Teaser

646 24 1
                                    

AHALINA
    (Siblings of different Father's)
(Book two in Aure uku series)
CHUCHUJAY ✍🏽
TEASER0⃣
HONG KONG UNIVERSITY CHINA .
    Ko wanne ɗalibi cikin su yana fama da tashe da Jin kan sa na rawa irin na yan jami'a,
Rayuwa ce wadda bayan ta zakaji idan ka zauna kana tunanin ta kace ina ma ta dawo koda sau ɗaya ne kayi wannan rayuwar ta Care free da freedom,
Su Shida ne a zaune a ajin bayan tashi sun gama tutorial,
Mata biyu sai maza huɗu yan kasar Nigeria dake karatu a kasar ta CHINA ,ko wanne ka kallesa kasan ba wai ɗiyan talaka bane,matan mata ne masu aji haka zalika mazan ,
Dukan desk ɗaya daga cikinsu yayi yace yes"lets bet na saka new range ɗinta in har NAMEER HABIB Ya yarda da game Ɗin nan da kake magana akai SALIS kai Mai kasa idan bai shiga ba cos naga kai kafi kowa zaƙewa akan bazai shiga ba,

Murmushi matashin da aka kira da Salis yayi ya kalli wanda yayi masa maganan yace ,FADIL kenan,ka raina girman kan Nameer fiye da tunanin Mai tunanin ,naji na saka maka sabon apartment ɗin da daddy Ya siya min a garin nan in har NAMEER Ya yarda Ya shiga game Ɗin nan,
Kallan sauran yayi yace ,FAROUK,SALMAN ,AMNA,AMIMA,JAMAIMA a gaban ku akayi ba,be My witness,
Tafi dukkansu suka fara suna shewa banda yarinyar da aka kira da JAMAIMAH wadda ke faman latsa wayarta kamar babu abunda ke faruwa kafun tace "Well i would be the bait indai da NAMEER ne i wont mind ,Y'all be My guest,sannan kunsan anything betting is haram ba?
Amma i wont mind this time,lets commit this little sin cos i find the game interesting."
Shigowar NAMEER yasasu yin shiru baki ɗayansu kafun FADIL Yace"game on ,game on Nameer oya zauna ,cikin yan matan nan ka zab'a marriage game zamuyi and Its just a game bro,Abeg ka duba mun i want to win this amazing Apartment na Salis Abeg."
    Kallan Salis Nameer yayi ganin irin kallan da yake masa wanda dama ba tun yau ba yake shige masa hanci da kudundune wanda ya sani sarai hassada ce kawai yake masa dan haka Ya samu guri Ya zauna yana Mai harɗe kafa yace game on!
Kallan yan matan yayi ɗaya bayan ɗaya Ya ,idanunsa ne Ya sauka kan JAMAIMAH wadda Salis ke da ido akai yace "Well i choose JAMAIMAH RAIS.
Da sauri Salis Ya kallesa yace"maza be careful 'fa,"
Kallansa Nameer yayi yana Mai matsa hannunsa yace "i hope Its not a threat?"
    Murmushi salis yayi yace "Its a warning."

Batare da ya kuma kallansa ba Ya sake kallan Fadil yace "maza i Said game on,muje zuwa mana ,i will marry maimah,"
Wani uban tsalle Fadil Ya buga yace maimah what's your price,
Rolling idanunta tayi tace "1.5,"
Tafi suka fara suna masu faɗin 1.5 million a yayin da NAMEER yayi murmushi Ya ciro wayansa yace mene Account no ɗin ki,
Cikin rashin damuwa ta faɗo masa inda take yayi wiring mata kuɗin ,
Yana shiga tayi gasping tana Mai kallansa tace "For real Nameer ?"
Ɗaga girarsa ɗaya yayi yana Mai kallan Salis ,
Dukan desk Fadil yayi yace "zan wakilceka ,Salman wakilci Maimah,".babu musu Salman wanda shima abun ke masa daɗi Ya wakilci Jamaimah inda a cikin abunda za'a kira shiririta da danne sani ,da kuma uwa uba JAHILTAR menene Aure a addinance suka ɗaura Auren NAMEER HABIB da JAMAIMAH RAIS.
Dukan desk Fadil yayi yace 'END OF THE GAME oya Salis your Apartment key and hey Nameer this marriage doesn't count idan kuma you're not okay kawai kace ka sake ta.
Tashi tsaye Jamaimah tayi tace "As If ,kunyi kuskure ai cos a yanzu na zama matar Nameer kuma babu wanda ya isa ya raba ,not him koda kuwa yana san yin haka,matsowa tayi gaban sa tana Mai shafa fuskarsa tace I've been carving for you,and idan kaga dama kayi zagayen duniya na shekarun da kaga dama ,amma kasan abu ɗaya a duk tafiyar rayuwarka ,kana da mata PRINCESS JAMAIMAH RAIS ɗiyar SARKI RAIS sarkin babbar masarautar Cikin DILAH dake garin CAMEROON,kasar dake cikin central Africa incase ka manta.
Murmushi tayi tana Mai saka glasses ɗinta ta fita ta barsu da babban mamaki cos Babu wanda yasan Asalinta a zamansu na shekara Biyu tare haka zalika itace wadda ta kawo wannan game Mai suna MARRIAGE BET sannan itace Mai bakin faɗa masu cewa Betting is haram ,
Shine MENENE KUDIRINTA?

