AHALINA
(Siblings of different father's)
Book 2 'in AURE UKU series
By
CHUCHUJAY ✍🏽
Episode 2⃣9⃣➡3⃣0⃣
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Cikin Yauƙi Jamaimah ke takawa dan zuwa motar da Nameer Ya shiga ,ganin Ya wa motar key tasan tabbas idan bata hanzarta ba zai tafi yabarta Ya saka ta ja akwatinta gudu gudu sauri sauri ta nufi motan tana Mai faɗin "Baby mana wai menene hakan?"
Buɗe bayan motar tayi ta saka akwatinta dan kit din kana ta koma passenger seat ta zauna,
Tun kan ta rufe ƙofar da kyau Ya fafareta dan har sai da ta saka ƙara saboda yarda ta tsorata,
Tunda suka fara tafiyar har suka isa gidan bai ce mata komai ba hakazalika itama dan ganin yarda Ya haɗe rai kamar an aiko masa da saƙon mutuwa,
Bakin katafaren gidansa dake cikin GRA ya tsaya yana Mai yin horn,sau ɗaya yayi Mai gadin gidan yazo da gudunsa Ya buɗe masa dan yasan motar Nameer sarai,
Bai tsaya kula gate man ɗin ba Ya nufi ma'adanar aje mota Ya aje,
Shi Ya fara fita Kana ita ,
Get man d'in da Ya tako garesu ta kalla da wani yauƙin wulaƙanci tace "kai zo ɗauki min akwatina ka shiga dashi ciki sannan kabi mun shi a hankali dan yayi costing salary dinka sau goma."
Da mamaki Nameer Ya juyo yana kallanta dan a haife Mai gadin Ya haifeta,
Hannayensa Ya saka a kugu yayin da Mai gadin Ya nufi akwatin dan dauka amma Ya tsaya a lokacin da Nameer yace "Baba sulaiman bari mata akwainta ka koma kan aikinka dan aikinka yafi ɗaukan akwatin nan."
Babu musu Baba sulaiman Ya juya yana Mai faɗin Angama ranka shi daɗe.
Buɗe baki tayi tawani shagwab'e fuska tace "yanzu dan Allah Baby mene hakan,Mai zaisa kayi humbling ɗina gaban Mai gadi kaskantacce,wannan ai salan kaja mun raini ne ina matar gida.
Karamin murmushi yayi Ya Kalleta a kyau yace "Jamaimah kenan,kina bani mamaki,ke gani kikeyi kamar ke kinfi kowa a duniya saboda kawai an haife ki gidan sarauta ko?
Ku gani kukeyi kowa ma banza ne saboda kuna da mulki ko?
Bari kiji da kyau ki kuma saurareni,abunda kikayiwa iyayena Yau yana daya daga cikin abunda zaisa bazan tab'a sakinki ba sannan bazaki tab'a samuna miji ba muddin ke wulakanci shine jigon rayuwarki,sannan zan nuna maki ke ba kowa bace face mutum wadda idan kika mutu kasar da za'a saka kaskantacen almajiri kema nan za'a sakaki ,kilanma nashi kabarin yafi naki idan yafiki aiki mai kyau domin abinda baki sani bs shine wulaƙanta dan adam kawai zai halaƙar dakai,.
Abu Mai muhimmanci kuma da nake san ki sani shine a kasarki ne kike gimbiya amma a ƙasata a gida na a matsayin Matata ke bakowa bace sai wadda zata zauna tayi mun biyyaya tayi ibadar Aure,idan kina so fa kenan,amma duk ta inda kika bullo nima na iya bullawa ta gurin ni dake kuma shege Ya fasa,kina wannan wulƙancin kuma wallahi zanyi Aure har mata uku musha soyayya ke kuma ki sha wulaƙancinki ke kaɗai tunda shi kika zab'a
Yana kai ƙarshen zancen sa Ya juya dan shiga cikin gidan,binsa tayi da ido tana Mai jin zuciyarta na mata wani irin zafi musamman da Ya kawo mata maganar Aure,Cije leb'enta na ƙasa tayi tace "ina sanka Nameer sannan kai nawane ni kaɗai ,bakuma zaka chanza ni daga yarda nake ba ,haka nan zaka karb'eni domin wannan sarautar a jinina take babu wanda ya isa Ya cire mun wannan izzar ."
