, to yau sai na koya miki hankali"
Muka fara faɗa kicici-kicici.
Ganin ta fara galabaitar dani sai na gaftara mata cizo a wuyanta. Ta saka kara. Na samu na turata da karfi sai gata cikin bahon kayanmiya.

"Wayyooooo Ummina, Wayyo, Wayyo niiii"

Maimakon ta tashi sai ta zauna a cikin bahon tana kuka, sai wayyo take kamar wacce aka kashewa iyaye.

Na ɗauka ko ɗuwawuntane ya makale tunda roban ba wani faɗi yake da shi sosai ba.
Na kama hannunta na jawota da karfi. Aikuwa sai ga jini. Na shiga uku akan wukan dake cikin kayan miyan ta faɗi.
Na saka hannu aka na kwala ihu ina kiran Umma Bilki, dama duk sunan da ya zo min.

Yaya Yusuf aka kira ya cire wukar. Ya mata first aid sannan suka wuce asibiti dan a mata ɗinki.

Kafin su dawo sai da na kwammaci ban zo duniya ba. Ummi kamma cewa tayi wai kishi nake da Zuhriyya, shiyasa nake son nakasa mata 'ya. wai ina bakin ciki saurayin Zuhriyya manajan banki ne.
To ni ina ruwana da saurayinta. Na ce musu ina neman saurayi ne. Ina tareda Affan ɗina mi zanyi da wani kato wai manajan banki.

Da suka dawo daga Asibiti na kukuta na je gaisheta, tana kwance tayi ruff da ciki daga ita sai shirt da bum short.
Ina cewa Zuhriyya ya jiki Ummi ta hayayyako mini.
"Me kuma kika shigo yi?"

"Ummi Allah ba da sani na bane"

"Sahala fita mana daga ɗaki kafin muma ki mana lahani. Mai farar kafa kawai"

Ban iya magana ba, na zame jikina na fita. Kullum maganar kenan, Sahla mai farar kafa. Na koma ɗaki na zauna a kasa na zabga uban tagumi kamar wata tsohuwar data rasa duka 'ya'yanta. Wato nifa yau idan aka ce babu Kaka a gidan nan ba karamin wahala zan sha ba. Babu mai sona tsakani da Allah.
Ni dai Sahla a komai bani da sa'a. Daga faɗa da 'yar'uwata shikenan sai ga ta da hujin ɗuwawu. Wayyo ni Sahla.

SAHLA a Paris (Hausa novel)Where stories live. Discover now