********************************************
    Cike da izza irin na yan matan nan masu ji da Kansu take takunta ciki filin da aka tanada na SHOW YOUR DESIGN TALENT ,
bayan ko wacce model dake ƙarƙashinta ta fita itama ta tako cikin nata takun tana Mai jin wani irin daɗi da farin cikin samun wannan nassara tata ta Kai team ɗinta zuwa babban stage na ZUMMA dake cikin garin Ghana,wanda take da yaƙinin Its a win win,
Bayan komawarsu cikin dressing room ta kalli ko wacce model ɗin tana Mai sake musu jinjina da basu ƙarfin gwiwa,
Kana ta kare magananta da faɗin "Dinner @8 and Its on me,"
Ihun murna suka fara suna masu praising nata,
Fita tayi domin zuwa management,gwaren da tayi da hard chest na mutum ne yasata saurin ja da baya tana Mai faɗin" im Sorry"
Ɗagowa tayi dan san ganin wanda ya bige ,
"Sorry ta sake furtawa amma kallanta kawai guy ɗin yake ,"
Ta matsa 'dan ta wuce sa shima Ya matsa ɗin suka sake haduwa guri ɗaya,left ta sake matsawa shima Ya matsa ɗin,
Yar ƙaramar dariyar frustration tayi tana Mai kare masa kallo,
Handsome guy ne wanda ba sai An faɗa maka ba cos a kallo ɗaya zaka gane,
Wuyansa ɗauke yake da chain na ice Mai ɗauke da cross yayin da kunnensa ke ɗauke da ɗan kunne guri ɗaya wanda baza tace ba magnet ne ko bulawa akayi,
Gashin kansa  ba Mai yalwa be amma ya kwantu irin na African ɗin nan wanda ke masifar ɗaukar ido,
Abu guda ɗaya ta sani wanda Shine ba musulmi bane 'dan shigarsa masulmi bazai yi ba,
Ganin yarda yake mata Kallan kurilla ne yasata faɗin"wani abu na damunka akai ko?
The fuck is wrong With you?
Hannunta tasa ta tura sa tace"Get out from My sight Man.
Rabawa tayi ta gefensa ta wuce da takunta Mai ɗaukar hankali,
Cigaba yayi da kallanta kafun yafurta NADIYA BILAL"
Murmushi yayi yana Mai jinjina kansa kafun Ya juya yana Mai tunani kala kala aransa cos jikinsa Ya gama bashi itaɗin tasa ce and zasu kasance tare.

*******************************************

       YOUNG SHEIK ABDALLAH HAFIZ,
Kyakyawar buduwar dake zaune tana wanke wanke ta faɗa a hankali a yayin a take jin tafsir ɗinsa cikin ƙaramar rediyon kakarta da taci gado,
Ball ɗin da akayi da rediyo Wanda yasata saurin ɗagowa 'dan ganin mai aika aikan duk da tasan wanene,
Cike da balai matar da tayi ball ɗin tace"shegiya gayyar bakajin magana ko?"
Baki da aiki sai sauraran wanda bai san dake ba ,ke bani tunanin ma har ki mutu ba zaki taka inda ya taka ba mistiyaciya gayyar tsiya.
"Wai nikam Laure meke damuwarki kike ta hayagaga kamar wata kura? tun daga bakin layi ana jinki ,haba 'dan Allah ya,sai kace wata ƙaramar yarinya,kedai a rayuwa baki da abiyar faɗa bayan Hafsatu menene wai kam,".
Cike da balai ta kalli mijin nata tace "Malam Balarabe ka ɗaga mun kafa fa kar ka nemi ka cuna mun baki kan wanga ɗiya dan tun yarinta nake wahalar ta sannan dole ne idan naga tana abunda bazai fisheta ba nayi magana,ina dalili yarinya tabi ta ɗorawa kanta ƙaddarar da bazata haifa Mata Ɗa mai ido ba ,bata da Aiki sai sauraro ko Kallan malamin nan Abdallah Hafiz wanda ni nasan kallan banza ma bata ishe sa ba,
Ka kallemu dai yadda talauci yayi mana katutu tunda ka dage sai ka Auri uwarta Laraba Ai gamu nan dai muna tacin ubanmu ta mutu ta barmu da jidali,idan zaki gama ki ɗauka mun tallan dawo gashi Chan na daka ki tashi ki fita chan kasuwar bakin hanya ta ɗari biyar ce ta ƙare kuma.

Kaɗa kai malam balarabe yayi Ya gifta Ya wuce su inda Hafsat ta miƙe 'dan ɗauko rediyo ɗinta,
Tsaki laure tayi tace "A banza man kare tunda dai baya tuya".

********
To masoyana abun Alfahari na gafa teaser nan na AHALINA littafi na biyun AURE UKU,
Sannan zaya fara zuwa muku cikin watan nan,kilan on 10th ranan birthday ɗin ko kuma kafun nan,
Koyaya dai Its DECEMBER and its my favourite month Kuyi expecting ɗina ko wanne lokaci ,i just hope zai maku daɗi sannan zaku karbesa kamar yarda kuka karbi AURE UKU Its gon be lit and yea dont ask me about yan uku zasu fito cikin littafin amma 'fa soyayya bassu cos sunyi yara😂😂who knows nasu labarin yazo,ban dai yi Alƙawari ba.
Ina mutuƙar ji daku,

Join My whatsapp channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Sannan kuyi joining update group!
https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

Chuchujay ✍🏽

AHALINA(book 2 in Aure uku series)✔Where stories live. Discover now