GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa 1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal 🥱ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Zan baku wannan garabasar ,masu cemun sati yayi kaɗa ga shi kanan sai 1st February 2024
maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm meAHALINA.
(Siblings of different fathers)
Book two 'in Aure uku series.
By
Chuchujay ✍🏽
(Amina jamil Adam)🥰
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Episode 4⃣1⃣➡4⃣2⃣
Zaune Nameer yake a office ɗin Nadiya hankali sa yayi mutuƙar tafiya nesa,tunani kala kala yake kan Jamaimah,yakamata ace a iya maganganun da Ya zauna Ya faɗa mata ta zama Mai fahimta da hangen nesa,a iya tunanin sa duk wani Mai hankali idan ka zauna kayi masa bayani kamar yarda yayi mata zai fahimta yasan menene dai dai ,amma ina kamar Ya sake tura mata rashin fahimta akanta.
Yana cikin wannan tunanin Nadiya ta shigo daga meeting ɗin da sukayi,
Zama tayi tana Mai faɗin"wash komai is stressing a rayuwarnan ,amma Ya mutum zaiyyi idan yana neman cigaba".
Ganin baice mata komai bane yasa ta kallesa da kyau tace "Hamma?,amma still shiru,ajiyar zuciya tayi da ta fahimci Ya tafi tunani ne,hannun ta saka tayi snapping a fuskarsa wanda hakan Ya sakashi dawowa daga duniyar tunanin da Ya tafi yace"Nadiya kin dawo kenan."
Cike da kulawa tace "Hammanmu 'dan Allah ka daina wannan tunanin da kake yawan yi kar yazo Ya zamar Maka damuwa,kar ka manta fa,komenene Allah Ya ɗorawa mutum to akwai dalili ,sannan shi mumini baya tab'a wuce ƙadarar sa kuma kasan ba'a jarabtar kowa sai mumini wanda nasan insha Allahu kai Mai cin wannan jarabawar da Allah Ya ɗorawa maka ne,'dan Allah kabar wannan tunanin,kar ka manta AHALINKA na tare da kai a duk wani step na rayuwa da zaka taka.
Sosa gefan fuskarsa yayi yace"amma dai Nadiya Kema kinsan babban jigon AHALINA bata tare dani ko?"
Mami bata amsa wayana ,yanzu maganar da nake sai da na biya gida Amma ko inda Nake mami bata kalla ba ,ko gaisuwana bata amsa ba duk yarda Papa yayi da ita,last naje Asibiti na sameta amma Mami magana take mun kamar mara lafiyar da yazo ganin likita ,wai sai nayi booking Appointment .
Ƙaramar dariya Nadiya tasaka wanda Ya sa Nameer kallanta yace"mene na dariya"?
Hannunsa ta kamo tace "kawai mami ce ke bani dariya,yanzu fa Ya kamata ace kasan wacece mami,to wallahi tafi kowa zama tare da kai kawai dai ranta ne Ya baci dangane da abunda yafaru,kasa kanka a wannan matsayin mana,kana matsayin iyaye ɗanka yayi irin abunda kayi kasan dole zakaji babu daɗi and you will feel less,amma Mami kam ko yau da asuba da naje gaisheta najita tana Addu'an Allah Ya fitar da kai duk wani hali da kake mara kyau yasa kayi overcoming,amma man ina shiga ta bari".
Ɗan shiru yayi kana yace "Nadiya ki yarda what i did was not intentionally sannan banyi ba domin Mami taji ƙanƙanta,wallahi kuskurene wanda baya wuce ranarsa"
Kaɗa masa kai tayi tace na sani Hamma and insha Allahu kuskuren nan zamu mayar dashi abunda kowa zaiyyi alfahari dashi.
Gyara zamansa yayi yace"banga Alama ba domin Jamaima ta wuce dukkan wani tunani ki,rashin fahimtarta da tunaninta zan ce maki yafi na jahilin da bai zauna a aji ba baki ɗaya "
Ɗan shiru Nadiya tayi kafin tace "inaji a jikina komai zaizo Ya wuce kamar bai faru ba time ne kawai ".
