Finale

244 19 0
                                    

AHALINA

(Siblings of different fathers)

Book two in Aure uku series

    By

CHUCHUJAY ✍️

FINALE

   Baki ɗaya kwanciyar Hankalin da suke nema sun samu domin kuwa kowa a gidansa idan ka kalla suna zaune ne cikin zaman lafiya mai daɗi,

Idan kana kallan rayuwarsu bazakace akwai wani abu behind it ba karma ace yarda Haɗin kai na AHALIN yake, idan ba wai an faɗa maka ba bazaka taba cewa wai yaran Umaimah Shida kowa da ubansa ba,AURE UKU da tayi ta yarda babu daɗi amma ta gamsu da cewa duk wani abu da ubangiji 'ya tsara maka shine gaskiya,babu wani abu bayansa sannan baya taba ɗora maka abu wanda yafi ƙarfin kanka,sannan every failure' is a blessing domin kuwa mutanen da suke jiran ganin failure' na Aurenta sunfi masu fatan ya ɗore.

    Taro ne suka tsantsara na Family bayan Wata guda da Auren Su Nadiya duba da yanayi na kowa zai tafi,Yan uku zasu koma makaranta Abdallah kuma da matarsa Adamawa domin Gaida iyayen Hafsa daga nan kuma  zasu wuce mecca domin Aikinsa yayin da Nameer Baba Bulama ya yanke masu ranar zuwa Cameron wanda tafiyace yake san suyi baki ɗaya domin kwantarwa da iyayen Jamaimah hankali akan tana cikin hannu mai kyau,ille kuwa ranar saturday da 'ya zamana weekend suka dugunzum wajen tafiya masarautar.

    Tun da jirginsu 'ya tashi kirjin Jamaimah ke dukan tara tara wanda Nameer 'ya kula da yanayinta,cike da kulawa 'ya kama hannunta yana mai shafa hannunta a hankali cikin sigar lallashi,ajiyar zuciya tayi tace "babe im scared bansan 'ta inda xan fara da iyayena ba,sake rubbing hannunta yayi yace komai zai daidaita ,insha Allahu babu wata babbar matsala,kar ki manta da Gradnpa Bulama a wannan tafiyar da Abuh da Papa da Mami da ummuh ga nan su Abdallah, su kansu zasu san guduwanki mai amfani ne after all ga ɗan Abbah a ciki ,

Tsintar kanta tayi da murmusawa tana mai faɗin"stop joking a moment ɗin nan abunda nayi musu ba dai dai bane ba".

Kaɗa kai yayi yace"na gamsu ba dai dai bane ba amma Abun daɗine da 'ya zamana kin dakatar dasu daga aikata ba dai dai ba domin kuwa da kin zauna zasuyi miki Aure ne wanda haramun ne saboda kina da Aurena wanda koda babu iyayen mu halsataccene duk da wata mazhabar kance babu aynayin waliyyai bai hallarta ba amma a musulunce munsan ya hallarta tunda an shaida kin karbi sadaki an daura wanda dama Aure shaidu yake buƙata ,dan haka ki kwantar da hankalinki komai zaizo da sauki da ikon Allah."

    A haka Nameer 'ya ringa assuring Jamaimah har suka isa kasar,already dama kafun isar su Granpa Bulama ya saka an sanar da sarki RAIS maganar zuwansa ta hanyar connection,duk da babu abunda 'ya taba haɗasu amma mahaifin Jamaimah ya saka aka shirya tarbasu tunda shi din sanannan mutum ne wanda zuwansa gurin mutum bazai taba zama sharri ba ,

Koda suka iso sarkin da kansa 'ya Aika a daukosa a airport',kallan Jamaimah kawai Drivern da aka aika 'ya ɗaukosun yake dan bazai taba manta fuskarta ba duk da kuwa baƙone shi,fuskarta tayi mutuƙar yawo domin mahaifinta lokacin batanta 'ya saka Milliyan biyu a kuɗin Nigeria ga duk wanda 'ya kawota,kasar ta dauki kara akan wannan offer da sarki rais 'ya bada hakazalika matasa sukayi chaa wajen neman Jamaimah , tashin hankali kuwa babu irin wanda harith bai shiga ba domin wannan gangancin shi Jamaimah tayiwa dan haka har a ranar bai daina nemanta ba a duk inda tunaninsa 'ya kai masa zataje,karshe kuwa da yayi yinkurin kashe Sarki Aka ɗauresa.

    Koda suka isa masarautar babban sashen dake daukar baki akayi dasu,gurin 'ya gaji da haɗuwa da girma ,kafun isowarsu kuwa makil aka cika ɗakin da kayan cima na alfarma domin tarbar su,basu dade da zuwa ba sarkin 'ya bayyana domin girmama bakin nasa,fadawa suka fara shigowa kana Sarki Rais a baya,

Koda ya shigo idanunsa basu sauka akan kowa ba sai batacciyar ɗiyarsa,wani irin abune 'ya daki zuciyarsa wanda bazai iya fasalta menene ba domin kuwa yanayin rabon sa dashi tun lokacin da aka sanar masa da sarauniyarsa ta haifi Jamaimah,

AHALINA(book 2 in Aure uku series)✔Where stories live. Discover now