AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two of Aure uku series .
By
CHUCHUJAY ✍🏽
Episode 4⃣7⃣➡4⃣8⃣
GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa 1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal 🥱ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Zan baku wannan garabasar ,masu cemun sati yayi kaɗa ga shi kanan sai 1st February 2024,Ya kusa karewa 'fa.
maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Tunda Abdallah ya koma gida hankalinsa yaƙi kwanciya baki ɗaya ya karkata gun Hafsa,Ya gama yarda da yana santa ,idan da za'a bi ta tashi kuwa wannan tsarin da ba'a yisa ba domin hankalinsa bai gamsu da hakan ba,
Wayarsa Ya ɗauko yama rasa abunda zai danna a ciki,numbernta da yayi saving da Heartthrob Ya shiga yana tantama na Ya kirata ko a'a ,daga bisani kuma zuciyarsa da abunda yake so yaci galabar sa yayi dialing numbern nata ba tare da yayi tunanin dare ne ba domin a lokaci karfe sha biyu na dare ,a ringing ɗin farko ta dauka cikin baccin da Ya fara ɗaukarta Kaɗan tace"Assalamu alaikum"
Ƴar ajiyar zuciya yayi daga ɗayan bangaren yace "wa'alaikis salam,na tasheki ko ?"Kimun afuwa nakasa samun nutsuwa ne sannan baccin yaƙi yazo wanda na alkantashi da rashin jin muryarki Mai daɗi da sanyi,ina fatan banyi laifi ba
Murmushi tayi kamar yana ganinta tace "aikam Bakayi laifi ba domin ni kaina baccin ne kawai Ya sace ne amma tsorone fal raina kar matar Hamma Nameer ta zo ta dakani cikin ɗaki babu wanda Ya sani.
Dariya yayi yace "bazata ma fara ba ,idan kuma ta fara daka mun abar kaunata to tabbas zata ga fushin Abdallah sosai,"
Cikin rashin sanin abunda zata faɗa kuma tace "Ai nama kulle ko ina and Aunty Nadiya ma ta jima kafun ta wuce sannan ta daɗe tana min hira a waya har na samu nayi baccin nan.
![](https://img.wattpad.com/cover/358007345-288-k287030.jpg)