Ɗan karamun murmushi yayi yace "Allah Ya nuna mun time ɗinnan na ƙosa cos im exhausted already,"
Kafun ta Sake wani magana telephone ɗinta yayi ƙara wanda tasan sakatariyar tace,dagawa tayi ta Kara a kunne inda take sanar da ita tana da baƙo,
Sanin wanene baƙon yasaka ta cewa Ya shigo,
Da sallama a bakinsa Ya shigo,haka nan ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki da ta tuna fa a yanzu shi ɗin musulmine kamar ita sannan yasan ƙaidoji da dama na musulunci wanda cikin sa harda idan kaje guri kayi sallama,
Juyawa Nameer yayi lokacin da Ya kallo fuskarta yaga wani irin annuri da farin ciki da take kallan Mai sallamar dan haka Ya juya 'dan ganin wanda Ya saka Nadiya wannan Nishaɗin.
Ganin Nameer Ya saka AHMED(Evans )saita kansa yana Mai nutsuwa domin ko ba'a faɗa masa ba yasan wannan ne brother ɗin ta Nameer cos kamar su ma kawai ta baka amsa ba sai anyi magana ba,
Ƙarasowa yayi cike da girmamawa ya mika masa hannu yana Mai faɗin Sallamu alaikum.
Kallan hannun Nameer yayi kana ya kalli fuskarsa da kyau yana san sanin inda yasansa,karban hannun yayi yace"Sallamu alaikum".
Ganin yarda Ya tsaya Nervously ne Ya saka Nadiya saka ƙaramar dariya tace "ka zauna mana ,ko ganin future brother in law ɗinka Ya saka ka shiga kiɗima ne".
Murmushi yayi Ya jawo kujerar dake kallan Nameer ya zauna yace"ba dole ba cos yarda nake tunanin zanga Brothern ɗin mu Ya fi haka and i was not thinking zamu haɗu a nan"
Gyara zama Nameer yayi yace "kamar nasanka ko kuma nace nasan Mai kama da kai ,amma wanda nake mistaking ɗinka dashi bama musulmi bane ,and He's a ghanian Actor which nasan babu abunda zai haɗasa da kanwata Nadiya nan,and idan fahimta takai inda nake tunani kai da ita ɗin kuna soyayya ne,so mind idan nasan more about you?
Ya karasa maganar da irin tone ɗin nan na babban yaya.
Kallanta Ahmed(Evans)yayi alamun Mai zaice,ɗaga kafaɗarta tayi tace "kajisa ai ka amsa masa tambayarsa ,he's My elser brother Nameer and yana san sanin wanene kai wanda na tabbata ba sai nayi masa bayani ba daga bakinka zaifi daɗi cos in baka manta ba nima nayi undergoing wannan investigation ɗin but trust me nawa kawai magana ne"
Ƙaramar dariya yayi da Ya fahimci abunda take nufi kafun Ya maida kallansa kan Nameer wanda Ya zuba masa ido yana Mai san tabbatar da ba Evans bane cos duk da a screen Ya saba ganinsa amma yawan kallasa a screen ɗin baya tunanin idan Ya gansa a zahiri zaiyyi masa wahalar ganewa,amma abu guda ɗaya Ya sani wanda shine Evans bazai saka jallabiya da hula ba,koda kuwa zai saka jallabiya bazai saka hula irin ta ustazai din nan da mutane Kema laƙani da"tashi kafiya naci"ba,sannan babbar maganar ma kuma itace babu wata alaka da zata shiga tsakaninsa da Nadiya.
Cike da rashin sakewa Ahmed(Evans )yace "sunana Ahmed Hans wanda ada nake Evans sannan Bakayi kuskure wajen gane wanene ni ba nine Evans Hans ghanian movie Actor and a model,i was a Christian amma a yanzu ni musulmine ,sannan ina san ƙanwarka ne tsakanina da Allah san kuma da nake mata na Aure ne bana wasa ba cos maganar da nake maka a yanzu mahaifiyata tana garin nan tana san ganawa da iyayen Nadiya domin suyi magana ".
Kallan Nameer Nadiya tayi tana kallan yarda Ya shiga Cikin shock da mamaki na confession ɗin Ahmed,
Yar karamar dariya yayi yace "you're not joking ko?,wait idan kai musulmine yanzu taya akayi kazama,Kana so kace mun saboda Nadiya?"
