X1▶2

274 17 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AHALINA

(Siblings of different Father's)

(Book two of Aure uku series)

CHUCHUJAY ✍🏽

Domin fahimtar littafin sosai zaifi kyau ka fara karanta Aure uku,amma idan wannan ɗin ma ka fara laha lau amma i suggest kafara karanta Aure uku.

Gamasu san a tallata masu hajarsu cikin farashi mai sauki 'a duk guri uku da ake posting 09058131213.

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

EPISODE 1⃣➡2⃣

INTRODUCTION

•NAMEER HABIB

Saurayi ɗan kimanin shekaru talatin da huɗu ,saurayi mai Kyau da ji da kuɗi da aji,

Architecture sannan business tycoon wanda ke da Construction company Mai zaman kansa,

C.e.o PIXEL CONSTRUCTION COMPANY.

Wanda Ya haɗu da tsaƙwakiya a rayuwar Auren sa.

NADIYA BELAL,

Budurwa yar kimanin shekaru ishirin da tara ,

Idan ka Kalleta kaji shekarunta take zaka ƙaryata shekarunta saboda baki ɗaya tayi ma shekarun kankanta,

Mai kyauce irin melanin ɗin nan wanda kana kallansu kaga Africans ,kalarta Mai kyauce sannan ga hutu da kulawa ta samu,

Model ce sannan Founder ta AFRICAN QUEEN(s) MODELING ROOM ,

Kungiya dake ɗaukar MODELs tayi managing nasu .

ABDALLAH HAFIZ.

Mutane na masa inkiya da young Sheik ,ƙaramun malami Mai fasaha da hazaƙa wanda kowa ke mamakin yarda yazama malami a shekarunsa ishirin da shida na haihuwa ,

Shahararsa da ƙokarinsa ba kowa bane illa mahaliccinsa da kuma maminsa da papansa waɗanda suka tsaya masa,

kowa da maganar Abdallah a bakinsa 'dan shi ɗin abun burgewa ne ,

Babban foundation yake dashi na taimakawa marayu da marasa karfi sannan a harkar kasuwanci shima ba'a barsa a baya ba yana tab'awa.

JAMAIMAH RAIS

Budurwa yar kimanin shekaru ishirin da shida,yar asalin garin CAMEROON ce sannan ɗiya a gurin sarki RAIS tilo 'dan haka Ya ɗauki dukkan soyayyar duniya Ya ɗora mata ,irin yaran nan ne da aka sangarta sannan suke gani babu abunda zasu nema su rasa,shagwababiyar gimbiya a masarautar DILAH sannan gimbiya mai taka dukkan wani talaka ,mutane kance wulaƙanci Shine ɗaya sunan ta amma ta faɗa soyayyar da take wahalar da ita .

EVAN HANS

Matashi ɗan shekara talatin da huɗu ,Ghanian ne wanda ke da rubi da Nigeria ,mahaifinsa 'dan ghana ne yayin da mahaifiyarsa Igbo ce asalin Nigeria cikin garin akwaibom ,

Christian ne sannan sana'arsa modeling bugu da ƙari shi ɗin actor ne ,

Soyayyar da ake kira da forbidding love a cikin danginsa itace tayi masa kamun kazar kuku

HAFSAT BALARABE

Ɗaliba a kwalejin fasaha da kimiya a cikin garin jibia dake garin katsina inda take karantar Computer science,budurwa yar kimanin shekaru sha tara ,

Iyayenta asalin Yan garin katsina ne sanann marainiya ce dake zaune gurin matar uba,

Bata da wani gata bayan na Allah 'dan mahaifinta Ya zama shanyayye a gurin matarsa ,

AHALINA(book 2 in Aure uku series)✔Where stories live. Discover now