Kodai musuluncin ka wata mafakace ta yaudarar Nadiya?
Bana fahimta ka fahimtar dani,
Kallansa Ahmed yayi cike da gaskiyarsa yace "wallahi yayan mu ban karbi musuluncin ba dan na yaudari Nadiya ba,ina mata soyayyar da babu yaudara acikin ta,na yarda itace mukulllin shiga musulunci na amma dana shiga na fahimci nanne wajen zamana inda zan samu kwanciyar hankali Mai daurewa wanda nake fata,dama kawai nake nema na samu na kula da Nadiya fiye da yarda zan kula da kaina. "
Shiru Nameer yayi yana kallan Ahmed da wata irin fuska Mai tsoratar da mutum idan yana gaban sirikai,
Ajiyar zuciya Nameer yayi yace"addinin mu bai hana mu aurawa ƴarmu wanda Ya karbi shahada ba abun dadine sannan abun alfahari ne gare mu ace dan Nadiya ce sanadin musuluntar ka sannan magana tana ga manyamu amma kafin nan sai ka nemi soyayyar ita Nadiyar"
Kafun kowannen su yace wani abu Nadiya yace "Ai hamma yama samu".
Buɗe baki Nameer yayi kana Ya saka dariya yana Mai miƙawa Ahmed (Evans )hannu yace "shikenan ta koreni ,Allah Ya bada sa'a abokina dan na fahimci ƙanwata nan ta gama faɗawa,"
Gaisawa sukayi inda Ahmed ke faman washe masa haƙora ,sallama yayi musu yana Mai faɗin "sai kinzo Nadiya da yarinyar da kikayi magana ".
********************
Bayan komawar Nadiya gida da dare bayan sun gama dinner tabi mami dakinta danyi mata maganar Evans,
Kallanta Mami tayi lokacin da tayi sallama a ɗakinta,
Cigaba tayi da cire agogan hannunta tana Mai fadin"idan kinsan maganar Nameer ce ta kawo ki spare me,
Shigowa tayi ciki ta zauna tana Mai matsa mata hannunta Kana tace"Mamina yau ba maganar hamma bace maganan tawace sannan nasan zakiyi farin ciki sosai da ita,"Ɗan kallanta mami tayi tace "inaji sannan kiyi magana softly kar ki tashi mahmood yanzu yayi bacci"
Kallansa Nadiya tayi ganin yarda yayi bul bul abunsa tace"yaran Mami sai wani fresh yake yi abunsa ."
Cikin rage murya tace"Mami kinsan yanzu im 29 ba?"
Sannan nayi achieving komai da yakamata mutum a shekaruna yayi ko?
Kallanta da kyau Mami tayi tana Mai san fahimtar inda maganar Nadiya kesan tafiya kafin tace"kin samu mijin aure kenan,to kice Ya turo".
Yar karamar dariya Nadiya tayi cike da jin kunya tace "Kai Mami "
"Ehen ai idan kaji budurwar yarinyan ka ta fara magana haka to Aure take so ,yanzu haka nima tawa budurwar dake gabana Aure take so,juyowa Mami tayi tana Mai faɗaɗa fara'ar da Rabon da tayi ta kwana biyu ,daga mata gira ɗaya tayi tace "uhum ina sauraranki wanene lucky guy din".
Ƙasa tayi da idanunta tace "Mami na ta kaina you got me,sunansa Ahmed and ghanian ne mahaifiyarsa kuma yar Nageria ce amma inyamura ce".
Ɗan shiru mami tayi na wani lokaci cikin fuskar da zakace abun Ya daki mutum tace"Mai ya faru da dukkan Hausawa da fulanin Nigerian da sai Kinje har ghana kin zaƙulo mana ɗan ghana irin inyamurai ni Umaimah ,"
Cije lebe Nadiya tayi tace "Ai mami bama wannan ba ,he was a Christian amma Ya musulunta sannan yanzu haka suna nan Nigeria da mahaifiyarsa akan tana san ganin iyayena"
Gyara zama Mami tayi tace "interesting,yanzu maganar da kuke yazo da Mamansa nan dan taga iyayenki ,ita ma musulmarce sannan a danginsu mace ke zuwa ganawa da iyayan mace ,bani nasha".
Sosa ƙeyarta tayi tace "ita ba musulma bace 'infact dukkan iyayensa ma babu musulmai shi kaɗai ne musulmi shima kuma haɗuwa dani Ya saka Ya musulunta".
"Uhum ,kice saboda ke Ya musulunta,abun gwanin dadi na kwana biyu banji labari Mai ban dariya da daɗin wannan ba,na kasa yarda Nadiyata ta faɗa tarkon mayaudara,dama da popcorn munayi munaci cos this is hilarious, "
Ganin da gaske Mami bata ɗauki abun gaske ba Ya saka Nadiya saka serious face tace "mami da gaske nake ba wasa ba Allah,Bana boye miki komai 'dan baki koya mun yi miki boye boye ba shiyasa a wannan karan bazan fara ba,na amince da shi Mami sannan na gamsu da cewa musuluncinsa ba domin Ya yaudareni bane Allah ne Ya kirasa Ya zabesa And Sanin wacece ni yasaka ban tab'a bashi dama ko na nuna masa amincewata da soyayyarsa ba har saida na tabbatar da cewa ni dashi akwai hallarci,
Bugu da ƙari kuma nasan AHALINA ba mutane bane masu duba banbanci na Al'ada muddin kuwa addinin mu abu ɗaya ne dashi kawai nayi amfani wajen zuwa sanar dake kai tsaye ba tare da Naji wani abu ba Mami.
Shiru Mami tayi tana kallan ta Kana tace"daɗina dake akwai iya tsara zance muddin kuwa Kina san abu,Naji dai yanzu gobe idan Papanku Ya dawo tunda bazani asibiti ba zamu zauna mu tattauna akan maganar sannan mu samu Daddy muyi magana dashi bayan haka sai su zo mu gansu nan da kwana biyu nasan dole Papanku bazai taba bada goyan bayansa ba ɗari bisa ɗari muddin baiyyi bincike sosai akansa ba da kuma danginsa".
Rungume ta Nadiya tayi tace "Allah Ya saka maki da gidan Aljanna Mamina uwa ta gari,"
Shafa bayanta mami tayi tace "uhum uchenna "
Dariya suka saka a tare inda Mami ta daɗe tana nazarin wannan baban al'amarin da Nadiya tazo dashi.
Kamar yarda tace sai tayi magana da Papa bayan dawowarsa kuwa ta zauna tana Mai zayyana masa abunda ke a aƙasa ,ɗan jim yayi kafun yace"kuma tace tana san yaran?"
Kaɗa kai mami tayi tace "haka nan tace sannan a idanunta ma na gano hakan ,kawai dai ina jin tsoron Abunda zaije Ya dawo ne wanda Ya shafi banbancin al'ada da kuma addini wanda kaga 'fa yaran nan shi kaɗai ne musulmi a danginsu wanda kuma sanadiyar ita Nadiya ɗin Ya musulunta".
Tabbas yasan maganarta da ƙamshin gaskiya,amma komai a rayuwa idan zaka duba ka duba positive side ɗinsa,
Cikin Hikima ya ƙwantar mata da hankali inda ya sake kwantar mata hankali akan zai yi bincke Mai kyau akansa 'dan haka suka bawa Nadiya dama akan yazo ɗin kafun su kai maganar gurin su Daddy,
Ille kuwa kamar yarda Papa ya bukaci ganin Evans haka yazo cikin shiga ta mutunci da kammala,a hirarsu da sukayi mai tsiya Papa da Mami suka nuna gamsuwatsu da Shi 'dan haka babu bata lokaci suka kai maganar gurinsu Daddy waɗanda suma bayan ganawa da mahaifiyarsa suka gane ita ɗin babbar mutum ce Mai fadin zuciya 'dan haka suka rufe babi na ƙabilanci da banbance Ra'ayoyi da Al'ada suka ƙarbi Evans da zummar zasu fadaɗa bincike sannan zasu nemesu domin tsayar da magana ɗaya.Chuchujay✍🏽
![](https://img.wattpad.com/cover/358007345-288-k287030.jpg)